MAMAYA: Cigaban Fitowa Ta Daya
*Shafi na daya.*
MADARASATUL IJJITIHADIL TA'ARIFUL DINIL ISLAM, shi ne sunan islamiyar da tayi fice a cikin garin Funtua da kewayenta, makarantace ta manya da yara, wacce ba laifi ana koya karatu gwargwadon ikon Malaman cikinta .
Malam Surajo shi ne shugaban makaranta, kowa yasanshi Malamine da bai da wasa gun koyawa, yana da tarin Malamai wadanda sune ke taimakawa wajen ba Ɗaliban makarantar karatun.
Kasancewar islamiyar ta yi suna ƙwarai, ya sanya aka hada kala-kalan yara cikinta maza da mata marassa adadi wajen lissafuwa.
Kamar yanda ɗabi'ar kowace makaranta take, haka itama Ijtihadi ana yima yara hutun rabin lokaci donsu fito su yi ciye-ciye da lashe-lashensu kafin a maida su azuzuwansu.
Dan-dazon yara na hango sunata siyen abubuwan motsa baki, cikin filin da aka tanada dan zaman masu tallan kayan makulashen yara.
Daga gefen gun wata shirgegiyar bishiyar kanya, yara maza da mata nata wasansu a karkashinta, basu ankaraba su ka ga wani ƙaton baƙin kare yana ta zazzalo halshensa waje a gabansu, da gudu yaran suka nufi wajen wasu jerin 'yan mata dake zaune saman katangar da aka gewaye masallacin makarantar dashi.
"Yaya Shema'u ga wani baƙin Kare can ya hanamu wasa a ƙasan bishiyar Kanya." (Su duka Yaran suka furta cikin nuni da inda bishiyar kanyar ta ke.
Wacce aka kira da Yaya Shema'u ta dubesu "Kai gaskiya bazan iya koran maku shiba, maza ku je ku kira Yaya Bilkisu ita ce kawai mai iya koran karen nan...”
Ba su bari ta kammala maganar ba da gudu suka nufi wani ɗan aji madaidaici suna kiran sunan Yaya Bilkisu.
Wata matashiyar budurwa ta ɗago ta kallesu "Lafiya kuke ta kirana haka ku kuma?’
"Kare ne ya hanamu zama kasan bishiyar kanya, shi ne Yaya Shema'u ta ce mu zo mugaya maki.”
Dan tsaki ta ja sannan ta yi gaba, su ka mara mata baya su duka yaran .
Tun daga nesa ta hango katon bakin karen, sai zazzalo halshensa waje yake tamkar wanda ke jin kishirwa ko rana ta dakesa ƙwarai .
Wani ƙaton dutsi ta ɗauka ta daidaici Karen ta jefeshi, da shi. Bazato dutsin ya sauka a kan tsakiyar fuskar karen, take wani baƙin jini ya dinga zubowa yana ɗiga ƙasa, ganin Karen ya yi tsaye yaƙi gudu daga inda yake saima kallonta da yake tamkar wani mutum jini sai malala yake yi, yasanya ta sunkuyawa ta ƙara ɗaukar wani dutsin ta sake jifarsa karo na biyu.
Wanan karonma ta samesa a gefen idonsa, har wani kuka yayi mai kama da gurnani sannan ya ruga ya nufi bayan azuzuwansu.
Yara suka saka ihu suna murna an kori-kare-an-kori-kare, suna cikin murnai aka kaɗa ƙaraurawar komawa aji dole kowanne ɗalibi ya koma ajinsu.
Tun daga ranar babu wani kare da ya sa ke zuwa gun wannan bishiyar kanyar.
_TSAKIYAR DARE_
Kowane Ɗan'Adam ya kwanta domin samun hutu ga rayuwarsa cikin kwanciyar hankali yana barcinsa, a dai-dai wannan lokacin Bilkisu ke zaune gaban darduma tana rera karatun Al- Qur'ani mai girma, cikin madaidaiciyar muryarta mai daɗin sauraro ga mai saurara.
Daga can kofar ɗakinsu Bilkisu wani bakin guntun abune keta mulmula yana birgima yana ƙara dunƙulewa waje guda, tamkar wani kullin magani. A hankali wani danƙwalelen ido ƙwaya ɗaya tal ya bayyana a tsakiyar dunkulin abun nan, sannu a hankali idon yayita tsawo yana kara girma ya nufi hanyar kofar ɗakinsu Bilkisu ,
sai dai idon kawai ke tafiyar jikin abun yana a inda yake tun a farko bai matsaba ya na jujjuyawa tamkar majau-jawa .
Ko da idon ya isa kofar ɗakin sai naga yadawo da matsanancin gudu, tamkar haske haka ya dawo ya shige jikin ainihin gangar jikinsa .
Yafi minti biyar bai sake fitowaba sai dai wannan karon gani na yi ya mike tsaye, yanata tsawo tamkar ana jansa da igiya kamar yanda ake jan robar wando duk inda ake so.
Iyakar hangen mai hange babu yanda mutum zai hango ƙarshen tsawon abun, sannan wasu kabta-kabtan yatsu suka bayyana masu wani kalan gashi lullube da jikin hannun, tamkar gashin mage ko akuyar dawa, kwanon dakin Bilkisu hannuwan suka sauka da nufin yayesa , sai dai ko ida sauka hannun baiba wata jar wuta tai fitar burgu ta baibaye hannun.
Tamkar kwallo haka Halittar tayi sama ta fado kasa tim.
Duk abun da ke faruwa ba wanda Bilkisu ta san ana yi, a kofar ɗakinsu hankalinta gaba ɗaya ya raja'a kan karatun da takeyi cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Sai da aka fara kiraye-kirayen sallar asuba sannan Bilkisu ta rufe Qur'anin ta nufi hanyar fita tsakar gida dan sake sabuwar alwalla .
Sai lokacin wannan halittar ta samu da ƙyar ta cunkushe wuri guda ta bace bat.
Kasancewar yau asabar babu makarantar boko sai islamiyya, ya sanya kowane ɗalibi yake sauri ya shirya in dai yana zuwa islamiyya ya tafi kar a taresa ayi masa bulalar makara .
Bilkisu nata sauri ta shirya ta tafi kar a tare ta dan tana da tsoron bulala sosai, musamman ta Mal. Aminu (Dan bahago) bulalarsa akwai zafi sosai.
Dai-dai matoya ta hango wata kawarta mai suna Nauwara suka tsaya suka gaisa Nauwara taita janta da surutu wai yau Ita baza ta islamiyarba sai gobe, Bilkisu ba ta ankaraba ta ga lokaci ya ja sosai cikin firgici ta wuce Nauwara da hanzari ta nufi Islamiyar .
Tun daga nesa ta hango Mal. Aminu ( Dan_bahago) rike da bulala yana zane 'yan makara, cikin sanyin jiki ta isa gun amma ko kallonta baiba ya zane sauran ya sakata kallon rana ya dora mata duwatsu a hannuwanta har ta galabaita iyakar galabaita amma ko yaji tausanta, ƙarshe yayi mata bulalai da sai da sauran Malamai suka rugo dan jin laifin da tayi masa haka .
Baiwar Allah Bilkisu tasha duka duk ta fita hayyacinta sai ajiyar zuciya take yi kawai, kafin a tashi zazzabi ya rufeta tamkar garwashi haka jikinta ya dauki zafi da kyar ta isa gida ta kwanta .
_TSAKAR DAREN RANAR_
Yau ba halin karatun Qur'anin da Bilkisu ta sabayi ta kanta take yi kwata-kwata jin jikinta take yi tamkar ba nataba, ta kasa daina jin azabar dukan da Mal. Aminu ya yi mata a jikinta, ga wani abu guda da ya tsaya mata arai shine ganin sanda Mal. Aminu na dukanta idanuwansa sun koma baƙi babu alamar fari ko kaɗan a cikinsu tamkar ba mutum ba.
Alamar tafiya taji tamkar ana yi a kofar ɗakinsu, cikin alamar tsoro ta kasa kunnenta dan ta ji gaskiyar abun da kunnuwanta ke jiyo mata gaskiya ne kuwa?
Ɗas-ɗas taji ana tafiya can kuma taji ana ƙwas-ƙwas, idanuwa waje ta ce "Mi ke faruwa ne waje ni Bilkisu?"
Cikin tsoron ta lallaba dan ta je taga abun da ke tafiyar a tsakar gidan nasu.
Shin me yake bibiyar Bilkisu ne haka?
Wacece Bilkisun ma?
Duk sai kun biyoni a shafi na gaba don jin yadda za ta kaya.
managarciya