EFCC Ta Kama Wasu Matasa 7 Bisa Zargin Damfara a intanet a Abuja

EFCC Ta Kama Wasu Matasa 7 Bisa Zargin Damfara a intanet a Abuja

Jami'an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta EFCC, sun kama wasu matasa 7 da ake zargi da damfara ta intanet.

Wadanda ake zargin, Nnonyelu Favor Chioma, Ajator Henry Sopulu, Ego Andy Seji, Okeke Ikechukwu Jude, Oshioriamite Perfect, Ego Akin da Okeke sun shiga ne a ranar Juma’a a wani samame da suka kai a unguwar Tunlapal da ke Kurudu a Abuja.

A wata sanarwa da kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, ya ce abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyin hannu da na’urorin kwamfuta.

Uwujaren ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.