Gwamnan kebbi ya raba wa manyan sarakunan jihar motocin alfarma

Gwamnan kebbi ya raba wa manyan sarakunan jihar motocin alfarma
Gwamnan kebbi ya raba wa manyan sarakunan jihar motocin alfarma
 
Gwamnan jihar Kebbi Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya kaddamar da raba wa manyan sarakunan gargajiya na jihar  manya-manyan jifa-jiffai domin gudanar da ayyukan yau da kullum.
 
Sarakunan da suka amfana da motocin sun hada da Sarkin Gwandu da Sarkin Argungu da Sarkin Zuru da Sarkin Yauri.
 
Gwamnan kebbi ya ce ya dauki wannan matakin ne na raba wa sarakunan motocin saboda rawar da suke takawa wajen samar da tsaro a fadin jihar.
 
 Abbakar Aleeyu Anache