Ma'aikatan Lafiya Sun Yi Zanga-Zangar Gargaɗi Kan Ƙin Biyansu Albashin Wata Biyu A Zamfara

Ma'aikatan Lafiya Sun Yi Zanga-Zangar Gargaɗi Kan Ƙin Biyansu Albashin Wata Biyu A Zamfara
Ma'aikatan Lafiya reshen asibitin ƙwararru ta Ahmad Sani Yariman Bakura  a Jihar Zamfara Sun gudanar da Zanga-Zangar gargaɗi  Sakamakon ƙin biyansu Albashi tsawon wata biyu da Gwamnatin Jiha ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bello Muhammad Mutawalle ta yi.
Ma'aikatan sun yanke shawarar fitowa wannan zanga-zangar ta gargaɗi in da suka bayar da wa'adin sati ɗaya in gwamnati ba ta duba kokensu ba, za su tafi yajin aiki har sai baba ta gani.
Ma'aikatan lafiyar na asibitin a ƙalla za su kai 600 suna fama da wahalar albashi tun a shekarar 2019 abin aka kasa gyarawa ana yi masu tsambare a tsakanin biyan albashin a wata-wata.
Jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar ma'aikatan lafiya(JUHESU) ya ce gwamnati ta soma duban ƙorafe-ƙorafen ma'aikatan yanzu haka an biya sama da kashi 80 na ma'aikatan albashinsu.
Ya ce masu biyar bashi ma sun fara samun kuɗinsu.
Yana ganin gwamnati za ta sharewa ma'aikata kukansu ba za su kai ga shiga yajin aiki ba.
Duk ƙoƙarin jin ta bakin kwamishinan yaɗa labarai na jiha Alhaji Ibrahim Dosara abin ya ci tura domin wayar shi ba ta shiga, an tura masa saƙon kar ta kwana shi ma bai ce komai ba har zuwa haɗa wannan rahoton.