Sakkwato Na Cikin Jijohi 18 Dake  Kan Gaba Wajen Samar da Kuɗin Shiga Na Cikin Gida

Sakkwato Na Cikin Jijohi 18 Dake  Kan Gaba Wajen Samar da Kuɗin Shiga Na Cikin Gida

 

Wani bayani daya fita daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa, ya nuna yadda jihohin Najeriya 36 ke samarwa kansu kuɗaɗen shiga na cikin gida. 

Rahoton ya nuna yadda kuɗin shigar jihohi ya tashi daga biliyan N682.67 zuwa tiriliyan N1.76 a shekaru 6 da suka gabata watau daga (2015 zuwa 2021). 
Duba na tsanaki ya nuna yadda yadda alƙaluman suka bambanta tsakanin jihohin.
Kuɗin shiga na cikin gida dai, shi ne kuɗaɗe da jihohi ke samarwa kansu domin gudanar da ayyukan cigaban raya ƙasa ba tare da an haɗa su da kuɗin da suke amsa daga gwamnatin tarayya ba. 
Kuɗin shiga na cikin gida na da matukar muhimmanci saboda dashi ake amfani wajen yin alƙalancin yadda gwamna ya jagoranci jihar sa tare da ganin yadda kowacce jiha ta dogara da kanta. 
Bugu da ƙari, jihohi dake da kuɗaɗen shiga na cikin gida mai yawa, ana kallon su da tattalin arziki mai kyau, wanda hakan ke janyo masu saka hannun jari. Jihohi na samun kuɗaɗen shigar su na cikin gida ne yawanci daga, kuɗaɗen rasiti da ake biya, haraji, jangali, tare da sauran su. 
Daga 2015 zuwa 2021, jumullar abinda jihohi 36 suka samu ya fara daga 158.37 cikin ɗari ko kuma tiriliyan 1.8 Naira.
Binciken da jaridar Legit.ng ta gabatar ya nuna cewa, a cikin jihohi 36, guda 18 ne suka samu nasarar wuce adadi mafi kanƙanta na ƙasa akan batun kuɗaɗen shiga na cikin gida.
Jihohin da Suka fi Samun Haɓakar Kuɗaɗen shiga na cikin gida: 
Zamfara (592.39%) 
Lagos (431.41%) 
Borno: (431.23%) 
Nasarawa (382.07%) 
Kaduna (358.31%) 
Ekiti (313.60%) 
Sokoto (281.09%) 
Yobe (275.16%) 
Kwara (276.20%) 
Kogi (245.94%) 
Plateau (209.45%) 
Jigawa (224.13%) 
Oyo (232.22%) 
Bauchi (232.25%)