Sarkin Musulmi Ya Samu Gagarumar Tarba A Sakkwato
Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya samu gagarumar tarba a lokacin da ya dawo gida bayan tafiyar da ya yi a wajen jiha.
Mutane sun nuna goyon bayan su ga Sarkin Musulmi a jiya Alhamis da yau Jumu'a bayan kammala sallah ne cincirindon Mutane suka biyo bayan Sarkin suna kabbara.
Managarciya na ganin wannan lamarin bai rasa nasaba da kudirin dokar masarautar Sarkin Musulmi da gwamnatin jiha za ta yi wa gyaran fuska ya sa wasu fitowa don nuna goyon bayan su ga Sarkin Musulmi.
Gwamnatin Sakkwato na kokarin gyara ga dokar da za ta shafi nadin sarautu, abin da tuni ya janyo ce-ce-ku-ce, duk da yake gwamnatin ta ce tsarin da ma haka yake a baya.
Ita kanta masarautar Sarkin Musulmi ta bakin wakilinta a wurin sauraren ra’ayoyin jama’a akan dokar, Sa’in Kilgori, Muhammad Jabbi Kilgori ya ce a shirye suke su yi aiki da sabon tsarin domin da ma sun saba da shi.
Sai dai har yanzu jama’a ba su karbi wannan tayi na gwamnati ba, kan gyaran dokar domin suna ganin taba martabar masarautar Sarkin Musulmi ne.
Jama’a ne suka yi cincirindo a hanyar shiga fadar Sarkin Musulmi suna yi masa maraba, Kamar yadda aka yi ta yada hotonan a kafafen sadarwa na zamani.
Tuni dai da majalisar dokokin jihar Sakkwato ta yi nisa da aiki akan gyaran dokar kuma kowane lokaci tana iya yin matsaya a kan ta.
managarciya