Babban Buri:Fita Ta Biyar

Gaba ɗaya ba wanda ya damu da Hajiya Inna a cikin gidan ko wannensu baya bi takanta da'ita har ɗan marayan da Allah ya ɗaura mata riƙonsa...

Babban Buri:Fita Ta Biyar

BABBAN  BURI

MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.


SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU} MARUBUCIYAR MATAR ABDALLAH.


FITOWA TA BIYAR.

 Bayan shekara ɗaya.

Zuwa lokacin Aminu ya yi aure harda samun ƙaruwar ɗaa namiji sai dai uwar jinjirin ko ganinsa bata yi ba Allah ya ɗauki abissa.

Hankalin Aminu ya tashi, amman kuma daga baya ya fawwala wa Allah komai, bayan kwana bakwai da haihuwar jinjirin a kayi suna inda yaron ya ci sunan ƙanen mahaifinsa wato ALIYU HAIDAR , wanda wannan wasiyyar kakansa ce Alh Sulaiman Wurno kenan!.
Zuwa lokacin dukiya ce dashi dashi kansa besan a dadinta ba, ya yin da ya ɗaura ƙanensa a kan ragamar mafi yawa daga cikin dukiyarsa .

Wannan abin shine musibbabin fitowar tsantsar ƙiyayyar da ƴan uwansu suke yi masu a fili.
Lokaci ɗaya suka ɗauki alwashin salwantar da rayuwar ALIYU, daga Aminun har Aliyun ba wanda yasan ƙudurinsu su kaɗai ne ke sha'aninsu.

Ganin ƴan uwansa suna ta aure , waƴansu su kama haya waƴansu kuwa su zuba matan a cikin gidan da suke zaune , wanda aka raba gado ko wannensu ya ɗauki nasa da yake gidan babban gaske ne, sai Aminu ya yanke shawarar gina nasu estate wacce zata yalwanta su.

Ba tare da shawara da kowa ba bancin ɗan uwansa a ka fara gina babbar estate, da yake kuɗi ke magana lokaci ɗaya aka kammala estate wacce ke ɗauke da part part har guda arba'in.

Sai bayan kammala ginin ne ya sanar da kowa haɗi da sanya lokacin da zasu tare, murna a gurin ƴan uwansa ba'a magana.

A daren ranar da suka ɗunguma gaba ɗayansu zuwa sabon gidansu a daren a ka kashe Alh Aminu a gaban tilon ɗansa da kuma ƙanensa, wanda lokacin shekarunsa biyar a duniya.
Bayan sun gama ai watar da ƙudurinsu a kan Alh Aminu sai kuma suka zo suka fara turbuɗe waƴansu layu a cikin gidan, lokaci ɗaya ALIYU ya fice daga cikin gidan a guje shi a keyi har yau ba labarinsa.

Iya tashin hankali Hajiya Inna ta shigesa lokacin data wayi gari taga mummunan al'amari.
Haidar kuwa gaba ki ɗaya anrasa gane kansa daya buɗi baki ba abinda yake faɗa sai "Baba Bello Baba Usman Baba Amadu Baba sunusi.".
Hajiya Inna bata kawo komai ba , yayinda uwayen gayyar hankullansu suka dugun zuma ainun suka tashi addu'ar su ɗaya ce kar Allah ya bashi ikon tona masu asiri.

An bayar da cigiya a gidajen rediyo da talabijin da dama amman haka aka share shekaru kusan tara ba labarin Aliyu.

Kullum addu'ar Hajiya Inna itace , Allah  ya bayya mata ɗanta idan yana raye , idan kuwa baya raye Ubangiji Allah ya jikansa da rahmarsa.

Zuwa lokacin HAIDAR yana kule da dukkanin ƴan gidan ya tabbata bame sonsa a cikin su , haka zalika har yau abinda ya faru da mahaifinsa yananan cikin kansa.

Yayinda su kuwa suke ta faman shan sharholiyarsu da dukiyar Maraya, ba ruwansu duk abinda suka so dasu har ƴaƴansu basa shayin yinsa, sun mayar da India da american da Dubai kamar kasuwar ƴar marana ko yaushe suka tashi shigarsu ba shamakin komai suke lulawa duniyar sama.

Gaba ɗaya ba wanda ya damu da Hajiya Inna a cikin gidan ko wannensu baya bi takanta da'ita har ɗan marayan da Allah ya ɗaura mata riƙonsa.

HAIDAR yana da shekaru a shirin a duniya zuwa lokacin ya mallaki hankalin kansa a haka ya ƙetara ƙasar Amurika wajen faɗaɗa karatunsa na business a cewarsa yana son gadon mahaifinsa ta wannan fanni.

Shekararsa takwas a can yana kwankwaɗar madar ilimi kana ya dawo da niyar ci gaba da jan ragamar dukiyarsa da kansa kamin lokacin da gaskiya zata yi halinta.

Yayinda iyayensa suke da burin haɗasa aure da ɗaya daga cikin yaransu domin su samu dukiyar tasa gaba ɗaya ta dawo hannunsu, a yanzu haka suna kan duba cikin ƴaƴansu wacce ce tafi wayo da dabara.

HAIDAR yaro dogo fari kyakkyawa son kowa ƙin wacce ta rasa , fari ne sol kyakkyawan gaske , sai dai yana da murɗaɗɗan hali ba wanda ya isa yaji cikinsa bancin kakarsa wacce ya ɗauka a matsayin uwa uba, miskilin gaske ne.

*Wannan kenan*

Ajiyar zuciya Hajiya Inna ta sauke kana ta ɗan gincira a saman kujerar da take kai.
Minti 2 nauyayyen barci ya yi awon gaba da'ita, koda ya fito a kwance ya taradda da'ita ganin magariba ta kunno kai sosai ya sanya shi fara ta data.
Ganin ta tashi ya yi azamar miƙewa ya nufi hanyar ficewa daga ɗakin yana meyi mata sallama kan zaije masallaci sai ya dawo.


Bayan ya dawo ya samu Hajiya Inna da batun fara aikinsa da zaiyi a Company mahaifinsa , kallonsa ta yi sannan ta ce "hakan yana da kyau gskya sai dai yaushe zaka fara zuwan?" "Monday" ya faɗa yana me kwantar da kansa a kafaɗarta.

★★★★★★

Bayan munyi sallar isha'i su Ahmad sun dawo daga masallaci muka zuba abinci a guri ɗaya muka fara ci.

Kallon Mama na yi sannan na ce "Wai Mama yaushe Baba zai dawo ne?".

Lomar data ɗibo ta kai bakinta sannan ta haɗiye ta ce "meyuwa jibi zai dawo muga me muka samu kuma, ko Yaya AUWALU zai bari a sayar da gonar ko akasin hakan."

Gyaɗa kaina nayi cike da tausayin kanmu, uwa uba tausayin mahaifina ne kwance cikin raina.

Tsame hannuna nayi daga cikin abincin naje na wanke hannu na sannan na fito da ₦500 ɗinnan da Hajiya Inna ta bani na kawo wa Mama.
Gaya mata gunda kuɗin suka fito nayi cike da farin ciki take sawa abin albarka dani kaina kuma.
Bata karɓi kuɗin ba ta ce "naje na siyo masu abinda ya kamata.

Nida A'isha muka fice , shagon da ake sayar da kayan masa rufi muka nufa, ganin kuɗin mu ba zasu saya mana kwanon shinkafa ƴar Hausa ba ya sanya na siyo mana ƙaramin kwano {ɗan maraha}, sannan na siyo mana mai da maggic da sauran kayan buƙata.

Nan take ₦500 ta mutu muka koma gida da shinkafar da sauran kayan da muka saya.
Su Umar sai murna suke yi gobe za'a dafa masu shinkafa a gidansu, har ƙwalla sai da na sharce a kan tausayin kanmu.

Tun da daddare na kammala ƴan ƙananan aikace aikace, sannan na shiga kitchin na harhaɗa itatuwan hura wuta a cikin murhu da zummar da safe hasa wutar kawai zanyi.

Alwala nayi naje nayi shafa'i da wutiri sannan na yi addu'oina na shafa na tashi naje gefen ƙanwata ba kwanta haɗi da rufe jikina da bargo.
Sai dai me?

Haka kawai tunanin Shalelen Hajiya Inna ya faɗomin a rai, runtse idanuwana nayi haɗi da ƙara lafewa a saman katifar, iname tunano ƙamshin dana shaƙa lokacin dana shiga ɗakinsa.
Sauke ajiyar zuciya na yi , ko ba'a gayamin ba nasan tsafta ta ratsa bawan Allah.

Nice bansan lokacin da bacci ya ɗauke ni ba dama yau munsha aiki sosai a gidan aikinmu kuwa.

Nice ban sake juyi ba sai da naji sanyi asuba na ratsani, buɗe idanuwana nayi na sauke su kan agogon bangon dake sarkafe a jikin ginin ɗakin na yi, miƙewa zaune nayi iname karanto addu'ar tashi daga bacci الحمدلله} الله الذي أحيانا بعدما اما تنا  واليه النشور} sannan na miƙe naje na ɗauro alwala na tada sallah , raka'a huɗu na yi naji Mama na buga mana ƙauren ɗaki, gyaran murya nayi domin ta tabbatar dana tashi.

Bayan na kammala lazumi ne na tadda A'isha dasu Umar dake ta sharar bacci.

A tare dasu mukayi sallar subh kana nace ko wannen su ya dauko abin karatunsa idan da gyara na gyara masu.

Haka mukayi ta karatu har bakwai na safe da yake yau ba da wuri zan fita gidan aikina ba.

Miƙewa nayi naje na fara share share yayinda A'isha kuwa tayimin wanke wanke.
Muna kammala aikace aikacen gidan na ɗibi ruwa nayi wanka sannan na hasa wuta na aza mana ruwan kunu.
Suna tafasa na dama mana koko sannan na aza tukunyar girkin rana.

A haka na barwa A'isha girkin nace ta kula dashi sosai nayiwa Mama sallama na doshi hanyar gidan aikina....

Zamu cigaba a gobe.....

ƳAR MUTAN BUBARE CE.