'Yan Bindiga Sun Fara Hijira Zuwa Ɓangarorin Jihar Neja

'Yan Bindiga Sun Fara Hijira Zuwa Ɓangarorin Jihar Neja
Daga Awwal Umar Kontagora.
Sakamakon hare-haren jami'an tsaro a yankunan jahohin Katsina da Zamfara ta sama, an fara ganin yan bindigar suna kwararowa wasu yankunan kananan hukumomin jihar Neja da ke iyaka da jahohin da jami'an tsaron ke kaiwa hari ta sama.
Rahotanni sun tabbatar da cewar ko a cikin makon jiya maharan sun kai hari garin Dusai da ke karamar hukumar Mariga inda bayan kashewa sun kuma yi garkuwa da mutane da dama inda suka yi awon gaba da sarkin mahoron Dusai.
Rahotanni sun bayyana cewar maharan sun kashe mutane biyu a wannan harin inda suka harbi mutum daya da ke jinya a halin yanzu. Bayan awon gaba da mutane da dama, wani da ya samu kubutowa a hannun maharan ya bayyana cewar maharan sun kashe sarkin mahoron Dusai tare da daure mutum daya inda suka jefa shi ruwa wanda zuwa yanzu ba a tabbacin hakikanin halin da ya ke ciki.
Maharan dai an bada rahoton ganin su kwamba a yankin karamar hukumar Rafi inda suka yi tsunke da ake kyautata zaton sun bangaren Kukoki zuwa yankin karamar hukumar Shiroro.
Wani da ya nemi a sakaya sunan shi da ya samu zantawa da wakilin mu daga karamar hukumar Rafi, yace lallai an sanar da jama'ar karamar hukumar mu da mu kiyayi yin nisa da gari musamman manoman da ke da gonaki nesa da gari, domin mun sha azabar wadannan batagarin.
Tau, muna tsammanin hare-haren sama na ba kakkyautawa da jami'an tsaro ke yi ne ya tsoratar da su barin sansanonin su, inda aka hanyar tsira da rai duk garin da suka cin ma a hanya suke tarwatsa al'ummar wurin.
Yanzu haka dai muna da yan gudun hijira da dama a sansanin yan gudun hijira da ke cikin garin Kagara fadar sakatariyar karamar hukumar Rafi, da kuma wadanda ke zaune a gidajen yan uwa da kuma wadanda ke cikin kangaye.
Mu dai muna kara kira ga gwamnati da tayi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan yan kasa da dukiyoyin su, mun san jami'an tsaro na bakin kokarinsu domin su ma a wannan aikin da daman su sun rasa rayukan su.