'Yarsanda da aka kora aiki ta yi barazanar kashe kanta da ƴaƴanta
Wata ƴansanda a Jihar Edo da aka kora , Sifeto Edith Uduma, ta yi barazanar kashe kanta da ƴaƴanta bayan da aka kore ta daga aiki saboda ta fallasa wani lamari da ake zargin fyade, wanda ya shafi wani abokin aikinta.
Ta zargi rundunar ƴansanda ta jihar da korar ta ba tare da adalci ba, tana mai cewa al'umma ba su ji bangaren ta na labarin ba.
Korar ta ta biyo bayan wani faifan bidiyo da ta dauka a watan Oktoba, wanda ya nuna wani jami'in 'yansanda, Sajen Abraham, yana cikin wani mummunar yanayi tare da wata yarinya 'yar shekara 17 a wani ofishin 'yansanda da ke yankin South Ibie na Jihar Edo.
An ga jami'in yana sa wando cikin hanzari yayin da yake tambayar dalilin da ya sa Edith ke daukar bidiyon. Haka kuma, an ga yarinyar tana kwance a kan kujera a cikin dakin.
An samu labari daga 'yan sanda cewa an kori jami'an biyu daga aiki bayan gudanar da shari'ar cikin gida a rundunar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Edo, Moses Yamu, ya fitar a watan Nuwamba, ya zargi Uduma da hada kai da mijinta, Insfekta Ibrahim Mohammed, don karbar naira miliyan daya daga Abraham domin boye lamarin. Sai dai an ce lokacin da Abraham ya ba da naira 45,000 kacal, an saki bidiyon a yanar gizo.
managarciya