Ciwon Sanyin Mata Da Ake Dauka Ta Hanyar Jima'i (STD/STI)

Haka kuma za'a yi iya samun cututtukam sanyi ta wata hanya da ba jima'i ba kamar ta hanyar ba da jini ga marasa lafiya wato jini mai dauke da cutar sanyi daga wani mutum, ko haduwar jiki fata da fata mai dauke da cutar ta fashe za ta iya harbin fatar wani mutum mai lafiya da cutar ta jini ko ruwa a jiki dake a jikin fatar mai cutar zuwa fatar wanda bai da cutar wato idan akwai ƙofa budaddiya komin kakantarta zuwa cikin hanyoyin jinin wanda baya da ciwon a fata zai iya samun cutar, misali ta hanyar sunbata ko tsotsan alauran me ciwon, kota hanyar sa tufafin sawarsa, kamar  Pant me dauke da kwayar cutar mai rai ,ko ta hanyar amfani da reza wanda wani yayi amfani da ita,reza mai dauke da kwayar cutar mai rai ,da kuma wasu hanyoyin na daban. Atakaice kwayoyin halittun  cutar ana yaɗa su ne daga wani mutum zuwa wani ta jini, maniyy, ruwan farji ko ruwan jiki.

Ciwon Sanyin Mata  Da  Ake Dauka   Ta Hanyar Jima'i (STD/STI)
MOMMYN MUSAB SPECIAL  GROUP ONLINE TRAINING 
                 & 
  GYARAN JIKI
 
SPECIAL GROUP TRAINING  PROGRAM 
 
 
 
 
Ciwon sanyi cuta ce da aka fi yadawa ta hanyar jima'i waton hanyar saduwa, shiyasa ake kiran dangin cututtukan da turanci da suna SEXUALLY TRANSMITTED DISEASES/SEXUALLY INFECTION (STD/STI)
 
CUTUTTUKAN DA AKE YADAWA TA JIMA'I 
 
Ciwon sanyi an fi yaɗa shi ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu dauke da ciwon su sakawa mazan  ciwon.
 
Ciwon yafi yaduwa kuma an fi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje 
 
Haka kuma za'a yi iya samun cututtukam sanyi ta wata hanya da ba jima'i ba kamar ta hanyar ba da jini ga marasa lafiya wato jini mai dauke da cutar sanyi daga wani mutum, ko haduwar jiki fata da fata mai dauke da cutar ta fashe za ta iya harbin fatar wani mutum mai lafiya da cutar ta jini ko ruwa a jiki dake a jikin fatar mai cutar zuwa fatar wanda bai da cutar wato idan akwai ƙofa budaddiya komin kakantarta zuwa cikin hanyoyin jinin wanda baya da ciwon a fata zai iya samun cutar, misali ta hanyar sunbata ko tsotsan alauran me ciwon, kota hanyar sa tufafin sawarsa, kamar 
Pant me dauke da kwayar cutar mai rai ,ko ta hanyar amfani da reza wanda wani yayi amfani da ita,reza mai dauke da kwayar cutar mai rai ,da kuma wasu hanyoyin na daban.
Atakaice kwayoyin halittun  cutar ana yaɗa su ne daga wani mutum zuwa wani ta jini, maniyy, ruwan farji ko ruwan jiki.
*********
Kaman yadda kowa yadauka infection kawai shi ne sanyi, ba tare da sanin  infection   suna da banbanci: 
 
Alamomin ciwon sanyi ga mata sun sha bamban tsakanin mata da ciwon ya harba, haka ya dangantane da nau'in kwayar halittar cutar wacce ta hadda ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mace ma'ana alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin Marar lafiya. 
 
Hakan kuma, alamomin sun sha bamban ta fuskar tsanani ko  sauƙinsu ko kuma rashin ganin alama ko ɗaya duk da cewa  akwai cutar a jikin Mace. 
 
A takaice dai alamomin ciwon sanyi za su iya buya amma gwajin asibiti zai iya nuna akwai cutar ko akasin haka 
 
Alamomin ciwon sanyi na "toilet infection"na iya kama da alamomi cutar sanyi da ake samu ta jima'i(STD/STI) sai dai bambancin shi ne hanyoyin samuwar cututtukan, kuma cutar sanyi "toilet infection" tafi saukin magancewa, ita kuma cutar sanyi da ake yaɗawa ta jima'i (STD) nada wuyar magani da naci musamman sabida wasu nau'o'in cutar daga kwayar cutar "virus" ne (kamar syphillis da genital herpes).
********
Ga alamomin kamuwa da cutar sanyi kamar haka: 
 1. Fitar ruwa daga farji, ruwa mai kauri ko kilili, kalar madara ko kore daga cikin al'urar mace.
 
2.Kuraje masu durar ruwa da fashewa a farji musamman wurin da pant ya rufe 
 
3.Feshin kananan kuraje a farji ko cikinsa
 
4. Raɗadi zafi a lokacin yin fitsari 
 
5. Jin zafi cikin farji lokacin jima'i 
 
6. Zubar jinin al'ada mai yawa ko zuwan jinin al'ada mai wasa, waton akan lokacin da ya saba zuwa ba 
 
7. Ciwon mara 
8. Zazzabi
 9. Ciwon kai 
10. Murar maƙoshi 
11. kasala 
12. Zubar jini lokacin saduwa 
13. Daƙushewar sha'awa ko rashin sha'awa, ko daukewar ni'ima 
14. Bushewar farji
15. ƙaikayin farji
16. Warin farji (ɗoyi mai karfi)
17. Kumburin farji da yin jazur
18. Gudawa
19 Rashin gani. 
****************
Wata alama daga cikin wadda muka bayyana a sama a can baya mun yi  bayanin ciwon sanyin mata na toilet infection (vegunities:yeast infection &bacteria vaginosis) wanda cutar sanyin mara ce wacce ba'a yaɗawa ta hanyar jima'i wato sanyin mara wanda mace ba za ta iya harbi mijinta da cutar ba ,wanda aka fi samu daga "toilet"duk da haka ,munyi bayanin wata nau'in cutar sanyi guda 1(trichomoniasis)a cikin waɗancan bayanan da suka gabata ,wacce cuta ce da mace ka iya sakawa mijinta ciwon STD a wannan karon kuma za mu yi bayani ne ƙadai akan ciwon sanyin mata wanda akafi samunsa
 ko yadawa
 
 
Gwajin asibiti ne kawai zai tantance da kuma kalan maganin daya dace a sha 
 
Mommyn Mus'ab
 
07041105956
 
Share✅
Edit❌
Comment✅