Babban Buri:Fita Ta Takwas

Babban Buri:Fita Ta Takwas

BABBAN BURI

SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.


بسم الله الرحمن الرحيم


FITOWA TA TAKWAS

Haka rayuwarmu ta yi ta tafiya yau daɗi gobe a kasin hakan.
Babanmu ya dawo sai dai ba'a dace ba domin kuwa koda yaje Kakanmu yana kwance ba lafiya shi'isa bema samu zarafin yi masa maganar ba ya juyo ya dawo gida.

★★★★★★

Shirye shiryen biki kawai ƴan gidan suke yi ba kama hannun yaro, ya yin da shi wanda akeyi domin sa bema san anayi ba , sha'anin gabansa ne kawai a kansa.

Hajiya Umma wato mahaifiya ga Safara'u ƴa a gurin Alh Bello, zaune take a gaban boka tana kora masa baya ni kamar haka "Ranka ya daɗe inason a sa masa son ƴata ko bayan haɗin da iyayensu zasu yi tsakanin sa da ƴar ƙane a gurin mahaifin Safara'u ne yaji yana muradin zama da ita."

Kallonta ya yi sannan ya ce cikin ƙaƙƙausar murya "Indan wannan karki damu zamu yi aiki a kansa amman aikin zai ɗauki tsawon lokaci domin kuwa shi yaron yana tsaye a kan ibadarsa abune me wuya asiri ya kamasa da wuri wuri koda ya kamasa kuwa zai iya sakinsa a ko wanne lokaci."

"A ƙoƙarta dai ranka ya daɗe domin kuwa suna gabbb da ɗaura aurensa ni kuwa bana son waccen ta riga ƴata shiga gidansa."

"Karki damu zamu tura a shagaltar dashi a kan ibadarsa domin mu samu yin galaba a kansa", kuɗi ta zube masa kana ta yi sallama dashi ta nufi hanyar gida da yaƙinin ƴarta ta gama shiga gidan AAS Wurno.

Fitowa ta yi daga dokar dajin ta nufi gurin da ta yi parking ɗin mota.
Kai tsaye cikin motar ta shige ta bata wuta sai gida.

Lokacin data je gida kuwa cike dajin daɗi take zayyanewa megidan abinda bokan ya ce, nan suka fara murna da annushuwa.

Kwance yake gaba ɗaya ya rasa meke damunsa a ƴan kwana kinnan, daya zauna bashi da tunanin komai saina yarinyar da baisan sunanta ba, ƙara miƙewa zaune ya yi sai dai har lokacin zuciyarsa hasaso masa yarinyar take yi.
Haka wannan daren gaba ɗaya ya ƙarƙare masa ba tare daya runtsa ba, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi domin kuwa besan me yake shirin faruwa dashi ba.
Kiran sallar farko ya miƙe yaje ya yi wanka kana ya fice zuwa masallaci.


Haka nima a nawa ɓangaren gaba ɗaya daren ban rutsa cikin saba, juye juye kawai na keyi da tunanin wanda bansan meye alaƙata dashi ba, da zansan yawa zuciyata tunaninsa.

Ganin baccin yaƙi zuwan min ya sanya na miƙe jiki a saɓule naje na ɗauro alwala kana nazau na dinga kaiwa Allah kuka na, anan saman sallayar nauyayyen bacci ya yi awon gaba dani.

Jin ƙwankwasa ƙofar ɗakin mu da akeyi shine ya farko dani, miƙewa nayi har lokacin bana jin ƙarfin a jikina, tadda su A'ishah na yi sannan muka je muka ɗauro alwala muka gabatar da Sallah.

Bayan dawowan su Baba daga masallaci mukaje muka gaidashi sannan muka dawo muka fara karatun da muka saba.

Dukkanin abinda na keyi inayi ne kawai amman gaba ɗaya nutsuwata bata tare dani.

Na rasa dalilin hakan, amman gaba ɗaya jina nake yi kamar na yi tsuntsuwa naga kaina gidan AS Wurno.

Tare da Mama mukaje gidan da A'isha domin su yiwa Hajiya Inna godiya ganin irin ɗawainiyar da ta keyi damu a ko wacce safiya.

★★★★★★★

A zaune suke a farfajiyar gidan ko waccen su sai faɗan irin shigar da zata yi a wurin dinner da kamun da za'ayi.

Yayin da uwar gayyar take zaune a gefe sai faman ɓata fuska take yi tana daƙilar waya, kallonta Haulatu ƴar wajen Alh Sunusi ta yi kan ta ce "kowa na magana amman Safiya kin dawo cikinmu kina jinmu kin kunnen uwar shegu damu, ko dai fasa kamun za'ayi ne bakya buƙatar sa."

Ɗago kanta ta yi daga kan wayar da take daddan nawa sannan ta watsa masu wani kallo kai ka ce ba ƴan uwanta bane ta ce "no ni bani da matsala da komai naku , ku ɗai tsara komai idan da hali zanje idan ba hali ba zanje ba , dan kunsan bana son takura hwa", a yangan ce take maganar tana faman ɗaɗɗaure fuska ita a dole zata auri mai kuɗi wanda za'ace ta tsinci dala kenan, domin tana da yaƙinin gaba ɗayan su su takwas duk wacce aka cewa za'a haɗata da Haidar zata yarda ba zata bijire ba.

Asiya  wacce suke cewa ƴar beauty ƴa a wajen Alh Bello ƙanwa ga Safara'u ce ta caɓe zancen da cewa "Ni naga sai faman ɗauke kai kike yi kina ya ƙunar fuska me wannan ke nufi?".

"Duk abinda kike nufi shi nake nufi", cewar Safiya kenan.

"Kwashewa su ka yi da dariya kana suka taɓe kan can ƴar beauty ta ce "tabb kar dai kice dan kinga ana neman liƙawa Yaya Haidar kene kike hura mana hanci?, Idan ma hakanne ki gaggauta komawa yadda kike yarinya domin kuwa anan gurin kinsan ba wacce zata gaya maki halinsa kece ma zaki bayar da labarinsa, wanda bema san me akeyi ba shine zaki dinga ɗage ɗagen kai a kansa?, tabbb ayi mugani."

Ta juya gurin sauran ta ce "tau hwa ƴan uwas ku kama kanku da bikinnan ki barta a haka tunda har ta nuna bata buƙata, tunkan taje gidan tafara hurar hanci tana hanka ɗarmu ina da ta shiga gidan ai nuna mana zata yi bata taɓa sanin mu ba.

Nan fa guri ya hargitse kowa da Abinda yake faɗa , da yawa duk sun fitar da hannunsu cikin lamarin bikin a cewarsu gwanda su kama kansu.

Shigowarsa cikin gidan kenan yana batun fitowa daga motar ya dinga jin hayaniyar mutane , idanuwansa ne suka sauka kansu , tsaki ya jaah kan ya yi kwafa domin kuwa duk abinda akeyi yana da labarinsa ya zuba masu idanuwa ne kawai yaga iya gudun ruwansu a zuciyarsa kuwa yana gitse wanne hukunci ya dace ya zartar Masu ne?.

Ta gunda suke zazzaune yabi ya wuce kota kan su bebi na ya yi shigewarsa sashen Hajiya Inna, yana me saƙa abubuwa da dama a ransa.

A Parlour ya tayar damu zaune dani da Hajiya Inna da Mama na da A'isha, sai godiya Mama ke zubawa yayin da Hajiya Inna sai faɗan "ai yiwa kaine bakomai wallahi."
Gaida Mama ya yi cikin sakin fuska abinda ko a mafalki ban taɓa sa rai ba.

A nan Hajiya Inna ta gabatar dashi wurin su Mama, suma ta gabatar dasu a gurinsa.
Da kallon sani yabi A'isha yana me tambayarta sunanta, ta amsa masa da A'isha cike da nazarin ina yasan fuskar yake kallonta , duk nazarin sa ya rasa gunda yasan fuska sai kawai ya basar da abin, kan ya nufi ɗakinsa a cikin takonsa na ƙasaita da jin kai.

Be jima da shiga ba sai gashi ya fito ya fice daga ɗakin can ba jimawa ya leƙo yana kiran A'isha.

Cike da tsantsar mamaki na bisu da kallo ya yin da Mama da Hajiya Inna basu bi ta kan abin ba suka ci gaba da firar su kamar waƴanda dama sun san juna.

Kaf yinin yau banyi aikin komai ba a gidan na dai shiga na gayawa su Yahanazu suyimin uzuri, na dawo waje nayi zaune iname duba hanya naga ta gunda ƙanƙara zata ɓullo domin kuwa hankalinsa ya yi masifar tashi da ganin tsawon lokaci ban ganta ba, da alamu dai gaba ɗaya basa cikin gidan.

Za mu ci gaba.......

ƳAR MUTAN BUBARE CE