Abin Ya Yi Yawa: 'Yan Bindiga Sun Koma Sace Mutum 61 a Kaduna
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
'Yanbindiga sun sace kimanin mutum 61 a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.
Ƴanbindigar sun kai harin ne a garin Buda ranar Litinin da daddare suka buɗa wuta, kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Sai dai babu wata sanarwa daga hukumomin jihar da jami'an ƴansanda da ke tabbatar da harin.
Amma mazauna yankin sun ce ƴanbindigar sun yi wa garin ƙawanya ne da misalin karfe 11:30 na dare suka dinga harbi kan mai uwa da wabi.
Ba wanda zai iya fadin adadin ƴanbindigar da suka zo suka tattara maza da mata, waɗanda suka kai kusan mutum 61 da suka tafi da su," kamar yadda wani mazauni garin ya shaida wa BBC.
Ya ce akwai ƴan'uwansa mutum shida cikin waɗanda ƴanbindigar suka tafi da su.
"Mun tantance mata 32 da maza 29 ke hannun ƴanbindigar kuma akwai mai jego cikin matan da suka tafi da su wadda ba ta wuce kwana huɗu da haihuwa inda suka tafi da ita suka bar jaririn," in ji shi.
Ya ce ƴanbindigar sun abka garin ne da niyyar tattara mutane da dama amma taimakon jami'an tsaro da suka kawo ɗauki ne ya taƙaita yawan mutanen da suka sace.
"Ƴanbindigar na cikin tattara mutane sai ga jami'an tsaro sojoji na Kajuru suka buɗe wa ma su wuta suka dinga musayar wuta."
"Ba don shigowar jami'an tsaro ba da ba a san yawan mutanen da za su ɗiba ba," in ji shi.
Ya ce an samu tsaikun samun labarin al'amarin sakamakon rashin hanyar sadarwa ta layin salula a yankin.
Harin na Kajuru na zuwa ne mako ɗaya bayan ƴanbindiga sun abka garin Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun inda suka yi awon gaba da ɗaliban makarantun firamare da sakandare 287.
Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ƴanbindiga ma su satar mutane domin kuɗin fansa. Kuma duk da iƙirarin hukumomin tsaro na ƙoƙarin magance matsalar amma kuma sai ƙara ƙamari take musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
Satar mutane domin neman kuɗin fansa wata sana'a ce da ke ƙara haɓaka - wani al'amari da ke razana ƴan Najeriya.
Ƴansanda da sojoji duka suna ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya - kuma biyan kuɗin fansa, masana na ganin wata babbar hanyar samun kuɗi ce da za ta ci gaba da rura wutar matsalar.
Wasu hukumomi sun hana biyan kudin fansa, kamar a jihar Kaduna.
Gwamnatin Najeriya kuma ta daɗe tana musanta cewa akwai alaƙa tsakanin ƴanbindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa a arewa maso yammaci da kuma Boko Haram a arewa maso gabashi.
Amma yadda ake ci gaba da satar mutane masana na ganin ya nuna akwai alaƙa tsakaninsu.
Ƴan ƙasar da dama sun yi imanin cewa akwai raunin a ɓangaren tsaro da gwamnoni waɗanda ba su da iko a kan tsaro a jihohinsu.
managarciya Oct 30, 2021 12 172
managarciya Feb 3, 2025 3 113
Maryamah Dec 14, 2021 2 90
managarciya Jun 24, 2023 5 77
Maryamah Dec 16, 2021 10 75
managarciya Nov 13, 2023 0 550
managarciya Nov 12, 2023 0 346
managarciya Nov 12, 2023 0 335
managarciya Nov 12, 2023 0 416
managarciya Nov 11, 2023 1 702
managarciya Oct 8, 2021 0 423
Wani abu da yafi ciwa da dama daga 'yan Najeriya tuwo a kwarya a Wannan lokaci bai...
managarciya Dec 24, 2022 0 4367
Yanzu dai ina da burin na zama ‘yar majalisar dokokin jiha mai wakiltar Sakkwato...
managarciya Oct 17, 2021 0 789
Kwadayi yana daya daga cikin matsalolin al'umma, kuma ya taka rawa wurin halakar...
managarciya Oct 31, 2021 0 461
8-Samun duniya da rashin tunawa mutuwa. 9-Rashin karanta alqurani a muhallin da...
managarciya Oct 15, 2021 0 977
Iyaye na taka muhimmiyar rawa ga tarbiyar yaran su, ta hanyar sanar da su banbancin...