ZAMAN JIRA: Fita Ta Farko

Wannan littafin na jima ina kai da kawo kafin na amince har a raina zan iya yin shi, duba da yadda wasu abubuwan dake cikinsa ya shafi Adabin bariki ne, sai dai a kula hakan ya zo ne dole kuma marubuci duk inda alƙalaminsa ya juya indai akwai gyara to ba laifi ba ne don ya yi rubutunsa, dai ana san kodayaushe a kiyaye alƙalami yayin aiki da shi.

ZAMAN JIRA: Fita Ta Farko

ZAMAN JIRA


               *NA*
*HAUWA'U SALISU (HAUPHA)*




                       *SADAUKARWA*

Na sadaukar da wannan littafin ga duk masoyana, waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba. Ina fatan Allah Ya ƙara danƙon zumunci a tsakanin mu yasa mu gama lafiya.

             *JAN HANKALI*


Wannan littafin na jima ina kai da kawo kafin na amince har a raina zan iya yin shi, duba da yadda wasu abubuwan dake cikinsa ya shafi Adabin bariki ne, sai dai a kula hakan ya zo ne dole kuma marubuci duk inda alƙalaminsa ya juya indai akwai gyara to ba laifi ba ne don ya yi rubutunsa, dai ana san kodayaushe a kiyaye alƙalami yayin aiki da shi.

                          Page 1 

Kai tsaye ya shige gidan yana jin wani iskar 'yanci na bin ko'ina a jikinsa. Shi fa duk lokacin da zai saki mace ji yake tamkar an ɗauke shi daga ruwan zafi ne an saka shi cikin na sanyi. Babban abin da ke birge shi da kan shi matakan da yake bi kafin ya saki duk matar da yake aure, ba ƙaramin jin daɗin halin nan yake ba na shi, duk da yana sane da cewa halin nan na shi ba ƙaramin ɓata ma wasu rai yake ba, amma dai shi ko a jikinsa, abu guda ya sani shi ne babu wanda ya isa ya sauya ma shi ra'ayi akan halinsa na rayuwar aure da ma sauran halayensa na yau da gobe.  Yana jin waƙar nan ta Sani Liya-liya mai suna 'mafaɗacin miji' ya afka gidan fuskarsa  kamar an yi mai albishir da zuwa Makkah ba ko sisinsa.  Turus ya yi yana ƙare mata kallo tana tsugunne sai kelaya amai take har da wani dafe ciki irin tana shan baƙar wahalar nan, murmushi ya saki ya kalle ta har zai wuce kuma sai ya dawo inda  take ya sunkuya ya dafa ta ya kama jera mata sannu yana shafa bayan ta. Yana gun ta gama aman, ya zuba mata ruwa ta wanke baki da fuskarta ya ɗebo ƙasa ya zuba ma aman, ya ja hannunta suka nufi ɗaki yana ta jera mata sannu. Ko da suka shiga ɗakin kai tsaye bedroom ya nufa da ita, sai bin ta a hankali yake tamkar a jikinsa ciwon yake a zahirance. Sai da ya taimaka mata ta kwanta ya ja bargo ya rufe mata rabin jiki, ya sunkuya daidai fuskarta ya ce cike da tausaya wa "Me kike son ci ko sha yanzu?"  Cikin muryar marassa lafiya tace, "Zan ci naman kai da biredi." Kamar ya kwashe da dariya sai kuma ya saki murmushi madadin dariyar ya ce, "Naman kan na Sa ko na Tunkiya ko Akuya ko na Ɗan'akuya wane kike so ne?"  Cikin galabaitar aman data sha tace, "Duk wanda aka samu zan ci."  Ɗan taɓe bakinsa ya yi ya fice, ransa cike da tunani, domin dai an raba mai hankali shi ya gama tsarawa yau sai ta kwana gidan ubanta, amma kuma ba zai hakan ba sai ya tabbatar da bata da ciki, idan har tana da ciki to tabbas zai haƙura ne sai ta haihu ta gama wanka ya yi zaman jiran abin da ta haifa ya isa yaye sannan zai saita mata hanyar gidan ubanta, don shi ba sakarai ba ne da zai zauna da mace ƙofar shiga alheri a wake kamar zaman sakarai ba. Da wannan tunanin ya je ya siyo naman kai mai lafiya da biredi ya dawo gidan, ya ɗauki waya ya kira ƙanwarta ya ce ta zo ta taimaka mata bata lafiya. Sai da ƙanwar ta zo sannan ya bar gidan, baka isa ka gane murna yake ko baƙin ciki ba.
Sai dare ya dawo, mamaki fal a fuskarsa ganin har zuwa lokacin ƙanwarta bata tafi gida ba. Cike da rainin hankali ya dube ta ya ce, "Me wannan take bata tafi gida ba har yanzu?"  Itama cike da mamakin a fuskarta tace, "Kwana biyu za tai min saboda jikina, idan na samu sauƙi sai ta koma gidan haka Mama tace."   Yamutse fuska ya yi ya dube su ya ce, "Saboda an ɗauke ni luƙeƙen ƙaton banza ko? To ba zan yadda ba 
 ta tashi idan sun rufe gidan ta ƙwanƙwasa su buɗe mata." 
Ta dube shi galala, sai kuma ta dubi agogo ƙarfe sha ɗaya har da rabi (11;30pm) zai ce yarinya ta koma gida, bayan shi ya kira waya ya ce a turo ta?
Ta dube shi cikin raunin murya tace, "Don Allah ka barta ta kwana a nan gobe sai ta tafi, yanzu dare ya yi ai... Kafin ta gama maganar ya kwaɓo mata wata maganar da  tashi zaune ba shiri. Bai ji komai ba ya sake maimaitawa, "Cewa na yi ita zata ban haƙƙina idan an jima ko ke? Don ba zan kwanan banza ba kin fi kowa sani. Kawai t? tashi kar ma daren ya ƙara nisa da safen ta sake dawowa, yanzu kam duniyar sama nake son zuwa duk yau shiru ce ba wadda ta sammun alheri kin ga kau ba zan bari nai kwanan keso ba a banza ina da mata ba."l0at
 Asiya na jin an zo nan ta miƙe ta ɗauki 'yar jakar kayan da ta zo da su ta yi tsaye idonta cike da hawaye ta ce, "Aunty bara na je kawai."  Itama kamar za ta fashe da kukan tace, "Yanzu ina za ki samu abin hawa cikin daren nan idan kin tafi?"     Ya yi wuf ya fito da ɗari biyar ya miƙawa Asiya ya ce, "Idan ba su isa ba idan kin je can gidan an cika maki,  gobe ki dawo wajen goma idan, idan kin ƙi dawowa kuma ita tai aikinta don ni dai ba abin da zai hana tai min aikin girkina ehe." 

Dukansu suka kalli juna jiki a sanyaye ta ja  ƙafa ta fice , Fati ta miƙe za ta  zata bita, ya janyo ta jikinsa yana sinsinar wuyanta, cikin raɗa-raɗa ya ce mata a kunne, "Madam mu je ki ban natsuwa duk a firgice nake, tsoro ma nake ji, ke ce kawai za ki saka min jarumta a wannan lokacin...  "Don girman Allah ka barni na kira yarinyar can kar ta fita a cikin daren nan, don Allah."  Sakin ta ya yi ya haɗe rai ya ce, "Ki je amma da nufin tana fita ki rufe min gidana ki dawo domin na rufe da na shigo ban san tana ciki ba. Kuma kar ki jima domin ke kawai nake jira komai ta nan a shirye yake." Ya juya ya shige ɗaki yana waƙa. 

Turus ta yi shin ƙanwarta za ta bi ko kuwa gidan za ta rufe ta dawo???


Haupha.......