MCRP: Tawagar Bankin Duniya ta ziyarci muhimman ayyukan cigaba a Yobe
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Tawagar Bankin Duniya mai kula da Kungiyar 'Multi-Sectoral Crisis Recorvery Project' (MCRP), wadda ke gudanar da ayyukan jinkai tare da sake farfado da yankunan da suka yi fama da matsalar tsaron Boko Haram, ta ziyarci wasu dsga cikin muhimman ayyukan da Kungiyar ta gudanar a jihar Yobe.
Tawagar, a karkashin jagorancin Fuad Malkawi, a ranar Alhamis kai ziyarar gani da ido a wasu muhimman ayyuka, wanda suka hada da duba aikin sake gina katafaren dakin ajiye magunguna a Ma'aikatar Lafiya a jihar Yobe, aikin gina gidajen likitoci, cibiyar horas da mata da ajujuwan gwaji ga kananan yara, da makamantan su.
A jawabin maraba da Ko’odinetan ayyukan MCRP a Yobe, Alhaji Musa Idi Jidawa ga tawagar, a karkashin Mista Malkawi, Ko’odinetan Kungiyar na kasa, Mohammed Danjuma, da sauran kwararrun ma'aikatan Hukumar sake farfado da Arewa Maso Gabas (NERSP/NEDC).
Bugu da kari kuma, Musa Jidawa ya yi wa tawaga barka da zuwa da fatan za a cimma nasarori kan batutuwan da kwararru a tawagar zasu tattauna, don kawo ci gaba wajen aiwatar da muhimman ayyukan da MCRP ta sa a gaba- bisa karin kudaden da aka samu.
Ya kara da cewa, ko a watan Mayu da ya gabata, tawagar Bankin Duniya ta ziyarci jihar da tattauna abubuwa da dama wadanda suka shafi ayyukan jinkai da Kungiyar ke gudanarwa a jihar, tare da hadi da masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban; wanda ya hada da yan kwangila da masu bayar da shawara da kuma wakilan al'umma da sauransu.
Ya kara da cewa, “Wannan tattaunawar ta fito da muhimman shawarwarin da muka bi tare da aiwatar dasu wajen cike wasu gibin da aka yi la'akari dasu, musamman karfafa hadin gwiwa, koyon sabbin dabarun yadda zamu gudanar da ayyukan mu, don haka muna sa ran wannan ziyarar za ta kara mana kaimi da ta hanyar duba ayyukanmu don karfafa mana gwiwa a ayyukan mu.”
“Wanda kuma mun fara aiwatar da karin kudaden tallafin da aka bamu bisa ingantaccen tsari; wanda ya kunshi aikin bayar da horo don gudanar da ayyukan mu ga ma'aikatanmu na kananan hukumomi, ba tare da tangarda ba. Sannan da aikin raba tallafin dabbobi ga jama'a domin samun dogaro da kai, wanda yanzu haka ya kai kimanin kaso 41 cikin dari na aikin."
"Haka kuma muna mika godiya ga wannan tawagar saboda goyon bayan da suka ba mu tare da gudummawa da daukar matakan gaggawa wajen yin bitar ayyukan da muka aiwatar wa. Kana da goyon bayan da muke samu na gwamnatin jihar Yobe."
Ya ce kyakkyawar alaka tsakanin aikin Kungiyar MCRP ya samo asali ne daga jajircewar Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda hakan ya bude kofa ga jiga-jigan gwamnati wajen bayar da cikakken hadin kai, wanda ya hada da yan majalisar dokokin jihar Yobe.
Ya ce "Wannan shi ne tushen samun nasarorin da muka samu kuma abin a yaba ne matuka. Za mu ci gaba da kai-komo a tsakanin bangarorin gwamnati da masu ruwa da tsaki a jihar Yobe wajen samun nasarar fitar da muradun al’ummar jihar Yobe a karkashin shirin: Burin Bunkasa Ayyukanmu.”
Alhaji Jidawa ya ankarar da tawagar Bankin Duniya dangane da kalubalen da ke yi wa jihar barazana, a kokarin Kungiyar na farfado da jihar, yayin da sakamakon ambaliyar ruwa a yan kwanakin nan ke kokarin kawo cikas, wanda yana da alaka da sauyin yanayi. Ya ce ambaliyar ruwan ta shafi kowane yanki a fadin jihar Yobe, al'amarin da ya jawo salwantar rayuka, gidaje, hanyoyi da gonaki, wanda ya kawo asarar biliyoyin naira ga al'ummar jihar.
Wanda ya bukaci tawagar ta sanya wannan matsala daya daga cikin abubuwan da za ta duba tare da saka shi cikin ayyukan jinkan da zata tallafa wa jama'a.
A nasa bangaren, Shugaban tawagar Bankin Duniya, Fuad Malkawi ya yaba da kokarin da Ko'odinatan ayyukan bisa taskace nasarorin da kungiyar MCRP ta samu a jihar Yobe, ya kuma godewa masu ruwa da tsaki da suka halarci taron.
managarciya