HAƊIN ALLAH:Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 24
HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
*AUNTY FAUZAH YAR AMANAH AVAILABLE*
*_Oh ni kawata kullum shiga kike ta Alfarma da kace raini haka wai duk Ina kike samun wanan kayan ne haka ko kema kinasa Order kamar yanda Naga hajiya bilki tasa? kawata O me order fa kikace ni rabani da kayan takaici da wahala hajiya bilki bagashin Nan ba an barta a wahala ba kudin mutane ba Kaya wanan shine ba uwa ba riba ai ni a waje Daya nake siyayyar kayana Kuma ta online, kawata kikace ta online fa? Online din da akace yawancin duk Yan danfarane mace Sai tai tallah Kaya Babu su ta anshe ma mutane kudin su Babu amo Babu labari, yawa gwanda da kikace yawanci bakice duka ba Kinga wanan shigar ta Alfarma danakeyi wajan sa Kaya masu kyau a jikina da kayan dakina da na kicin da suturuna duk a online nake siyan su wajan Yar Amanar mu lak'abin sunan ta yayi dai dai da ita tana kasuwanci Babu cuta Babu cutarwa kayanta yanzun duk Available ne kinsan tana Lagos da zama shiyasa zakiga Kaya Yan gaske a jikina ba irin shaku shaku ba Sai na gama yayi Kaya sanan nake ganin shi aduwawon wasu Kayanta daret daga Lagos tana da group din Yan sari da Kuma group din Yan siyan dai-dai wanan Yan kunne da sarka da zoben da abin hannu danabaki set duk a wajanta na Sara kinsan yanzun ba'a zama in kika zauna zakiga zaunau tana da wani group LAGOS ORDER in kinyi payment 10 days kayan ki sun zau insha Allah saboda kanta take shiga kasuwa Kuma abin da zai baki sha'awa shine kinsan munasan siyaya Aman kudin mota ke hanamu Sai muga ribar kamar duk zata tafi a kudin kawo Kaya toh ita Yan gari Daya kamar mu Nan da muke Kano zata hada kayanmu waje Daya Aman kowa fa nashi daban sunan shi a jikin kayan shi zata turo wajan sister ta Sai ta fadan Mana kudin mota Sai kiga kudin Bai taka Kara sun karya ba sanan naji ta taba magana a group Yan kaduna ma awajan sister dinta suke amsa kamar yanda muke Amsa, sauran garuruwan Kuma Suma akwai inda suke amsan nasu Kai kawata wai dame dame Yar Amanah Nan taki take Sai da wane? Kai Kai Kai kawata abin da yawa wai mutuwa tashiga kasuwa a abubuwan amfani na gida komai tana Sai dawa sanan wajan kifitoh kamar dawusu wajan ado nanma ba'a barta a baya ba abin na Yar Amanar mu Sai dai muce Alhamdulillah Masha Allah toh kawata ko Zaki bani number tane ? Kai kawata kinsa Nima Ina daukar Kaya a wajanta in tallah ta ko dai in saki group dinane ki dinga siyayar a wajena, Kai kawata Nima tallah Zan dingayi in nagani a wajanta kinsan kowa Yana San sauki toh badamuwa ga number Tata 09073738449 a wanan number Zaki mata magana zata saki group Aman kice na Yan sari tunda Sara kema Zaki dingayi don in ba sari zakiba a normal group zata saki ko kinshiga na sari mutukar ba sarin zakiba zata cireki, balle ma sarin zanyi kawata wai tana Sai da Lagos less ne? Tab ai babuce kawai Bata siyarwa Kinga Lagos less kayan Yara takalma Yan kunne set dinsu agoguna jakunkuna ke abubuwan fa da yawa aman Bari in baki link dinta na normal group zakiga abubuwan hajiyata Sai kin rasa nasiya fa don Allah Bari kiga_*
https://chat.whatsapp.com/HJ6k82WxPpk8BQdNYENGkb *_yawa kibi wanan link din zai kai ki group din YAR AMANAH AVAILABLE shine zakiga abubuwan da nake fadan Miki Ina fatan zakiji Dadi siyaya wajan AUNTY FAUZAH YAR AMANAR MU ita tana maraba da Yan sari da siyan dai dai toh kawata nagode sosai Allah yabar zumunci, Kai kawata Sai kace wace ta baki kudi au baki saniba da'a baka kudin da bazasu isheka sarafawa ba ai gwanda a nunamaka hanyoyin samin kudin Kinga Ni dai zaman banza in kashe lokacina a online batare da ko ficika ta shigomin ba Sai a sarar data Kinga ai yanzun Zan samu motsi yafi labewa ko ai kuwa kawata Allah yasa Mana Albarka a Neman mu Ameen kawata_*
```Aunty fauzah tana maraba daku Sai kun zo
Page 24
Ya rasa ya zai da rayuwarsa, shike nan ace mutum ya yi aure don ya huta amma sam bai samu hutun ba? Gaskiyar magana yana shan wahalar rayuwar aure shi kam, yaushe zai daina irin wannan baƙin cikin na wannan rayuwar? Bai san rayuwar farin ciki ba, yana baƙin ƙoƙarin sa kan rayuwar gidansa amma a banza, ya sha zama ɗaki ya sha kukansa kan baƙin cikin da yake fuskanta na rayuwarsa. A hankali ya fara tunano rayuwarsa ta baya kafin ya yi aure, lokacin yana cike da ji da kansa yana cikin ƙwalisa da bushashar rayuwa.
Kasancewar tun da ya kammala karatunsa yake sha'awar kasuwanci, don haka ya nufi mahaifinsa da zancen neman shawarar wace sana'a ya kamata ya fara yi, domin sam aikin gwamnati bai birgeshi saboda a ganinsa aikin gwamnati ba wani aikin da zai tsare maka dukkan buƙatunka bane na Yau da kullum ba. Sai dai Baban ya dube shi yana murmushi irin na ta Yaro kyau take ba ƙarko, ya dube shi ya ce, "Mustapha ka sani indai zaka ɗauki shawarata to ina son ka fara neman aikin gwamnati sannan sai ka cigaba da sana'ar, saboda ba a zama a ɓangare guda a wannan lokacin, dole ne kai taɓa kiɗi taba karatu, saboda rayuwar yanzu kowa kansa ya sani, kuma sai kana da shi ake yi da kai. Don haka ka fara neman aiki sannan sai ka ɗora kasuwancin." Sosai ya gamsu da maganar Babansa don haka kai tsaye ya nufi gidan Yayan Babansa don ganawa da Salim abokinsa (Uncle Salim) kasancewar tare su kai karatu tare su ke komai na rayuwarsu, tasu ta zo ɗaya sosai.
Yana zuwa ya iske Hajjo zaune tana ta faɗa wai Salim ya yi mata alƙawarin nama don shegantaka sai ya kawo mata goro madadin naman, wai ai shi ne naman tsaffi irin ta. Har suka gaisa Hajjo bata daina faɗan ba don haka ya tashi tun kafin ta juyo kansa ya nufi ɗakinsu Salim ɗin. Yana zaune yana kallo kamar baisan abin da ke faruwa ba. Duka ya kai ma shi, "Amma fa baka ji wallahi kana ji fa Hajjo nata faɗa, kuma kaine ka tsokane ta, wai ina naman yake nasan dai ka siyo tunda ka ambata." Salim ya yi dariya ya jawo ledar naman dake kusa da shi ya ce, "Ka ganshi nan, bari nayi ya huce sai na kai mata, ai ta kwana biyu ba tai faɗa ba shi ne Yau naga ya kamata ta wasa muryarta ta ƙara zaƙi."
Su kai dariya su duka, Mustapha ya dubi Salim ya ce, "Daga gun Baba nake, shi ma dai kamar yadda kace haka ya ce, na haɗa kasuwanci da aikin gwamnatin duk nayi, don haka ga takarduna ka haɗa duka ka ba Baba na nan gidan kamar yadda kace da farko, idan ya so daga baya sai mu fara kasuwancin."
Amsar takardun ya yi ya aje, suka fita tare ɗauke da ledar naman Hajjo, suna dariyar abin da zata ce yanzu kuma.
Goron na hannunta ta gutsura take cewa, "Yaro ya maida Ni abiyar wasansa, ina ya taɓa ganin goro ya fi nama ne?" Salim ya aje mata ledar naman ya ce, "Musty ina ka taɓa ganin inda tsohuwa ke ƙaunar nama fiye da goro don Allah?" Ita dai ta ɗauki ledar namanta tana cewa "Can ku ƙarata tunda ka kawo min."
Sati guda da bata takardunsu suka samu aikin, sai dai ba nan cikin garin Kano aka aje su ba, can wani ƙauye mai suna Rano aka kai su, basu ji daɗin hakan ba, musamman Mustapha da ya fi Salim son rayuwar birni da wayewa, a ganinsa zaman ƙauye na iya maida mutum ɗan ƙauye shima, sannan me ye a ƙauye wanda zai ƙara wayar da kan mutum ma wai? Hakan yasa ba wani karsashin aikin da yake sai dai kawai idan an taya shi murna ya amsa ba don yana murnar ba.
Babansa sarai ya fahimci inda damuwar take, Musty akwai son gayu da gogewa hakan yasa bai murna da samun aiki a ƙauye ba, don haka ya kawo ido ya saka mai kawai.
Cikin ikon Allah suka dinga zuwa aiki a Rano suna dawowa weekend duk ƙarshen mako gida, tun Mustapha na ƙorafi har ya gaji ya daina ƙorafin zuwan sa ƙauye aiki.
Watarana yana zaune ƙofar gidansu yana latsa wayarsa sai yaga wata yarinya ta fito daga layin dake bayan gidansu, har ta wuce yana bin ta da kallo, bai dai ce komaiba har a ranshi, kawai dai yasan ya tsare yarinyar da kallo ne amma bai san dalilin kallon da yake mata ba sam. Wasa-wasa sai ya kasance duk weekend idan ya dawo gida yana zama dai-dai lokacin da ya tabbatar da yarinyar na wucewa, wadda har zuwa yanzu bai san sunanta ba, haka bai san daga wane gida take ɓullo wa ba. Yau dai sai ya saka a ranshi zai gwada yi mata magana saboda ya fahimci son yarinyar yake. Lokacin da zata wuce kau ya tashi ya bita a hankali yana yi mata sallama.
Cikin natsuwa ta waigo ta kalle shi sai kuma ta cigaba da tafiyarta bayan ta amsa sallamar da ya yi mata.
"Amm, idan ba damuwa ina son yin magana dake Please."
Kamar bata ji shi ba, haka ta nuna domin tafiyarta kawai take ba alamar zata tsaya balle ta saurare shi, don haka sai ya yanke shawarar ya koma kawai sai ya nemi inda gidansu yake ya iske ta.
Har zai juya sai ya ga ta tsaya fuska ba walwala tana kallonsa.
"Ga dukkan alama idan ba shi ne ya yi magana ba tabbas bata da alamar yin magana ita, don haka ya dube ta yana murmushi ya ce, "Don Allah ki yi haƙuri na tsaida ki ko? Ina son yin magana da ke ne mai amfani don haka na biyo ki domin ki ban umarnin zuwa gidanku ta hanyar yi min kwatance idan na dace."
Kamar dai bata magana yanzu ma amma sai ya samu kunnuwansa da jin muryarta mai daɗin gaske tana cewa, "Lafiya kake neman na baka kwatancen gidanmu?" Tabbas ya ji daɗin muryarta don haka bai ƙasa a gwiwa ba ya ce mata, " Babban laifi ma kuwa ki kai wanda ba inda ya kamata ai maki hukunci sai gaban iyayenmu."
Walau ta ɗan watso mai manyan idanunta masu haske, alamar tsoro da mamaki sai kuma ta basar bata ce komai ba. Hakan yasa yasan cewa zai aiki kafin ya samu abin da yake so.
Cikin alamar zolaya ya ce mata, "Kar dai ace kin razana bayan kin san kin aikata abin da nace?"
Dariya ta ɗan yi mai alamar murmushi tace, "Uhmm! Akan me zan razana tunda ban sanka ba, baka ban aikata maka komai ba?"
Murmushin shima ya yi, ya ce, "To yanzu dai kar da na tsaida ki, zan so ki ban damar mallakar sunanki, da arziƙin sanin inda gidanku yake don Allah."
Tai murmushi karo na barkatai domin ƙamshin turarensa na tafiya da imaninta yadda ya kamata, ashe shi ne ke wannan ƙamshin turaren duk lokacin da zata wuce tana jinsa, bata taɓa tunanin daga gunsa yake ba ai sai yanzu. Cikin sakin fuskar da bata san tana da ita ba tace, "Sunana Maryam kuma gidanmu na bayan layin nan, ban san kuma me kake so ba, bayan hakan." Ta faɗa tana kallonsa idanunta cike da haske.
"Gaskiya godiya zan jibga maki na bani wannan gagarumin abubuwa masu daraja a guna." Daga hakan ya dube ta yana jin nishaɗi fal a ransa ya ce, "Mu je na raka ki ko kin yafe min rakiyar? Amma fa ki sani idan kin yafe min rakiyar nan tabbas zuciyata zata yini cikin hukunta ni, saboda ban bata damar raka wadda take da dogon burin bayyanawa abubuwa masu yawa a gareta ba."
Batai mai musu ba, don haka suka jera suna tafiya yana bata labari mai kama da labarin soyayya.
Bayan wani lokaci soyayya mai girman gaske ta bayyana tsakanin Mustapha da Maryam, wanda nan da nan iyaye suka shiga cikin maganar ba tare da ɓata lokaci ba aka saka wata shida na aurensu.
Sosai yake nuna mata soyayya duk da ita ma ba laifi tana nuna mai so iyakar iyawarta, sai dai shi a nashi hangen ba irin wannan son yake so ba, yafi son soyayya irinta wayewa wadda zata dubi idonsa ta zayyana mai yadda take jinsa a ranta da zuciyarta, ta dinga nuna mai yadda take jin kewa idan yana gun aikinsa, ta dinga tura mai saƙon soyayya akai-akai ta waya. Amma ya lura ita hakan ba shi ne gabanta ba, kawai dai tana son shi don haka ba sai kuma ta ƙara da wani abu ba bayan son da take mai ai tunda tace zata aure shi to a ganinta magana ta ƙare ta gama mai komai.
A ganinsa idan akai auren zata daina, zata zama yadda yake sonta zata dinga yi mai abin da yake buƙata, don haka sai ya tattara damuwar komai na rashin nuna mai soyayya da take ya watsar gefe ya dage da shirin aurensa, yasa a ransa idan ta je gidansa zai koya mata zata zama yadda yake so, ba mamaki ma ta iya soyayyar yanzu tana jin kunya ne da nauyin ba ai masu aure ba, don haka bata iya furta mai ko da kalmar ina ƙaunarka ne a gabansa, sai dai wani lokacin a wasiƙa takan ce mai "I love U."
Duk abin da aka tsaida rana to tabbas za a wayi gari ranar ta zo, don haka Yau kowa ya shaida ɗaurin auren Mustapha Kabir da amaryarsa Zainab Usman, kan sadaki lakadan ba ajalan ba.
Tun a satin farko ya fuskanci Maryam bata da matsalar komai wajen girki ba laifi ta iya girki, sai dai har zuwa yanzu ya rasa yadda zai ta daina nuƙu-nuƙu a gabansa, sam bata iya ko cire kaya a gabansa, ya ɗauka don ciniki bai faɗa bane don haka a ranar da tai saki guda cif da zuwa gidan ya lallaɓa ya amshi haƙƙinsa gunta, ta sha wahala sosai saboda shi ne karon farko, hakan yasa ya ɗauke ta da kanshi ya nufi toilet don ya taimaka mata ta gyara jikinta, sai dai sam Maryam taƙi ko buɗe idonta ta ganshi saboda tsabar kunyar da take ji tashi, shi kam har ga Allah bai san wannan kunyar da take nuna mai, domin alama ce ta zata danne mai abubuwa da daman gaske, wanda ko shakka ba zai iya jurewa ba.
Da ƙyar ya samu ya taimaka mata tai wankan suka dawo ɗaki, kafin ya je ya yi nashi wankan har ta ɗauki kayanta ta saka ta shige cikin bargo tai kwanciyarta.
Babu abun da ke ma shi daɗi ko a tunaninsa irin ya ganshi kwance jikin matarsa suna kwance sun yi lamo yana wasa da gashin kanta yana lallaɓa ta har tai barci, sosai yake da wannan burin na ganin komai zai matarsa na manne a jikinsa tana zuba mai shagwaɓa yana ta lallashinta, sai ya ji ya halaka baki ɗaya.
Yana ta tunanin ne ya shirya ya fesa turare ya haye gadon ya yaye bargon ya fesa mata turaren don bai ji alamar ta fesa ba, yana gamawa ya shige cikin jikinta, ya juye ya koma kan katifar ya maida ta saman ƙirjinsa. Yana da niyyar cigaba da wasa da gashinta ne kawai ya ji ta zame daga jikinsa ta sauka ta koma gefe ta kwanta.
Murmushi ya yi don ya yi tunanin ko ɗan fushin nan ne na amare ta nuna mai. Don haka ya sake mirgina wa yasa hannu ya kamota ya jawo ta jikinsa yasa hannunsa duka biyun ya rungumeta yana raɗa mata kalmomin ban haƙuri a cikin kunnenta.
Sai dai da gaske Maryam take ba ta iya kwanciya a jikinsa don da gaske ta ture shi, ta koma wani wajen ta kwanta har da ture bargon ta lulluɓe da zanin gado.
Nan da nan damuwa ta ziyarci zuciyarsa baki ɗaya sai duk wani farin cikin da yake ji da karsashin da yake ji ya fice daga zuciyarsa sai tunanin yadda za ai ya yi rayuwar da Maryam ke so bayan shi ba ita ce rayuwar da yake mafarkin yi a gidansa ba.
Washegari ya rigata tashi, don haka sai da ya jira ta tashi ta yi masu breakfast, ko a nan ya so ƙwarai ta zuba masu a waje guda, sannan ya so ƙwarai ace yana bata a baki tana ba shi amma sai Maryam ta haɗe rai karma yaga wargi ya kawo mata raini.
Yana kallonta ta aje mai na shi ita kuma ta ɗauki nata ta nufi ɗaki, hakan yasa ya fahimci shima wannan tsarin ba zai yiyu a gidansa ba kenan na zama tare a ci abinci ana annashuwa da farin ciki tare da tsokanar juna. Bayan hakan yana cikin mafarkinsa na zaman aure.
Cikin wata guda abubuwa suka dinga faruwa marassa daɗi tsakaninsa da Maryam, sam bata san ya dawo daga gun aiki ba ta je ta tarbeshi ba, haka bata san idan gari ya waye ba ta gaida shi ba, haka bata da lokacin zama da shi su yi hira balle yasan damuwarta kawai idan tana son abu zata dinga kumbure-kumbure ne sai da kanshi ya fahimta ya tambaye ta damuwarta sannan zata ce ka za take so. Idan bai mata ba sam bata jin nauyin gaya mai maganar duk da ta zo bakinta haka zata yaɓa mai hankalinta kwance.
Bata damu ba idan ta ganshi a damuwa ba ta zauna gabansa ta tambaye shi damuwarsa ba.
Saboda ya samu natsuwa da kwanciyar hankali yasa ya nemi transfer daga gun aikinsa ya dawo Kano amma duk a banza sai ma ya ji ina ma ace bai dawo ba? Ina ma ace sai ƙarshen satin yake zuwa ya kwana biyu ya koma kamar yadda yake tun baya? Ace kana auren mace amma sam bata san ta dinga maka kissa da ɗan kisisina ba, babban damuwarsa bata taɓa nuna tana son ko da wasa ba ta nemi haƙƙinta ba na aure sai dai kawai idan ya neme ta zata amince amma ita kam tafi ƙarfin ta neme shi, hakan na ci mai tuwo a ƙwarya sosai.
Ganin har ta samu ciki bai samu damar karkato da hankalinta ba kan irin rayuwar da yake mafarkin yi da ita ba yasa ya gina ɗakinsa daban ya kwashe kayansa ya koma can da rayuwarsa domin cikin yasa baki ɗaya ta ida ƙazancewa ba ruwanta da shara ko wanke-wanke sai ta tara kayanta baki ɗaya sannan take zama ta wanke da ƙyar.
Ko da ya koma ɗakinsa daban shi kenan sai sharar nata ɗakin ya faskara balle ta je ta share nashi ɗakin, haka zai share abinsa bata jin komai, haka ko a jikinta.
Sai su jima bata je ko hanyar ɗakinsa ba, abinci ma idan ya dawo ya leƙa ya ganta ne zata tambaye shi ko zai ci abinci? Idan ya ce mata zai ci shi ne zata kai mai, idan ya ce ya ƙoshi shi ta shafa ba ruwanta.
Ganin ya kasa samun abin da yake so ne yasa ya fara neman wata yarinya ya aura, mai suna Hafsat, sosai yake da burin yarinyar ta kasance cikar burinsa saboda har ga Allah bai da burin tara mata a gidansa yafi son ya yi rayuwa irinta hutu da jin daɗi yasan kuwa tara mata ba zai ba shi damar hakan ba,amma ya zai yi, dole ya ƙara aure indai yana son kwanciyar hankalinsa na zaman auren daya tsara a rayuwarsa.
Hafsat yarinya ce wayayya wadda ta gama karatunta, tana da kyau daidai nata, sannan tafi Maryam surutu nesa ba kusa ba, hakan yasa yake tsammanin zata cike ma shi gurbin da Maryam ta kasa cike mai na rayuwar aure.
Lokacin da labarin aurensa ya isa gunnen Maryam ba irin haukan da batai mai ba, amma ya nuna mata ko a jikinsa kawai hidimar aurensa yake bai tsaya bi ta kan haukanta ba, nan da nan ya tsira ɗakin amarya cike da farin cikin cikar burinsa na samun wadda zai dinga farin ciki da rayuwar jin daɗi da ita watau Hafsat.
Cikin ikon Allah akai auren wanda ba irin tashin hankalin da Maryam ba tai ba, har barazanar zubar da cikin dake jikinta tayi amma ya yi mata ko'in kula, da taga ba Sarki sai Allah ta shafa ma kanta lafiya.
Amarya Hafsat ba laifi tana da wayewa amma sai dai sam bata da kunya abu kaɗan tana iya danƙara mai zagi, bata jin shakkar gaya mai kowace irin magana, idan ya tanka mata nan take zata kwashe kayanta ta nufi gidansu tayi yaji sai ya bita.
Ga shi Allah Ya ɗora mai masifar son Hafsat, duk yadda take ci mai mutunci take gara shi hakan bai hana shi sonta.
Ga shi Maryam ta haihu amma sun kasa zaman lafiya koda yaushe suna cikin masifa da faɗa da juna, abin takaicin kuma kowace laifinsa take gani domin gani take yana bayan waccan ne bai bayanta.
Baki ɗaya komai ya yi mai tsaye ko da yaushe cikin tashin hankali yake a gidansa, abin da ya kai su da ba mai ganin kowa da mutunci a tsakaninsu.
Ban basu daraja shi kowacce kanta kawai ta sani, basu damu da yadda yake faɗi tashi kansu ba, ko da yaushe cikin damuwa yake baki ɗaya gurinsa ba wanda ya ci ka na rayuwar aure kullum sai an zo rabon faɗa gidansa, ko kuma ko da yaushe iyaye na gidan yin sasanci.
A haka dai itama Hafsat ta samu nata cikin wanda ba abin da ya ragu na fitinar da ake cikin gidan sai ma abin da ya yi gaba.
Ko da yaushe cikin zullumi da tunanin yadda zai da rayuwar gidansa yake abin da yasa abokansa da dama ba shi shawarar ya ƙara aure ya aje matar gidanta daban ya barsu can sui ta abun da suka saba shi kuma ya nema ma kansa wadda zata kula da shi.
Ganin kamar hakan mai ɓullewa ne yasa wani abokinsa nema ma shi yarinyar makwabtansu mai suna Badiyya cikin lokaci kaɗan akai komai sai dai matsalar da aka samu ashe Badiyya bata son shi kawai ta aure shi ne don cikar wani burinta.
Lokacin da ta fahimci burin ba zai cika ba sai kawai ta fito da munanan halaye masu ciwo ita ma ta dasa daga inda su Maryam suka tsaya.
Badiyya bata damu ba don ta kwashi ɗanyen abinci ta kai gidansu ko ta saida ta kashe kuɗin, sam bata da tausayi ita kawai burinta a bata kuɗi ne ai mata hidimar kuɗi.
Zuwa lokacin Maryam da Hafsat kowace ta tara yara don haka hidimar tai mai yawa ga rashin kwanciyar hankali ga hidimar gida ta mata uku da yaransu domin itama Badiyya ta haihu.
Suna a haka ne Hafsat ta cika jakarta da kaya ta watsar da yaranta tace dole sai ya sake ta, ga shi yana masifar sonta duk abin da suke mai a cikinsu babu wadda zai iya rabuwa da ita domin baki ɗaya so yake ya shafe tabon da mutane ke mai na cewa bai iya riƙon aure, saboda babu wadda saki bai ratsa a tsakaninsu ba da ita.
Mutane ba ruwansu da tambayar ko jin gaskiyar magana kawai sai suka yanke mai mummunan hukunci na cewar bai riƙon aure wasu ma cewa su ke zagi da dukan mata yake bayan bai taɓa dukan mace ba sai maida magana idan suna yi mai rashin kunya.
Saboda mutane ne yasa bai da burin ƙara sakin kowace mace daga matansa wanda hakan da suka fahimta yasa suke gwara mai kai tamkar wani majaujawa idan wannan ta yi yaji ta tafi gidansu ya samu ta dawo sai waccan ta tafi nasu gidan.
Yanzu haka Badiyya ke gidansu mahaifinta ya tabbatar mai da cewa ba zata sake komawa gidansa ba, haka itama kullum sai ta kira shi a waya ta gaya mai magana mai ciwo akan ya sake ta ko tai mai rashin mutuncin da bai taɓa zato ba...yana cikin lamarin ne kuma Jiddah ta faɗo rayuwarsa a karo na barkatai.
Ajiyar zuciya ya saki lokacin daya dawo daga duniyar tunaninsa. Yanzu kuma ya kasa gane inda ya nufa tabbas yana son Jiddah amma bai san matsayinta ba tana da aure ko babu.
Mu haɗu a kashi na gaba.
Taku a kullum Haupha!!!!
managarciya