‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 65 A Kasuwar Goronyo
Ya ce Kasuwar tana da kofofi 7 ta duk in da mutum ya bi zai samu mutanen sun a harbi a haka suka ta yi ta harbin mutane a har zuwa Tara na dare suka shiga asibiti suka harbi wasu mutane suka bi ta garin Kumaji suka bar garin na goronyo. Ya cigaba da cewa mutanen ba su san yawansu ba suna dauke da bindigogi miyagu domin shi ma kansa ya rika kallonsu ne a wani wuri da ya labe, an kashe mutane da yawa an jikata wasu da dama, "a lissafin da muke da shi mutanen da aka kashe sun fi 65 a gabana mun lissafa gawa ta kai 65 cikin ba mu sanya mutanen Bodinga da Shinaka da wasu dake cikin garin goronyo da sauran wasu dake zuwa cin kasuwar garin.
‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 65 a babbar Kasuwar Goronyo a karamar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato.
"Mahara sun shigo a kasuwar ne a jiya Lahadi ana kusa da tashi a kasuwa Magrib ta matsa kusa, an rika ganin wasu da kayan mata suna zagaya Kasuwar a lokacin da suka isa wurin masu sayar da Dusa a lokacin suka fara harbi ta ko'ina, anan take 'yan uwansu suka shigo kasuwar ta kowace kofa a kasuwar suka rika harbi kan mai uwa da wabi a jiyan da dare kai tsaye an dauki gawa tafi 40", a cewar majiyar da aka yi a gabanta.
Ya ce Kasuwar tana da kofofi 7 ta duk in da mutum ya bi zai samu mutanen sun a harbi a haka suka ta yi ta harbin mutane a har zuwa Tara na dare suka shiga asibiti suka harbi wasu mutane suka bi ta garin Kumaji suka bar garin na goronyo.
Ya cigaba da cewa mutanen ba su san yawansu ba suna dauke da bindigogi miyagu domin shi ma kansa ya rika kallonsu ne a wani wuri da ya labe, an kashe mutane da yawa an jikata wasu da dama, "a lissafin da muke da shi mutanen da aka kashe sun fi 65 a gabana mun lissafa gawa ta kai 65 cikin ba mu sanya mutanen Bodinga da Shinaka da wasu dake cikin garin goronyo da sauran wasu dake zuwa cin kasuwar garin.
"a jiya da lamarin ya faru kasuwar ta cika sosai ganin wasu kananan kasuwanni sun daina ci kan matsalar tsaro sai ga wadan nan bata garin sun zo," a cewarsa.
Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa mutum 30 ne suka rasa rayuwarsu.
Tambuwal ya bayyana hakan a lokacin da shugaban Hafsan sojojin Nijeriya Janar Faruk Yahaya ya kai masa ziyara a litinin.
Har zuwa hada wannan rahoto ana kan fitar da gawa a asibiti da kasuwar domin da yawan wasu da suka jikkata da aka harba a kai da kirji suna rasuwa, hakan ya sa yawan kididdigar ke karuwa cikin kowane lokaci.
managarciya