Labarin GUDALIYA Mai Ƙusumbi

Labarin GUDALIYA Mai Ƙusumbi

 GUDALIYA 

"Yarinya wai wa kike yiwa dariya ne?"
Dattijon ya faɗa yana kallon yarinyar da take ta faman dariya har da kwanciya a ƙasa.
Sai da ya maimaita tambayarsa kafin ta kalle shi cikin dariya.

 "Yo Baba da wani a gurin ne bayan mu biyu? Kai! Amma Allah Ya hore maka mashaƙar iska...."
Ta faɗa tana kallon hancinsa kafin ta ɗora "Don Allah Baba taya kake numfashi da wannan hancin? Ko da yake ba ma hancin ne abin kallo ba, wannan ƙaton kai naka mai kama da falalin dutse..." Duk wannan zancen tana yinsa ne cikin dariya.

Abin da ya fusata tsohon kenan ya nufo ta a sukwane, tana ganin hakan ta ranta a na kare.
Bin bayanta ya yi.

 "Fitsararriyar yarinya mu je na ga wanda ya tsaya miki kike yi wa mutane shaƙiyanci."
Duk da tana cikin gudun ceton kanta ne hakan bai hana mata yin wata tsokanar ba. Wani matashi ta tarar tsaye tana gab da shiga gida, kawai ta daka tsalle ta falle shi da mari. 
Dai dai zata shiga gida ta juyo tare da zuro majiyar ɗanɗanonta waje tana masu gwalo 
"To masu kan kwakwa na barku lafiya."
Ta shige cikin gidan da gudu.

Mamanta na zaune tsakar gida tana tankaɗen garin tuwo, bata da wani ceto kawai ta ji mutum ya bi ta kanta ya wuce da gudu. Tuni garin ya yi fallatsi, tamkar yadda ƙaiƙayi ke komawa kan masheƙiya, haka garin ya wanke wa Maman jiki.
"Na shiga uku ni jikar mutum huɗu!"
Ta faɗa tana dafe ƙirji, sannan ta ɗora.

"Da gani kin yo sababben halin naki ko? Haba Gudaliya kullum ke sai kin ɗebo mana rigima? Watarana sai kin ɗebo ruwan dafa kanki idan baki daina ba."

Wannan sababin da take shi ake kira ihu bayan hari domin tuni Gudaliya ta shige ɗakin Babanta tana haƙi.

Jin wannan furucin ya fito da Mudan daga daƙinsa tamkar an harbo shi a kibiya, ya dira gaban matar tasa.

"Bakinki ya sari ɗanyen kashi Karime, ba abin da Gudaliyata za ta gani sai alkhairi Insha Allah......"

Sallamar da ake ta rangaɗawa daga kofar gida ya saka shi fita a fusace Gudaliyarsa tana take masa baya.

"Lafiya kuke ta damunmu da sallama tamkar mun ci bamu biya ba?" 

Tsohon ya kwashe komai ya faɗa masa.
Me Mudan zai yi in ba dariya ba?

"Ai kuwa yarinya ta yi gaskiya, Allah Ya Yi halitta a nan, Ƙurungu kenan."

A fusace tsohon ya juya ya ce "Ashe kai kake ɗaure mata kugu, ku je zaku ga ni."

"Mu ga alkhairi....!" 

Bai gama rufe bakinsa ba ya nemi tsohon ya rasa. Ashe tsohon nan aljani ne. Mudan ya tsorata sosai ya sunkuci gudan jininsa suka yi ciki da gudu.

Washegari sai tashi aka yi aka ga Gudaliya da ƙusumbi a baya. Haka halittarta ta sauya zuwa ta tsohon da ta yi wa izgili.
Mudan ya sha kuka ganin yadda  tilon 'yarsa da ya mallaka ta dawo. A maimakon jama'a su tausaya masa kowa sai dariya yake yi.

ƘARSHE.....

Ruƙayya Lawal Ibrahim