Ka sani cewa wa'adin ka a matsayin Sufeto-Janar na Ƴansanda ya ƙare, MURIC ta gargaɗi Egbetokun

Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmai ta Ƙasa (MURIC) ta yi gargaɗi kan yiwuwar ƙarin wa’adin aiki ga Sufeto Janar na Ƴansanda, Kayode Egbetokun.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin, Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana cewa ƙarin wa’adin zai iya rage ingancin aiki, haifar da rashin jituwa, da kuma rage ƙarfin gwiwar jama’a ga rundunar ƴansanda.
A cewarsa, gyaran dokar ƴansanda da ya ba da damar ƙarin wa’adin Egbetokun abin damuwa ne.
Sabuwar dokar, sashi na 18(8), ta ba da dama ga Sufeto Janar na ‘Yansanda ya ci gaba da riƙe muƙaminsa har zuwa ƙarshen wa’adin da aka tanada a takardar nadinsa, maimakon yin ritaya a shekara 60.
Akintola ya jaddada cewa rundunar ‘yansanda ta samu ci gaba sosai a ‘yan kwanakin nan, inda aka ceto daruruwan mutanen da aka sace tare da warware manyan laifuka da dama.
Sai dai ya nuna damuwa cewa ƙarin wa’adin na iya hana wannan ci gaba da haifar da rabuwar kai a cikin rundunar.