ZAMAN JIRA: Fita Ta Huɗu

Ya kwashe da dariya ya ce,  "Ashe ma ke ƙaramar 'yar balaja'u ce, tun da har za ki iya ba da hakuri akan abin  da bai taka kara ya karya ba? Da kika ganni nan ba ƙaramin aikina bane ba na gama da ita na yo kanki ba, to me ya dame ni ai kunya ni gaba na bata ba baya ba. Da kike gani na nan, ita kanta kunyar tasan ni na yaye ta don haka tsorona take. Fati kam ta riga ta gama tsinkewa da lamarin Nafi'u bata taɓa tunanin zai iya aikata wannan rashin kunyar ba, kusantar ta a gaban Asiya. Asiya ba tai wata-wata ba ta kwasa da gudu ta buɗe gidan ta bar warin takalmin ta, a hargitse ta isa gida tana ba Mamarsu labarin abin da ya faru. Ita kan ta uwar kusan daskarewa tai tsabar tsoron Allah da ya kamata. Jinjina kai tai kawai ta tashi ta bar gun don har ga Allah kunyar ma Asiya take da har Nafi'u ya cire kaya a gabanta ya cire na Fatin. Tabbas ko Fati bata so sai ta bar gidan Nafi'u ko dan tarbiyyar yaran da za su haifa ma, ina dalili ka tara yara da marar kunya irin wannan?...

ZAMAN JIRA: Fita Ta Huɗu

ZAMAN JIRA


               *NA*
*HAUWA'U SALISU (HAUPHA)*


( _Book 1_


                     Page 4


*Ayi min afuwa kwana biyu an ji ni shiru, yau da gobe ce.*


Fati ta zabura ta nufi inda yake zata ba shi haƙuri ya daka mata tsawar gaske ya nuna Asiya da hannu ya ce,  "Ke don Ubanki ni kike wa rashin kunya har cikin gidana, waye tantarin marar kunya kaf ahalinku? To yau zan gwada maki kaf garin nan babu mai ja  da  iskancina balle ya kamo kwatar tantirancina, ba dai akan matata kike wannan zaƙewar ba? To a gabanki zan mata ƙarshen wulaƙanci  idan kin isa ki wuce da ita gidanku don kutumar Ubanki. Asiya ta wani zaburo, "Wallahi ba dai ubana ba, kuma kai baka isa ka wulaƙanta wanda Allah bai nufa da wulaƙancewa ba don haka shege ka fasa ni da kai...bakinta ya datse lokacin da taga ya cakumo Fati ya cire mata rigar jikinta, ya manna bakinshi a nata. Da gaske yake yamutsa ta yana neman shigar ta dama shi wando ne kawai a jikin shi don haka bai sha wahalar about that person shi ba, sai a lokacin ta gane me yake nufi. Lallai Nafi'u ya wuce tantarin da take kallonsa ya dube ta ya kwashe da dariya ya ce,  "Zan mata cin kaca a gabanki na kuma yayyaga ta a gabanki duk da nasan hakan zai iya zubar min da ciki, kuma wallahi cikina ya zube sai na maka ki ƙara kotu nace ke ce kika zubar min da ciki a bi min haƙƙina. Runtse idonta tai ganin da gaske ya ke hawaye suka zubo mata, da gaske ne Nafi'u ya fi ɗan balaja'u masifa kuma duk abin da ya ce zai aikata tabbas zai aikata shin. Don haka idonta rufe ta tsugunna ƙasa ta fara ba shi haƙuri,  "Don darajar Allah Yah Nafi'u kai haƙuri kar kai mana wannan ɗibar albarkar, tabbas nayi kuskure amma kai haƙuri shi ne na ƙarshe da zan sake shiga sabgarka in sha Allah. Idan ma so kake ka haɗu da matarka ku je can ɗaki ba a gabana ba don Allah. Wannan zuwan shi ne zuwana na ƙarshe gidanka in sha Allah kai haƙuri kar ka tozarta ni har haka don Allah."
Ya kwashe da dariya ya ce,  "Ashe ma ke ƙaramar 'yar balaja'u ce, tun da har za ki iya ba da hakuri akan abin  da bai taka kara ya karya ba? Da kika ganni nan ba ƙaramin aikina bane ba na gama da ita na yo kanki ba, to me ya dame ni ai kunya ni gaba na bata ba baya ba. Da kike gani na nan, ita kanta kunyar tasan ni na yaye ta don haka tsorona take. Fati kam ta riga ta gama tsinkewa da lamarin Nafi'u bata taɓa tunanin zai iya aikata wannan rashin kunyar ba, kusantar ta a gaban Asiya. Asiya ba tai wata-wata ba ta kwasa da gudu ta buɗe gidan ta bar warin takalmin ta, a hargitse ta isa gida tana ba Mamarsu labarin abin da ya faru. Ita kan ta uwar kusan daskarewa tai tsabar tsoron Allah da ya kamata. Jinjina kai tai kawai ta tashi ta bar gun don har ga Allah kunyar ma Asiya take da har Nafi'u ya cire kaya a gabanta ya cire na Fatin. Tabbas ko Fati bata so sai ta bar gidan Nafi'u ko dan tarbiyyar yaran da za su haifa ma, ina dalili ka tara yara da marar kunya irin wannan?...

Nafi'u ganin Asiya ta fice da gudu ya wantsalar da Fatin ya shige ɗaki ko ta kan gajeren wandonsa bai bi ba. Da ƙyar ta tashi ta ɗebi nata kayan ta haɗa da wandonsa ta nufi ɗakin ita ma domin ta je ta ba shi haƙuri don bata san faɗan shi da Asiya ya shafe ta hakan zai ba shi damar lagwaigwaita ta yadda ya kamata, domin shi ko faɗa ya yi da mace bai hana ya kusance ta shi hakan ma wata hanya ce ta mugunta gare shi, domin sai ya yi tun tana jin daɗi har sai ta koma jin zafi tun tana kukan daɗi sai ta koma na baƙar wahala. Sam bai da sauƙi haka bai da tausai ya sha gaya mata shi ba duka ba zagi amma akwai babban duka a cikin wandonsa ga kowace tantiriyar mace. 
Yana kishinge a yadda yake ta isa ya tsugunna a gabansa tace,  "Don dajarar Allah kai haƙuri ka yafe mana ni da Asiya, hakan ba zai sake faruwa ba. Kuma nasan da Asiya tasan waye kai da gaske tabbas da babu abin da zai sa ta haye maka irin haka, amma ina da tabbacin ta yi na farko ta yi na ƙarshe."   Ya miƙa mata hannu alamar ta isa gare shi, cikin sanyin jiki ta isa jikinsa ya rungume ta yana shafa marar ta ya ce, "Kai kam boy me yasa baka san Babanka na shiga alheri ne? Kowane yaro janyo ubansa yake cikin alheri amma ban da kai, to ka sani nima zan rama zaka ga yadda zan dinga yi wa danginka alheri ban yi maka. Kamar wani mahaukaci ya ci-gaba da cewa,  "Yanzu haka akwai ɗan'uwanka na bayan fage da ace an shaida na sai uwarsa da ba abin da zai hana na yi mai kyautar bajinta ranar da ya diro duniyar nan amma ina na bar shi ya fito duniya sai mutane sun sa uwata ta tsine min don ma jan wuya ne ni ba haka nan na barta kara zube ba yadda take da bin ƙa'idoji da san al'ada da yanzu ta tsine min na bi uwa duniya saboda iya shegen da nake tabkawa tana ji tana gani kuma. Tabbas maganganunsa sun fi guba dafi a cikin zuciyarta amma ya ta iya, idan ta furta wata maganar jikinta ne zai gaya mata kuma sai ta yi nadamar maganar koda kuwa tana da gaskiya. Hakan yasa ta tattara kukanta da duk wata maganarta tabarwa ƙasan ranta tasan ita ce mafita gareta. Kamar daga sama ya jeho mata wata tambaya, "Madam  me yasa Mamarki ke son na sake ki a wannan lokacin? Shin bata san cewar ba a zaman jira na ba ni? To wallahi ba zan sake ki ba, haka zalika ba za ki sake zuwa gidan nan ba, duk wanda ya zo daga can kuma ki gaya masu nace a daina zuwa min gida saboda na lura munafurci ke kawo su da neman su zuga ki, kuma wallahi ke za su kai su baro ba ni ba, domin kuwa ni abin da kawai na yi niyya shi nake yi ba wanda wani ya saka ni ba.  Sannan kuma maganar da zan gaya maki a kan haƙƙina shi ne zan dinga yi sau ko uku ne a duk lokacin da na ji ina buƙatar jin lagwadarki. Kawai ki dage ki dinga yi min wasu dabaru waɗanda ba dole sai na je ciki ba a nan waje zan ƙoshi na gamsu kamar na je duniyar sama. Nasan kin gane abin da nake nufi ko sai nayi maki dalla-dalla sannan za ki fahimci me nake so ? Kodayake akwai mafita mai kyau, ya ɗauki wayarsa ya shiga wani video ya bata "ki kalla ga yanda ake komai nan a sauƙaƙe, ki lura da kyau ba cizo ake ba kar ki samu tsoka ki daka mata haƙora ki kashe ni da gangan ni ban kukan daɗi ba nayi na masifa, wallahi ba wani ɓoye-ɓoye sai na rama yarinya don ba a wasa da ruhi sam. Dariya ta so ƙwace mata amma saboda gudun masifa yasa tai shiru kawai tai kamar kallon take da gaske, amma ba abin da ta tsana irin wannan kallon dolen da yake sa tana yi na dole.  Ya dube ta ya yi miƙa ya ce,  "Madam a fara gwaji man naga ko kina ganewa."  Saboda ya ce gwaji kuma ba shigar ta zai ba yasa cikin daɗin rai ta fara gamsar da shi ta hanyoyi masu sauƙi, kuma ta ji daɗin yadda saƙon ke shigar shi sosai, duk ya cika falon da nishi da ihu lamarin da yake bata ƙwarin gwiwar bijiro da wani sabon salon.  Sai da suka natsu ya dube ta ya yi murmushi ya ce, "Munafuka ashe kina iya wannan lamarin mai shegen daɗi amma kika bar ni ina ta wahala ni kaɗai?"  Sunne kai ta yi a jikinsa alamar jin kunya. Da sauri ya ɗago mata da kai, ya ce,  "Haba Madam me ye haka, kunya a gidan Nafi'u kuma? Lamarin kamar na yi maki Allah Ya isa ma wallahi domin zagina ki kai wallahi kai tsaye."  Ita dai bata ce komai ba, sai ta zame jikinta ta nufi toilet domin tai wanka. Bayan ta kimtsa ta fito cikin doguwar riga ya ɗago ya bita da kallo ya taɓe baki ya ce,  "Madam ba fa zan yadda ba, haka kawai ki dinga zama da kaya a cikin gidana ina dalili kawai ki aje su idan za ki fita kin saka amma daga yau indai ina cikin gidan nan ki dinga tsayawa a zigidir ki dinga kai da kawowa a haka ina kallonki ina ƙarewa kuɗaɗena kallo domin ban manta iyayen kuɗaɗen da na kashe ba da zan wabto ki daga gidanku ba, hatta masu taimaka min da du'a'i ba ƙaramin lashewa su kai ba.  Sannan don an raina ni sai a dinga yawo da kaya cikin gidana bayan kin san  babu mai shigomin gida daga ni sai ke amma sai a dinga ɓoye min halalina don mugunta."  Ta dube shi ta dubi jikinta tabbas duk wata hanyar da Nafi'u yasan zai baƙanta mata rai ya santa, ko indiyawa  na yawo yadda ya ce ne su da suke ma da jiki mai kyau misali balle mu Hausawa da ba laifi mun fi su cikar jiki ko'ina ɓul ba laifi.  Amma da yake ba wani zaman gidan yake ba sai ta ji sauƙi ta koma ta ciro rigar ta dawo, tana fitowa ya fashe da dariya ya ce,  "Kambu! Madam dama haka kike wai ? Na rantse da Allah daga yanzu duk wadda zan aura sai na ganta a zigidir domin kar a cuce ni." Bata abin cewa don haka tai banza da shi kawai, amma sai ya ce, "Ta shi ki je baƙin ƙofa ki dawo ko sau biyar ne, kina yi kina ɗan juya min duma-dumai na."  Salati kawai Fati ke yi a ranta, watau yau dai Nafi'u ya rantse sai ya ci ubanta a sauƙaƙe , bata san ya sake kawo mata tsirfar don haka ta tashi ta yi abin da ya ce, ya kuwa dinga ihu yana ɗaga ƙafa irin abin ya yi mai daɗi, tsabar iskancin Nafi'u sai kawai ya ci gaba da waƙar,

"Saka ɓurna ɓa ɓurna."

Tana gamawa sai kuma ya kunna kiɗa wai tai mai sexy dance tana juya ko'ina amma tana yi tana shafa shi.
Hankalinta ya tashi tai tsaye duk wani nishaɗi yabar jiki da zuciyarta domin tana ga bayan musguna wa har da cikin jikinta yake son zubarwa domin ya sallame ta da wuri, ita kam ba zata taɓa barin hakan ya faru ba. Tabbas tana son Nafi'u duk mugayen halayensa tana sane kuma tana jin haushin su amma bata shirya rabuwa da shi ba, so take ta kafa tarihin gaske a rayuwar Nafi'u na yin rayuwar har abada a gidansa. So take yai ta zaman jiran lokacin sakinta ita kuma za tai ta zaman jiran shiryuwarsa. 
Murtuke fuska ya yi yai magana da tsawa-tsawa, "Ke nake jira fa, na rantse da Allah idan ba ki yi rawar nan ba sai na kawo wadda za ta koya maki kuma a zigidir zata koya maki rawar, duk abin da ya biyo bayan koya rawar kar ki zarge ni ki zargi banzar zuciyarki, zan ƙirga goma ki fara idan ba haka ba kanki za a ji ba Nafi'u ba."


                      ***************

                  GIDAN AUDU NIƘA


Yau kowa ta kanshi yake a gidan, ba wani motsi daga kowa, don dama yaran su ne ke ci da gidan duk wata buƙata su ne ke yinta, tun daga biyan kuɗin wuta, ruwa da kawo abincin da za a dafa duk su ne ke kawo wa. Duk ranar da ba su kawo ba to ranar iyayen sun kama faɗa da zagin su kenan suna cewa ba su ga amfaninsu ba, wannan wace irin haihuwa ce ace yaro ba zai maka duk wani abu ba na jin daɗin rayuwa ba, bayan kai ne silar zuwansa duniyar baki ɗaya. Hakan ce ta faru yau, dukansu ba mai ko sisi ga yunwa suna ji ga ba wadda aka aiko kira kowace sai kiraye-kirayen samari take amma ba wanda ya biyo kiran saboda duk wanda aka kira yasan kuɗi ne za a roƙe shi. Ga yanayin na yanzu sai hamdala su kansu 'yan iskan ba shegun a wajensu duk Tinubu ya natsar da kowa sai fa masu ƙarfin hali su ma ba su wuce idan sun yi su ba da ɗari biyar ko dubu ba. Wani lokacin ma haka nan su ke karawa su yi a kyauta su kama gabansu. Nafisa ta dubi A'isha tace, "Wai ke A'isha jiya ina kallonki kina min dube-dube a cikin kayana kamar kin ban ajiya, ko lafiya?"    Wadda aka kira da A'isha tana kwance ta tashi zaune cikin hayagaga tace,  "Zan ci uwar yarinya don ubanta tun da ba sa'ar yi na bace ba ita, uban me ke gareki da har zan duba kayanki, ban da ma kin raina min hankali ni kaɗaice a cikin ɗakin da za ki ce wai kin ganni, uwar gani na ki kai... Hadiza dake kwance yunwa ta ishe ta, ta watsama A'isha harara tace, "Ke jakka kin ishi mutane da wasu 'yan iskan maganganu ki bar mutane da abin da ya ishe su ma."      Aishar ta yatsume baki ta dube ta a wulaƙance tace,  "Ke kuma a suwa kare da gudun layya? Kuma ke ce ƙatuwar jakka ba ni ba, ubanwa yasa da ke a cikin maganar nan, ban da shegen shisshigi da ƙwala  kai a faranti uwar wa ya sanya ki a cikin maganar nan? Ban san iskancin banza ni yanzu na tashi a buga a ga wanda za a ci da yaƙi... Taja wani uban tsaki tana gyarawa saboda kar ta kwana kar a shammace ta.
Mamarsu na jin su amma ko ƙala bata ce ba sai ma harara da take watsa masu kamar su duka haushin su take ji.
Uban ne ya leƙo ya dubi uwar ya ce,  "Ba wani abu nan ne, yunwa nake ji wallahi  na yi neman gidan buki ko suna babu ke wallahi yau har gidan mutuwa na nema ban samu ba don dai kawai na je na cika cikina."  Ta watsa mai harara tace,  "Sannu Audu, watau ka je ka gama yawon gararanbar taka ba malashi shi ne jagwal-jagwal ka kwaso jiki ka dawo nan ka ci banza ko? To babu ai ni ma nan cikina kukan yunwa yake jikan ko kai ko waɗannan yaran nake."  Ya ida shigowa sosai cikin ɗakin ya ce,  "Ke Asabe ban san iskanci aikin Gwamnati nake da zan dawo da abinci ko kuma na dinga ci da ku kullum? Kina gani fa nan-nan na samu sakin Wawa naso na aure ta amma na buga ko'ina ban samu kuɗin sadaki ba, kuma har lefe ta yafe min don ƙaunar da take min na zo na tara yaran nan na yanka wa kowacce abin da za ta ba da saboda mugun baƙin halinki ki ka hana su  tara min kuɗin sadakin ina ji ina gani na bar garar nan ta halalina kin sa yanzu sai ta buga-buga nake samu ina kashe gobara ta da ita." Ta kau taso har zanenta na neman ɓallewa ta cakumi rigar shi tace,  "Daman malam ya gayamin kana tare da shegiyar nan ita ce ke ƙwaƙule duk samunka shi ya sa baka kawo  ko sisi to wallahi yau ba sai gobe ba ni zan maka maganin duk wani iskanci dake yawo bisa kanka... Ya buge mata baki ya fizge rigar shi data riƙe ya ce,  "Ke Asabe har gobe ruwa na maganin dauɗa ɗan ubanki...sai rigima ta kaure tsakaninsu suka kama buga-in-buga, ta gefe guda kuma su ma yaran sun kaure da rigima abu dai ya girmama har ƙofar gida, mutanen unguwa dama tuni sun daina shiga sabgar mutanen wannan gidan domin kowa yasan yadda su ke zaman kansu yaran ke yi iyayen suma hakan take ba wanda ke girmama wani a kaf gidan, ga shi Allah Ya ba su duk mata, kuma kyawawa sai suka daina komai suka dawo da burukunsu  kan abin da yaran ke kawowa saboda kodayaushe ƙofar gidan cike yake da maza masu zuwa zance gun yaran gidan. Sai da sukai mai isar su sannan suka koma cikin gidan duk sun  yaga wa juna kaya ba iyayen ba haka zalika ba yaran ba.  
Nafisa ta ɗauki sabuwar wayar da Nafi'u ya sai mata ta kira shi, bugu ɗaya ya ɗauka, "Ya ne kayan lambuna masu zaƙi ya ake ciki ne, ko kina son ganina ne da gaggawa abin ya motsa?"    Tai dariya tace, "Ƙwarai kam abin ya motsa har yana dukan headquarter ta yanzu haka?"   Wani uban nishi ya ja ya dubi Fati dake tsaye kamar gunki ta kasa rawar da ya saka ta, sai kawai ya saka wayar a amsa kuwwa (handsfree) domin Fati ta gane babu abin da zai nema bai samu ba a gun mace, asalima kiransa ake ana neman ya taimaka ya je ya kwashi ruwa a banza shi ne ke jan aji ma, sai ya sake narke murya ya ce,  'Beb rawa nake so ai min mai tada hankalin nan... Bai ida maganar ba Nafisar tace,  "Lah ai ta zo gidan sauƙi kawai ka zo mu je na yi maka rawa har sai ka kai geji Beb, mu rawa a gunmu irin wannan ai son ta muke domin ko banza tana ƙara mana kasashin bala'i balle yanzu da nake a cikin yanayin neman taimakonka Beb."   Shiiiiiiit ya ja numfashi yana kallon Fati hannunsa a Nigeriarsa yana wasa ya ce,   "Kawai ki ban minti biyar zan zo idan har ba ai min abin da nake so ba a nan tabbas zan zo ai min a nan, duk kin fara tada sojojin yaƙi na ma yanzu haka ɗan yi min kukan nan na ji sauƙi Beb."
Nafisa ta waiga ta ga Hadiza ta tsira mata ido ta maka mata harara ta juya mata baya ta maƙe murya ta fa kukan iskanci. 
Nafi'u ya kama cewa,   "Ohhh Beb za ki kashe ni! Beb ina yinki, wayyo Beb kin iya fa sosai. Wow Beb daɗi, kin iya kukan daɗi Beb ci-gaba man."

Fati ta rugo da gudu ta rungume shi ta baya ta fashe da kuka tana cewa,  "Don Allah kai haƙuri ka daina ba zan sake ba, zan duk abin da kace ka ji mijina?"  
Ya yi kamar bai ji ta ba ya ci-gaba da wayarsa kawai. 

Fati ta tashi da sauri za ta kunna kiɗan sai kuma tai tsaye zuciyarta na raya mata sabuwar mafita. 
Ta waiga ta kalli yadda ya bararraje yana iskanci a cikin wayar sai kawai ta fasa ƙara ta sulale ƙasa.

Nafi'u ya waigo da sauri ya kalle ta, yaga ba jini sai kawai ya ce ma Nafisar yana zuwa ya kashe wayar ya buɗe Fridge ya ɗauko ruwa mai sanyin gaske ya buɗe robar ya sheƙa mata su a jiki. Dole tai firgigit ya ja numfashi ta fashe da kukan takaici tace, "Yanzu don Allah abin da kake min akwai adalci a cikinsa? Kodayaushe kai burinka ka ɓata min rai, don Allah ka daina zubawa zuciyata mugun dafi akan rayuwar aure, tabbas ina jin nadama da takaicin aurena amma na kasa samun mafita akan komai kuma duk kai ne ka toshe komi ka hanani samun sauƙi. Na ji zan rabu kowa nawa amma kai min alƙawarin kaima zaka rabu da duk wata mace da kuke tare don Allah."   Wani banzan kallo ya maka mata ya ce,  "Amma dai ba a taɓa ɗaukata luƙeƙen ƙaton sakarai ba sai ke a yau, watau a tunaninki mata nake bi?  To bari ki ji sai Allah Ya sakamin akan wannan maganar domin ni ban bin matar kowa sai wadda take a sake ba nauyin kowane ƙato a kanta, ke ban da kin maida Ni sakarai ma me zan yi da kayan da wani ƙato ke ta lakuta shekara da shekaru, to na ki uban me a ciki? Ai ni da kike gani sai ɗanyar kaza budurwa ita ce kawai nake samun abin arziƙi idan na je lakuta ko ita ma sau ɗaya nake kai kaina sauran zuwan duk ita ce zata kawo kanta domin ki gode wa Allah Ya baki mijin da yasan kowane style na zuwa duniyar sama. Nasan ko rantsewa nayi kaf  unguwar nan babu mai gamsar da matarsa irin yadda nake gamsar da ke, ki tuna fa sai na wanke ki tas, na shafe ki tas da zuma haka zan bi kaf jikinki na lashe da harshena ban jin komai zan saka bakina a headquarter ki na lashe maki ita tas na dawo gun 'yan biyuna suma haka nake ɓata tsawon lokaci ina sha maki su domin na lura ke nan ne makunnin zuwanki duniyar sama, amma duk ƙoƙarin nan nawa baki taɓa gode min ba, ko kuma ki ware rana guda ɗaya tal ba ki rufe gidan nan kice min kar na je ko'ina yau haƙƙinki kike so. Ki baje min komai na shiga alheri, saboda mugunta da shegen son kanki, bayan ina ƙoƙarin aje maki kayan da za ki ci ki ƙara tumbatsa ki sake tara min mai daɗi. Shin wai Fati me kike ɗaukar kanki ne ma wai? Sau nawa ina ce maki ban san kina shiga tsakanina da kayan lambuna na waje ne? Yau da ace ina maki ƙauro ne ko kuma ban sakar maki ita kina kwasar ganima sai ki gayamin amma kodayaushe nike bin ki da alherin baiwar Allah kina gujewa fa. To kashedi na ƙarshe akan maganar kayan lambuna idan kin ga dama ki ce baki ban idan na zo amsa ki ga yadda za mu kwashe ta dake, ai kin san dai ni ba irin sahoramin mijin da sai yadda matarsa tai da shi ba ne a shimfiɗa ba ko?  Ya ja tsaki ya tsallake ta ya shige ɗaki, bai jima ba ya fice fes da shi yasa kai ya bar gidan. 

Fati ta ji wani ɗaci sosai a ranta, wai me yasa ita kuma tata ƙaddarar rayuwar ta zo mata a kan mijin aurenta ne? Me yasa kodayaushe bata samun karsashi da damar buge Nafi'u a magana ne? Tabbas dole ne ta rayu da Nafi'u irin rayuwar da kowace matar aure ke yi da mijinta ko da hakan na nufin bin shawarar Asiya ne, ta gaji da gashin da Nafi'u ke yi mata a cikin gidan nan. So take ta zama kamar kowace mace a cikin gidanta tsakaninta da mijinta yana ganin daraja da kima tata, miji na jin tsoron aikata abin da zan matarsa zai ɓaci ko da ace hakan zai sa ta rasa komi nata ciki har da yaran da take sa ran haifa to za ta haƙura idan ya so idan Asiya tai aure ta haihu ta bata ko ɗaya ko biyu ne yaran sun ishe ta. Tabbas ta gaji da rayuwar aurenta da Nafi'u haka sauyi take so, sauyi take nema ta kowane hali kau sauyin nan nemansa take. Zumbur ta miƙe ta nufi cikin ɗaki bata ɓata lokaci ba ta shirya tsaf da nufin zuwa gidansu gun Asiya domin ta rakata gun malamin da ke ma Yayar ƙawarta aiki itama yasa ta cikin jerin mata masu ƙyalli a idon mazajensu.  
Tana zuwa bakin ƙofar fita gidan ta ji baki ɗaya hankalinta ya tashi ta rasa me ke mata daɗi sam bata iya ko kama ƙyauren ƙofar gidan balle ta buɗe ta fice, bata san kukan miye ba kawai ta tsinci kanta tana ta faska kuka a gun. 


         Nafi'u kau yana fita bai za me ko'ina ba sai gidan da ya kama ya turawa Nafisa saƙon ta iske shi can ya yi gaba. Bata ɓata lokaci ba ta tashi ta shirya tana maka wa sauran 'yan'uwanta harara sai kuma ta fashe da dariya, ita so take ta nuna masu ta fisu farin jini da kasuwa. Kaf cikinsu babu wadda ta kai Amina ko faɗan ɗazun da akai abin da yasa bata tanka ba saboda yunwar da take ji ne ga shi ta cire ciki ta sha magani ba kuma abin da ta ci don haka tai banza da su bata tanka wa kowa ba, amma da ace lafiya-lafiya ita har uwarta shigar wa faɗa take idan suna yi da uban ba abin da ya shafe ta. Ta dubi Nafisar cikin galabaita tace "Idan za ki dawo don Allah ki ranta ɗari biyar ki sawo min gurasa, idan kina da nauyi ki ƙara min da tsiren dubu ɗaya kan kirasar idan na fita da dare na dawo zan baki kuɗinki." Sanin hali yafi sanin kama, don haka sai ta ce, "Shike nan zan dawo maki da abin da ya samu, amma dai kin san da cewa Nafi'u bai bada kuɗin kirki ko? Da dai ace ma wani ne daban sai na ci nace a ban wani na taho da shi, to shi sai a hankali bai da sakin hannu kin kuma san hakan."  Amina ta haɗe wani miyau da ya taho mata, yaushe rabon da Nafi'u ya neme ta, har ta manta ko kiranshi tayi sai ya dinga yi mata kame-kame ko ya ce mata yana da abin da zai yi saboda kawai ya dawo gun ƙannenta, ya kamata ta ɗauki mataki akan yarinyar saboda ta lura duk namijin da ya zo gunta sai ya koma gun yatinyar, idan tai sake sai an wayi gari ta rasa kowa mai zuwa gunta sai dai ta gani ana zuwa gun ƙannen nata, don haka ba zatai zaman jiran wannan baƙar ranar ba, tabbas za tai zaman jira amma na ganin yarinyar ta rasa masinsi ko ɗaya... "Wai ke Amina ana maki magana kin banza da mutane kuma sauri nake yi fa." Cewar Nafisa tana hararar Aminar, uwar tai caraf tace,  "Tun da ta gaya maki ba shike nan ba, kuma yaron da kika ce ba gunta na san shi ba ma wai?"  Nafisa ta fice tana gyara hijabinta bata ce komai ba domin bata da wannan amsar. 

Har ya cika ya batse wai ta shanya shi, da ta gaya mai bata da lokaci ai da ya kira wata,  ta dinga ba shi haƙuri,  da ƙyar ta samu ya sauko, yunwa take ji sosai ta so ace abinci ya fara bata kafin ya fara leƙewa duniyar amma kamar mayunwacin zaki haka ya durfafe ta sai kawai ta biye mai cikinta na kukan yunwar gaske.  

        ************************

  Nusaiba na zuwa gidan Kursis ta amshi wayar yaronta babba ta kira, amma bata shiga duk wayoyin yaran ta amsa ta kira amma amsar ɗaya ce ake gaya mata 'is not richable at the moment' ta zauna ta dafe kanta, ta rasa me ke mata daɗi, ta rasa ina za ta je, ita fa tana son cikinta kuma ba zata juri fushin Kursis ba a kanta ba. Ganin bata da mafita yasa ta kwashi motar ta je gun da suke siyen kayan mayensu ta kwasa ta nufi wani hotel dake lungu ta kama ɗaki ta shige ta sha iya wanda za ta iya sha ta baje kan gadon tana sambatu irin na masu shaye-shaye har barci ya ɗauke ta a hakan.
Ba Nusaiba ta tashi ba sai da ta shafe awa biyar tana a buge sannan ta tashi tai wanka tai oder abinci ta ci ta sha lemu ta fito fes da ita kamar ba ita ce a yanayin maye ba ɗazun, maimakon ta tafi sai ta kira wata yarinya dake jami'a tace ta zo ta same ta nan ta tura mata kuɗi tace ta zo masu da kayan lambu. 
Ba jimawa kau sai ga yarinyar ta zo ta ƙwanƙwasa ta je ta buɗe mata, suka rungume juna suna tsotsar bakin juna a haka har suka faɗa kan gado kayan da yarinyar da shigo da su suka watse a tsakiyar ɗakin. 
Nusaiba ta ƙware da bi da kowane jinsi ba mazan ba haka ba matan ba, da gaske take ta koyi abubuwa da dama daga gun Kursis amma a matsayin yanzu sai dai ita Kursis ɗin ta koyi sabbin style daga gare ta domin kowace rana sake samun sabon samfur take na lamarin. Sai da su kai nisa da iya shegensu sun ma manta da sam basu rufe ƙofar ba kawai shigowa akai ɗakin ba su ma san an shigo ba. 
Yau rana ta ɓaci 'yan hisba ne suka kawo sumame a cikin hotel ɗin cikin dace suka iske su Nusaiba a cikin wannan halin. 
Sai da wani ya maka ma Nusaiba duka sannan ta dawo hankalinta har yarinyar suka ga mutane kewaye da su. Nusaiba gabanta ya faɗi ganin wani cikinsu na yi masu video amma don ƙarfin hali ta dubi wanda ya maka mata duka ta ɗauke shi da mari mai kyau tace,  "Wallahi ba zaka daki banza ba, saboda ba uwarka ta haife ni ba, ko uwarka ta haife ni baka dukana na ƙyale ka balle haɗuwar hotel.  Ta watsa wa sauran kallo tace,  "Wace uwar ce ta kawo ku room ɗina? Ko akwai ƙaton da na aikawa da alewar gayyata ne? Tabbas a yau za ku yi nadamar gani na a gun nan domin sai na sa an yi maganinku daga can inda kuke taƙama ɗin, shegu ƙananan 'yan iska an gaya maku bamu san duk bula bace ba? Sai ku zo da wata shegiyar mota ku ga 'yan hisba wai kuna da'awa sai kun kwashi 'yan mata ku je ku kai su office ɗinku duk ku cinye su, waye bai san abin da kuke ba eye?" Ta daka masu tsawa tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya ranta a ɓace. Ganin duk sun yi shiru ba wanda ya ce ƙala tace, "Okay mu je can ɗin za ku ban ama ne." Yarinyar dai jikinta sai rawa yake amma ita Nusaiba ko a jikinta nema take ma su tafi office ɗin.  Biyu daga ciki suka ware kome suka ce oho suka dawo suka ce,  "Hajiya ba wani ɓoye-ɓoye sai gaskiya mun kama ki kawai amma dai kina iya bamu na mai sai mu koma inda muka fito kawai." 
Ta yi dariya tace, "Shegun sama, ba za ku ci ko sisina ba sai dai ku ci daga wanda kuka tara, ta jawo wayarta ta kira wata number tasa wayar a handsfree tace,  "Hello, ina san ka sakamin kuɗi a Opay ɗina yanzun nan kar ka ɓata min rai kuma."  Cikin mamaki suka tsinkayi muryar shugaban da'awa na marairaicewa yana bata haƙuri da alƙawarin yanzun nan zai saka mata tai haƙuri. Ta yamutse fuska tace, "Sai na gansu yanzun ɗin." Ya ce, "Yanzun nan ranki ya daɗe, amma don Allah hukuncin da ake min a duba ni haka nan na tuba ko da na mintina ne a taimaka aban don Allah." Ta fashe da dariya ta kashe wayar.
Kafin ta gama wayar ashe sun fice saboda akwai yaronsa guda ɗaya a cikinsu, don haka baki alaikum suka bar gun ba ko waige.

Nusaiba ta ja tsaki ta dubi yarinyar tace, "Za ki iya tafiya na saka maki ta Opay ɗinki, sai wani time kuma." Yarinyar tai godiya ta fice daga ɗakin tana jinjina rashin daraja irin na matar nan.

Nusaiba ta sake komawa kan gadon tana jin wani sabon feeling na tsiro mata domin ko rabin kaiwa geji ba tai ba, wannan karon kuma ba mace take so ba namiji take so, tai wuf ta ɗauki wata wayar ta kira wata number, "Hello Oga ina a hannu yau dai damar taka ce kana gari?" Daga can wata ƙatuwar murya tai ihu ya ce,  "Please kina ina, yanzu na zo wallahi nima a hannu nake kuma ke ce kawai za ki iya kai ni bango gayamin ina za mu haɗu?"  Ta ja wata siririyar dariya tace,  "kai ma kasan ba zan kama maka ɗaki ba don kawai ka zo ka bugi tudu da kwari ba oga idan ka kama mana ɗakin ka turomin address ina jiran ka idan kuma kai wasa na kira nawa ogan ya ja rabage ehe."  
Tana kashe wayar sakon inda yake yana shigowa a cikin wayarta don haka ta miƙe ta fice kanta a tsaye ta nufi hotel ɗin da ya turo mata.

Daidai bakin fita daga lungun su kai kicibus da Jabeer cikin tashi motar su biyu shi da wani ya yi mata fitila ko a jikinta ta raɓa su ta gefe ta wuce tana ganin sai ɗaga mata hannu yake alamar bye-bye ta ja tsaki. 
Abokinsa Jabeer dake zaune yana kallon ikon Allah a gaban motar Jabeer ya ce,  "Wai ba matarka bace waccan ta wuce mu ba?"  Jabeer ya yi murmushi domin duk lokacin da aka ambaci sunan Nusaiba aka ce matarshi ji yake ya fi kowa farin ciki da dacen samun mace. Yana murmushin ya ce, "Nusaiba ce man baka ga na ɗaga mata hannu ba?"  Abokin ya ce, "Indai ita ce na yi mamakin ganinta a irin wajen nan saboda nan daga gidan student sai hotel kuma kowa yasan hakan."    Jabeer ya ɓata fuska ya ce,  "Tabbas haka ne amma kai me ya kawo ka wajen idan haka ne?"  Jin tambayar Jabeer tasa Auwal kama bakinsa ya yi shiru, amma sai da Jabeer ya sake maimaita mai tambayar don haka ya ce,  "Mun zo ne mu gama magana da Alh. Lawal kan aikinsa da ya bamu." Jabeer ya ce,  "To itama ina kyautata zaton hakan ce ta kawo ta nan ba mamaki ma kasuwancin da ya kawo ta yafi namu samun riba saboda jarinta yafi namu kauri."  Auwal cikin sanyin jiki ya dube shi ya ce, "Haka ne Allah Ya taimaka, ka yi haƙuri idan maganata ta ɓata maka rai."

Duk abin da suke cewa a kunnen Nusaiba domin ta dasa mai recorder a cikin motarsa duk wani motsinsa a cikin motar ta sani. Jin abin da ya faru yasa ta karya motar ta fasa zuwa inda ake jiranta kai tsaye ta nufi gidan Malam Habu, domin ta tsani wani ya saka mata ido akan rayuwar ta, ita fa a ganinta rayuwarta tata ce ba mai iko da ita don haka duk wanda ya shigo tsakaninta da rayuwarta sai ta ji dalilin shigowarsa.  Tana zuwa gidan cike da mutane har a waje amma da yake malam yasan da zuwanta sai ga shi an aiko ta wuce kawai, abin da ya jawo ka-ce-na-ce a gun mutanen da aka iske a gun. 
Ta ja tsaki ta wuce tana masu kallon uku saura kwata.  
Malam Habu ya dube ta ranshi a ɓace ya ce, "Kina kusa da shiga cikin tashin hankali wanda ke ce silar faruwar komai,  kin san kau me kike shirin ja ma kanki? To ki sani bala'i yana tafe gareki nan ba jimawa ba. Karanto min alƙawarin da mu kai da ke."  Nusaiba ta ruɗe cikin firgici ta fara zayyano alƙawarin da su kai da malam Habu kamar haka...


Ko wane irin alƙawari ne wannan za ta ce?


Haupha