DUHU DA HASKE: Fita Ta 24
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 24*
~Kasar Libya asibitin kansa ɗaki me number goma anan aka kwantar da manal bayan an gama mata aiki, babban likitan da yayi mata aiki ya shigo ɗakin komai na ɗakin me kyau ne kamar ba asibiti ba, ga gadon marasa lafiya ga kuma na waɗanda suke jinyan marasa lafiyan, man yana zaune a kusa da ita ya ɗaura kanshi akan gadon yayi shiru ya gaji sosai yau kwanansu huɗu da zuwa saida suka bata sharaɗin irin abincin da zataci na kwana uku kafin yau sukayi mata aikin, tun safe akayi aiki bata farfaɗo ba har yanzu karfe 8 na dare, man duk ya fita a hayyacinshi da kyar ma yanzu bacci ya saceshi, dr yace "hello..hello.. hello"
sau uku yana kiran man bai tashi ba, saida ya bubbuga gadon da ɗan karfi kafin yayi firgigit ya tashi, dr yace "very sorry abdool gaskiya na jinjina maka da irin kulan da kake bawa matarka a wannan zamanin da muke ciki kaɗan ne a cikin maza zasu kula da matansu irin yadda kake kula da matarka, Allah ya barku tare har karshen rayuwarku yasa mutuwace zata rabaku"
shiru man yayi bai amsa addu'an ba, murmushi Dr yayi yace "naga kana cikin damuwa karka damu matarka zata farfaɗo amma tana bukatan jini sabida haka zamu duba jininka idan yayi daidai da nata saimu sa mata"
a hankali ya gyaɗa kai idanunshi sunyi luhu-luhu ya faɗa sosai, tashi yayi yabi bayan Dr aka ɗiba jininshi aka duba kafin suka ɗiba wanda zai isa suka tafi tare, zama yayi domin jiri yakeji tsaban gajiya akayi fixing jinin ya fara tafiya kaɗan kaɗan, kyakkyawan fuskanta ya kalla, manyan idanunta da take kallonshi dasu yau a rufe suke, kallon karamin bakinta yayi wanda kullum sai tayi mishi kiss ko yana aiki ko yana free sai tayi mishi idan yaki tayi fushi har sai ya yadda, lumshe ido yayi yace "Allah ya baki lafiya"
tunda ya buɗe ido bai kara rufewa ba har karfe biyu da rabi na dare yana zaune kusa da ita, a hankali ta fara buɗe idonta ta sauke akan Abdool dake kallonta, kara rufe idon tayi sannan ta kara buɗewa a hankali, murmushi ta gani akan kyakkyawan fuskanshi, motsa hanunta tayi taji ya mata nauyi, cije ɗan karamin bakinta tayi sannan tace "ciwo nakeji a jikina my Abdool"
da sauri yace "sorry bari na kira Dr"
tashi yayi zai fita ta rike hanunshi, tsayawa yayi tace "kaine Dr ɗina my Abdool, idan kana kusa dani ina samun lafiya from no where, dan Allah kada ka tafi ka barni koda na minti ɗaya ne"
shiru yayi, ta bashi tausayi yadda take magana tana nishi da alama tana shan wahala sosai, yace "manal dr dole su san kin farka ko akwai abinda zasuyi miki please ki bari naje na kirasu kinji my baby?"
a hankali ta sakeshi tace "to"
fita yayi cikin jin daɗin ta farka yaje ya kira Dr, tare suka shigo dr ya fara dubata sannan ya fara mata tambayoyi tana amsawa, cikin tsawa yace "ke ana tambayanki kina bawa mutane amsa a hankali ba zaki buɗe baki kiyi magana ba ke kurma ce?"
kallonshi tayi ganin babu abinda tayi na ɓacin rai da zaisa ya hasala haka ta juya baya ta daina kallonshi, cikin tsawa yace "ba magana nake miki ba? zaki juyamin baya wacece ke?"
Abdool zaiyi magana ya ɗaga mishi hanu, shiru yayi, yace "ba zaki juyo ba? useless"
cikin wani irin fusata manal ta juyo tana aika mishi wani mugun kallo, take idanunta suka sauya kala zuwa jajur tana dunƙule hanu tace "kaine useless ni banyi kama da useless ba, sannan idan baiyi maka ba ka koreni a hospital naku"
yace "koda na koreki babu inda zakije ki samu sauki kamar nan sabida haka ya zama dole kimin biyayya jahila kawai"
tashi tayi daga gadon ta sauka cikin fusata tace "kaine jahili"
zuwa yanzu jikinta rawa yake, yace "ai kinsan kece kikafi kama da jahilai banza"
da ihu kamar zata fasa hospital ɗin tace "kaine banza, kuma wallahi"
hawaye masu zafi ne suka fara wanke mata fuska zama tayi a bakin gadon tace "get out"
murmushi yayi ya kalli Abdool yace "Alhmdllh ciwonta anyi nasara a aiki yanzu ta samu sauki, tunda babu aman jini duk da ranta ya kai kololuwan ɓaci kuma bata rike zuciya ba alaman yana mata ciwo, saide muce Alhmdllh dama haka muke gwada duk wanda muka yiwa aiki kuma muna gane munyi nasara ne ta wannan hanyan"
kallon manal yayi wacce ta sunkuyar da kai bataji komai ba saɓanin da idan ranta ya ɓaci sai taji aman jini yana zuwa mata, hanu tasa ta dafa kirjinta taji babu komai, murmushi yayi yace "yi hakuri manal haka muke gwada nasaran aikinmu amma Alhmdllh kin samu sauki"
murmushi me haɗe da hawaye tayi sannan tace "na gode dr"
kallon man tayi tace "na gode Abdool"
dr yace "Abdool Allah ya kara muku zaman lafiya da matarka gaskiya mijinki yana sanki domin ko rintsawa baiyi ba haka ya kwana ido biyu sabida ke"
murmushi tayi dr yace "to Abdool tunda matarka ta farfaɗo sai kayi bacci ko?"
murmushi kawai yayi kanshi a kasa, hanu ta mika mishi bayan Dr ya fita, yasa nashi a nata janyoshi tayi ta nuna mishi cinyarta tace "kwanta"
zaiyi musu tace "no please abdool kwanta idanunka sun sauya kala gashi kayi zuru zuru gaba ɗaya ka rame yanzu ba na samu sauki ba?"
gyaɗa kai yayi ya kwanta akan gadon tana daga zaune ya ɗaura kanshi a cinyarta, shafa kanshi take a hankali bacci ya fara fizganshi, ba jimawa bacci me nauyi ya ɗaukeshi, ido ta zuba mishi babu ko kyaftawa murmushi tayi tace "Abdool kayi hakuri ba zan iya haɗaka da kowa ba, yadda ka zama nawa tun daga farko haka zaka zama nawa har karshen rayuwa, Abdool wallahi ba zan taɓa barinka ba, wallahi Abdool duk ranan danaga zaka fita a rayuwata saide mu rasaka mu duka dani da ameesha"
murmushi tayi tana shafa sajenshi dake kwance tace "Abdool Allah ne ya samin sonka a zuciyata babu wanda ya isa ya cire sai ranan dana kwanta na mutu amma koda kaine ka mutu saina bika"
tana maganan har bacci ya ɗauketa.
Ameesha da sauri ta bawa baba megadi ledan fruits data kawo mishi da kaza me zafi sannan ta shiga ciki da sauri da wasu manyan ledojin a hanunta, sauri take cikin uniform ɗinta da alama yau tayi late ne sabida taje aiki, kai tsaye ɗakin ammi taje tana ganinta tayi murmushi tana sanye da kayan da ameesha tasa mata tun jiya, aje ledojin tayi akan gadon sannan ta fara cire babban rigan lauya dake sama tana cewa "Ammi ki gafarceni banzo da wuri ba yau wani case na fyaɗe muke yi a kotu amma Allah yasa munyi nasara an aika wanda ya aikata laifin gidan yari, hankalina yana wajenki dan nasan masu aikinki basa kula dake Atika kam ma guduwa garinsu tayi itada nake tunanin zata kula dake, badan ina zuwa kullum ba nasan da zaki fara wari ma ammi"
murmushi take mata har ameeshan tasa aje rigan tazo wajen tana naɗe ƙafan wandon dake jikinta na jinx, ɗaura ammi tayi akan wheelchair zata fara turata wayarta yayi kara da sauri ta amsa ganin sunan yazeed, tace "hello kasan me? yau naje wajen aiki tunda asuba ban samu daman fitowa ba sai yanzu, shiyasa ma ban kiraka ba kawai nazo gidan ammi sabida Inaso kaima ka huta yau, yarinyar da aka yiwa fyaɗe Allah yasa mun gama case ɗin harma an yiwa yaron hukunci, inada Imran? kace Imran ya ajemin abinda na bashi kada ya kuskura koda wasa ya taɓamin koda abu ɗaya ne a ciki sannan....."
cikin husky voice nashi yace "meesha baki gajiya da surutu ne? tun ɗazu fa da kika ɗaga wayan nan kike surutu baki barni ko magana ɗaya nayi ba"
turo baki tayi tace "to ai yanzu zanje nawa ammi wanka"
yace "to shikenan idan kin dawo sai muyi magana ko nazo mu koma tare?"
tace "eh kazo mota yana kofa ka jirani a ciki idan na gama saimu koma tare ko?"
yace "yes"
tace "good"
ɗit ta katse wayan ta wurga akan gado sannan ta fara tura ammi zuwa toilet, tace "kin san me ammi? a ranan dana fara zuwa fa kunnuwana sunyi min karya wallahi sai naji kamar kince min kin gode, to amma dana koma gida sai nayi tunanin ko dai tausayinki da nakeji yasa naji kamar kin fara magana? sannan kin san me ammi? ya yazeed yana kula dani sosai, su fahad da kuma Imran sun samu rayuwa me kyau harma fahad ya fara zuwa school, to amma abu ɗaya ke ɗauremin kaina shine fahad da yazeed basa yadda su saki jiki da momy wai sunce tayi kama da manal ƴarki shiyasa suke tsoron sakin jiki da ita, abin yana ɗauremin kaina, kuma kinsan momy macece me hankali gata kyakkyawa kamar balarabiya, gata da gashi ga rashin magana, kuma kinsan momy wani abu? da gaske tana kama sosai da ɗiyarki manal"
wankan tayi mata kamar kullum ta fito da ita, kayan bacci tasa mata sannan ta ɗauko abincin data kawo mata da fruit da kuma kaza wanda yake kashi, murmushi tayi mata ta ɗan waro ido irin na yara idan zasu baka abu surprise ɗinnan tace "guess what?"
ammi ta kasa ɗauke idonta akan ameesha, kullum idan tazo sai taji kamar kada ta kara tafiya tayi ta zama kawai tana kallonta, yarinyar tana da sa mutum dariya gata da fara'a kamar me kyautan dariya bata fushi sam, ice cream ta ciro daga leda tace "ice cream na siyo miki"
murmushi anmi tayi har hakoranta suka bayyana sunyi fari kal sabida brush ɗin da ameesha take mata kullum, ɗibowa tayi a cokalin ta kai bakinta, a hankali ta buɗe tasa mata, tace "amma fa ammi kamar kullum yauma kyautar yara zanyi miki tare zamuci dan nima yunwa nakeji kinga tunda asuba na fito banci komai ba shiyasa na siyo mana dayawa, kin san kullum mama tana cemin kada na damu da damuwata fiye da yadda zan damu da damuwan mutane shiyasa nake aje damuwata a gefe na fara solving na mutane"
tana bata tana ci itama ameesha tana ci, saida suka koshi tace "yawwa Alhmdllh mun koshi"
wayarta taji yana ringing tayi saurin ɗauka tace "ya yazeed"
yace "nazo fa tun ɗazu"
tace "gani nan fitowa"
da sauri ta tashi tana ɗaukan uniform nata data aje tace "ammi bye saina dawo gobe"
gani tayi fuskan ammi ya canja yanayinta ya zama abin tausayi, shiru tayi tace "kinga ko? zaki fara sa jikina ya mutu karki damu gobe zan dawo kinji?"
shiru tayi tana kallonta ta ɗaga mata hanu tayi mata alaman bye bye sannan taja kofan ta fita da gudu sabida yazeed yana jiranta, sallama ta yiwa baba megadi tace "baba sai gobe kada ka manta idan sun dawo ka sanar dani"
yace "to ƴata"
da gudu ta fita, yana zaune a motan ya kunna waƙa yana ji, yana kallonta tana gudu tana gyara karamin mayafinta kawai yayi murmushi, yaranta ya mata yawa wani lokaci, buɗe motan tayi tana nishin gajiya tace "wayyo ameesha yau kinga ta kanki, kin gaji sosai gashi an saki gudu kamar soja"
da sauri yace "waya saki gudun?"
nunashi tayi tace "kai mana"
kallonta yake batama san tayi karya bane sai aje kayan take a bayanta tare da jakanta, saida ta aje tace "ba zaka tada motan bane?"
yace "yaushe na saki gudu?"
murmushi tayi tace "awww na gane shiyasa kaki tada mota?"
tada motan yayi ya fara driving, sunyi nisa akan titin yace "meesha"
tace "na'am"
yace "meyasa kike ɓoye damuwanki?"
tace "babu wani damuwa fa meka gani?"
yace "kina kewan mama amma kina ɓoyewa sabida kada kisa mutane cikin damuwa, meesha kinaso kiga kowa cikin farin ciki koda ke kina cikin bakin ciki, kullum kina nunawa kowa hanyan da zaibi yayi solving damuwarshi ke kuma bakida hanyan solving naki, hakika kece irin wanda Allah yace mutane ne na musamman a cikin ƴan adam, Allah ya miki albarka ya cika miki burikanki"
tace "ameen ya yazeed"
hanan ce ta kirata ta ɗauka tace "Darling sis"
hanan tace "ina kike? nida su Imran mun fita har mun dawo bamu ganki ba"
tace "sorry yanzu muna hanyan dawowa yau case ɗin da mukayi ya bani wahala fyaɗe ne wani kato ya yiwa wata karamar yarinya, nayi niyan kiranki sabida ki duba yarinyar amma already an kira dr, wallahi hanan mutumin baida imani bai san ma yarinya ce karama ba saida yayi mata kaca kaca harma bata iya numfashi da kyau"
hanan cikin tausayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ina meyasa rashin imani yake karuwa a cikin al'ummanmu ne? meyasa babu tausayi a zuƙatan mutane? shiyasa idan Abba ya samu irin wannan case ɗin yake kashe makudan kuɗaɗe dan ganin an hukunta wanda yayi laifin, duk yawan karuwan da suke duniya basu ishesu ba sai sun haɗa da kananan yara? Allah ya shiryesu idan masu shiryuwa ne, idan kuma ba masu shiryuwa ba Allah yasan yadda zaiyi dasu"
tace "ameen hanan"
tace "keda wa kuke dawowa? naji kince kuna hanya"
tace "nida ya yazeed"
murmushi hanan tayi taji daɗi a ranta tanason ganinsu tare yadda suke shaƙuwa da juna yana mata daɗi zata so abinda take zargi ya zama gaskiya dako sai tayi kyautan mota a ranan data tabbatar"
jin tayi shiru tana murmushi ameesha ta katse wayan, yazeed yace "kinyi kokari Allah baki lada"
tace "ameen"
yace "amma sun biyaki kudi ko?"
girgiza kai tayi tace "naki karɓan ko naira biyar q hanunsu, sabida inaso nayi koyi da Abba na zama me kyauta da kyawawan hali"
suna hira har suka isa gida, ya rike mata rigan uniform ɗin suna tafiya tare har zuwa cikin falon, hanan tana kwance akan sofa ta ɗaura kanta a cinyar momy suna kallo, Imran da fahad suna zaune akan sofa suma suna kallon suna hira, momy sai murmushi take tana kallonsu suka karaso, ameesha ta kwanta itama ta ɗaura kanta a cinyar momy tace "matsa to tunda ba momynki bace ke kaɗai"
dariya momy tayi tace "ni momynku ne ku duka, dama akwai kayan dana sa aka kawo muku daga Egypt abaya ne me kyau sosai nasan zai muku kyau"
tare suka tashi sukace "ina yake?"
tace "yana cikin wardrob..."
kafin ta karasa suna rige rigen zuwa ɗauka kowacce bataso ɗayanta ta riga zuwa dan zata zaɓe wanda sukafi kyau, murmushi momy tayi tace "Allah ya shiryamin ku"
tace "yazeed nasa maka abinci?"
girgiza kai yayi ya tashi bai mata magana ba, jikinta yayi sanyi, tace "Imran fahad nasa muku abinci?"
duk suka tashi sukace "no"
tafiya sukayi suka barta ita kaɗai a falon, shiru tayi tayi tagumi, ameesha ce ta fara fitowa da zazzafan abayan data siya musu, ganin tayi tagumi tasan su yazeed ne suka ɓata mata rai, a hankali ta aje abayan a gefe ta rungume momy tace "nifa banson ganin momyna tana tunani"
murmushi tayi mata sannan tace "bana tunani fa ameesha na gaji da kallon ne kawai"
ji tayi jikinta ya kara sanyi domin momy akwai sanyin murya gata kalan tausayi, tace "kinci abinci?"
tace "a,a ina jiranku kuzo muci tare"
tace "ai ni a koshe nake momy naci abinci"
tace "hanan ma tace a koshe take"
ganin bataji daɗi ba da babu wanda yaci abincinta ameesha ta tashi ta ɗauko abincin tazo ta zuba musu ta daure ta rinƙa cusawa nan take momy ta sake suka fara cin abincin tare, ganin farin ciki akan fuskanta ameesha taji hankalinta ya kwanta, saida sukayi sallaman saida safe sannan momy ta rakata har ɗaki ta shiga ta kwanta, can dare yazeed ya kirata suka fara hira, hanan kamar me bacci amma ba bacci take ba banda murmushi babu abinda take yi.
*Duhu da haske is ₦400 ta account 8144818849 hauwa shuaibu mapi opay, evidence via 08144818849*
_jiddah Ce....
managarciya