KAEDCO: Ana Fama da Matsin Rayuwa, an Kori Ma'aikata Kusan 1,000 a Kaduna

KAEDCO: Ana Fama da Matsin Rayuwa, an Kori Ma'aikata Kusan 1,000 a Kaduna
 
Al'ummar jihar Kaduna sun shiga duhu bayan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na jihar (KAEDCO) ya kori ma’aikata 900. 
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin ya fara raba takardun sallamar aiki tun ranar Asabar har zuwa Lahadin da ta gabata. 
The Nation ta ce a ranar Litinin, ƴan ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) suka fara yajin aikin sai baba ta gani don nuna adawa da korar. 
Sun kuma fita zanga-zanga a hedikwatar kamfanin da ke kan titin Ahmadu Bello, Kaduna, suna rera wakokin adawa da matakin korar ma'aikata. 
Fustattun ma’aikatan sun ɗaga alluna masu rubuce-rubuce daban-daban, sun kuma toshe kofar shiga hedikwatar kamfanin, suka hana ma’aikata da abokan hulɗa shiga. 
Ƙungiyar NUEE reshen Kaduna ta zargi shugabannin kamfanin KAEDCO da rashin adalci da kuma take duk wata yarjejeniya da aka cimma. 
Shugaban NUEE na jihar Kaduna, Kwamared Sheyin Nuhu Wakili, ya shaida wa manema labarai cewa: “Yayin da muke kokarin warware matsalolin da ake fuskanta,ɓshugabannin KAEDCO sun kori manyan ma’aikata 10 ba tare da bin ka’idojin aikin kamfanin ba. 
"Duk da shiga tsakani da yarjejeniyoyin da aka cimma a tarurruka da suka gabata, haka kamfanin ya yi fatali da komai, ya ƙi aiwatar da su yadda ya kamata. 
"Abin mamaki, mun samu labarin cewa shugabannin sun fara sallamar ma'aikata sama da ma’aikata 900." 
Rahotanni sun nuna cewa kusan kowane yanki a jihar Kaduna ya fada cikin duhu sakamakon wannan yajin aiki na ma'aikatan wutar lantarki. 
Sai dai shugabancin kamfanin ya musanta cewa adadin ma’aikatan da abin ya shafa ya kai 900 kamar yadda NUEE ta bayyana. 
Shugaban sashen hulda da jama’a na KAEDCO, Abdulazeez Abdullahi, ya shaida wa jaridar Punch cewa za a warware matsalar gaɓa ɗaya ranar Talata. 
A cewarsa: “Za a warware komai gobe. Amma adadin ma’aikatan da korar ta shafa bai kai 900 ba kamar yadda suke ikirari."
A wani labarin, kun ji cewa Kamfanin Wutar Lantarki watu TCN ya bayyana cewa an lalata turakun wutar lantarki akalla guda 18 wanda ya jawo rashin wuta a ƙasa. 
TCC ya ce wannan lamari na lalata kayan wuta na daga cikin babbar barazanar da kamfanin ke fuskanta a ƙoƙarin wadata ƴan Najeriya da wutar da lantarki.