ASUU ta janye yajin aiki bayan wata Takwas

ASUU ta janye yajin aiki bayan wata Takwas

 

Kungiyar Malaman Jami’o'i ta Ƙasa,  ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe watanni takwas ta na yi.

Kungiyar ta yanke  shawarar janye yajin aikin ne a babban taron Kwamitin Zartaswarta da ya gudana a Abuja a jiya Alhamis.

A safiyar yau Juma’a ne dai wani babban jami’in na ASUU da ya halarci taron ya shaida wa Daily Trust cewa, “Gaskiya ne, mun janye yajin aikin… Nan gaba kaɗan da safiyar nan Shugaban ASUU na Kasa zai fitar da sanarwar a hukumance.”

Wata takwas cif ke nan da malaman jami’o’in gwamnati su ka shafe su na yajin aikin da kungiyar ta kira tun ranar 14 ga ga watan Fabrairu, 2022.