DUHU DA HASKE: Fita Ta 36
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 36*
~Manal tayi murmushi tana kallon momy tace "shiyasa na cewa su man manal tashi ce ita kaɗai ba zan haɗashi da kowa ba, sannan daga yanzu zan fara aikina tunda dama na fara tunda jimawa, ameesha zaki san kin shigo gonan manal, yanzu nasa kowa yana zarginki wallahi saina nesantaki da man, baki san bakin cikin da nakeji ba a duk lokacin da naga man yana kallonki, bale naga ya taɓaki ko kuma naga yana miki kiss ji nake kamar nasa hanu aka nayi ihu, amma na danne na daure nayi kokari ban yadda nayi mistake ko ɗaya ta yadda zaku ganeni ba, har yazeed kun turo sabida ya shiga rayuwata ya gane ko nice ko ba ni bace, abinda baku sani ba shine manal tanada wayo fiye da kowa, amma banda mamanta"
dariya momy tayi sannan tace "kin sani ai nice kika gada, kin ganni nan? Abinda nayi ko rabinshi bakiyi ba manal, nice na haukace da kaina sabida na cimma wani burina kuma na cimma, tunda gashi na auri Alhaji Abdullahi"
Manal tace "momy dama kin sanshi ne?"
momy ta girgiza kai tace "ban sanshi ba, amma kinsan meya haukatani?"
tace "a,a momy"
tace "kishi, manal ko yatsana baki kamo ba a kishi, tsananin kishi yasa na haukace na fita a hayyacina, yau zan baki labarin duk abinda ya faru a rayuwata sabida ke ƴata ce"
manal ta zuba mata ido, tace "sunana rukayya amma kawayena suna kirana da ruky, mamana balarabiya ce babana kuma bafulatani ne, tunda na taso bana kula yaran talaka ko a hanya banso na haɗu da talaka, iyayena basu da karfi amma saida nayi iya yina ba siyi zazzafan mota kuma nasa iyayena a ƙerarren gida, a takaice da kaina na maida mu masu kuɗi, daga nan na fara yin kawaye yaran masu kuɗi sannan na fara samarai yaran masu hannu da shuni, kyawuna yana samamin komai da nakeso, watarana na haɗu da wani saurayi ɗan gidan tsohon shugaban kasa sunanshi Ahmad, manal naso Ahmad son da har ya illatani, akan Ahmad ina iya kwana banci abinci ba, Ahmad yana sona amma bai kai wanda nake mishi ba, muna soyayya sosai dashi sai kwatsam naji iyayenshi sun nema mishi matar aure harma ansa rana, kin san me nayi?"
girgiza kai manal tayi, murmushi momy tayi tace "faɗan abinda nayi ni kaina yana bani kunya da nauyi gara na rufe tunda Allah ya rufe"
haka aka fasa auren sunan gidansu ya ɓaci ya rasa daga ina matsalan yake, mahaifinshi ya kasa fita shi kanshi Ahmad ya kashe wayoyinshi sun zama kamar basa nan, kawai saiga ruky ta shigo rayuwarsu ta gyara kamar yadda ta ɓata, daga nan mahaifinsa yace ya aureni, bayan ya aureni sai naji ina son mahaifin ba yaron nakeso ba, to ya zanyi manal? saina fara yiwa mahaifin tallan kaina daga nan shima d sharrin shaidan da sharrina saiya amince, a duk lokacin da Ahmad baya nan sam bana damuwa tunda ina tare da ubanshi, sai na fara jin kishi akan maman Ahmad, naji bazan iya jure ganinshi yana tareda wata ba, saina fara neman hanyan rabasu, bayan na rabasu sai yace zaiyi aure, manal ashe Ahmad yasan halin da ake ciki, ya sakeni Abbanshi kuma zai yi aure, hmmm saida na rugurguza komai, saida nasa Ahmad da Abbanshi da mamanshi ko kallon juna basaso, mamanshi ganin kishi zai kasheni yasa ta kara tura matar da zai aure tana kara shiga jikinshi harma Abba ya daina ɗaukan wayata, a ranan da naji yayi aure shima Ahmad yayi aure a ranan saida na tabbatar babu wanda yake numfashi a cikinsu, daga nan nima na haukace na bar garin adamawa na koma kaduna da zama"
manal tace "amma momy ke muguwa ce ashe ke na biyo"
tace "wannan kaɗan ne daga cikin abinda na aikata wanda na faɗa miki sauran ba zai faɗu ba sabida ke ƴata ce"
manal tace "to yanzu momy ya zanyi na mallaki man?"
momy tace "yazeed tunda na zauna dashi naga soyayyan ameesha a idonshi, zakiyi amfani da wannan son da yake mata ki jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya"
tace "kina ganin zai yadda?"
tace "kwarai amma saikin fito mishi da asalin ke wacece daga nan zai yadda"
tace "to momy ki tayani addu'a"
tace "hmm koda banyi miki addu'a ba zakiyi nasara, a ranan da zasu ratayeki ina biye dasu nasan na baki maganin da zaisa ki suma tun kafin ayi miki hukunci basu sani ba suma kikayi sun zaci mutuwa kikayi, ni kuma ana kaiki nasa aka toneki daga nan na turaki saudiya sabida ki nutsu ki koyi larabci kizo kiyi musu basaja kuma hakan ya faru domin kuwa kin ɓata auren hakika man naki ne ke kaɗai, yanzu ki shirya dole ki san me kike yi"
tace "to momy bari na fita kada suyi zargin wani abu"
tace "to jeki"
fita tayi taga ameesha zuwa yanzu ta fara kuka harda shesheƙa Imran sai lallashinta yake, zama a gefenta amal tayi tace "ki daina kuka komai zaiyi"
Imran ya bita da kallo shi haka kawai ya kasa nutsuwa da yarinyar.
kamar da wasa har kwana biyar basu bari anga Abba ba banda news da ake yaɗawa tako ina, hanan har zazzaɓi tayi, sam babu wanda yake kula ameesha sai Imran ne, man dasu ammi duk sun ɗauke mata wuta, baba baya zama kullum yana hanyan zuwa duba Abba, yauma kamar kullum ya shirya zai fita duk da basa barinshi ya ganshi hakan baya hanashi zuwa, ammi tace "Allah kiyaye hanya Allah ya tsareka"
yace "ameen ina ameesha?"
tace "inaga tana ɗaki"
komawa yayi yaje ɗakinsu tana kwace tayi shiru tana kallon sama hawaye yana wanke mata fuska bata damu data share ba, zama yayi yace "ameesha?"
tace "na'am baba"
yace "tunda nake ban taɓa ganin mace me jajircewa kamar ke ba, bai kamata wannan abin yasa ki zama weak ba, kinyi taimako sosai sannan shi abban naku yasan ba zaki iya haka ba, yau nayi miki alkawari idan naje sai sun barni na ganshi ko a ɓoyene zan haɗaki dashi a waya kinji?"
da sauri tace "da gaske baba?"
yace "kwarai da gaske Allah ya miki albarka"
tace "ameen baba"
rakashi tayi har zuwa kofa, a lokacin man ya shigo duk ya rame yace "sannu baba"
baba yace "yawwa Abdulrahman bari naje na duba abbanku ko?"
yace "baba koda kaje basa bari a ganshi"
yace "hakan ba zai hana naje ba man, ka kula da ameesha kada kuyi zarginta akan abinda kun san ba zata iya ba"
baiyi magana ba, baba yace "Allah muku albarka kune family ɗina, na rasa kowa amma na sameku a rayuwa kuma naji farin ciki sosai ina fatan Allah ya kara baku hakuri duk wanda kuka shiga rayuwarshi sai kun maidashi mutum yaji kamar yanada family Allah muku albarka"
suka amsa da ameen, har wajen mota suka rakashi, yana tafiya suka raba hanya kowa yayi tafiyanshi basuyi magana ba.
har dare baba bai dawo ba daga duba Abba, man da yazeed tare suka fita nemanshi sun fara zuwa station akace musu baizo ba, daga nan suka fita cikin tashin hankali suna tafiya, yazeed ne yaga mota a kone a gefe kamar accident akayi da sauri yace "man tsaya"
tsayawa man yayi yace "menene?"
yace "kalli wani mota a kone"
tsayawa yayi babu shiri yana kallon wajen, tare suka fito, ganin motar a kone man yace "tabbas wannan motar baba ne"
tambaya suka fara wani yace musu ai accident akayi ɗazu da safe mutumin ciki ya rasu basuma cire gawanshi ba, kasancewar babu waya shiyasa kowa kawai ya bari sabida ba'asan ta yadda za'a fara neman family ɗinshi ba"
man daurewa yayi bayi ihu ba, yazeed kam zama yayi daram a kasa yana cewa "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
waya suka kira sukace ammi da duk ƴan gidan suzo, sun faɗa musu daidai inda zasu samesu, harda momy wacce itace ta haɗa abin suka fito tana ciza baki alaman batada lafiya, ammi suma tayi lokacin da taji kuma taga abinda ya faru da baba, ameesha wacce ta bisu a baya, kuka ta fara tana cewa "Baba? Baba?"
yazeed cikin tsana yace "duk ba dan ke hakan yake faruwa ba?"
tana kuka tace "yaya yazeed....."
tafiya sukayi suka barta a wajen tayi kuka kamar ranta zai fita da kyar ta iya lallaɓa kanta ta koma gida, zazzaɓi me zafi ya rufeta ta kasa gane kanta sai rawan ɗari take, duk gidan ya zama shiru babu wanda yake yanayi me daɗi, rabonsu da shiga irin wannan yanayin tun manal na raye, haka suke rayuwa yanzu babu me kula ameesha duk abin duniya yayi mata yawa, ga mutuwan baba daya tsaya mata a rai, manal da momy sun san takunsu ta kasa suke shirya komai ba tareda kowa ya gane ba.
yazeed ne zaune akan sofa yana danna laptop, ya rame kaɗan ya zama wani kala, Amal ce ta fito daga ɗaki tayi kyau cikin baƙin riga da wando, a gefenshi ta zauna ta zuba mishi ido, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, tace "yazeed?"
da mamaki ya kalleta jin ta kira sunanshi kai tsaye tayi murmushi tace "kayi mamaki ko dana kira sunanka?"
bai kulata ba, tace "nazo maka da wata magana ne idan ka yadda shikenan"
yace "ina jinki"
tace "naga soyayyan ameesha a idonka ina kula da yadda kake ɗauke kai idan kaga tana tareda man, ni kuma matar man ce ina laifin mu haɗa hanu mu raba man da ameesha kai ka auri ameesha ni kuma na komawa mijina"
aje laptop ɗin yayi a gefe ta kalleta yace "kin san me kike cewa kuwa? wacece ke?"
tace "sunana manal umar maidawa"
da mamaki yace "kina nufin keba Amal bace?"
tashi tayi, hanunta tasa akan ɗayan karamin yatsan dake gefen hanunta ta cire, rufe ido yayi, ganin ta cire yatsa ba shida dake gefen hanunta tace "niba Amal bace hasalima acting na Amal da nake haushi yake bani domin ina kaskantar da kaina ne, idan har ka amince mu haɗa hanu idan baka amince ba shikenan"
juyawa tayi zata tafi yace "na amince"
murmushi tayi ta juyo ta mika mishi hanu suka gaisa tace "karka manta nice manal duk abinda zakayi dan ganin kamin sharri ko kuma ka fallasani zan rigaka sabida manal tasan me take yi"
yace "na jima inason ameesha hanyan samunta ne na rasa shi yasa na hakura"
tace "kwarai na sani kuma na maka alkwarin zan mallaka maka ita"
yace "amma waya fitar dake daga kabarin da aka binneki?"
murmushi tayi tace "wannan bai shafeka ba"
daga nan ta tafi, tun daga ranan suka haɗa hanu da yazeed duk hanyan da zasu raba man da ameesha saida sukabi.
zuwa yanzu man babu wacce ya tsana kamar ameesha ta rame sosai tayi fara, damuwanta shine halin da ammi take ciki bata yanayi me daɗi, momy ce kawai take kula da ita, yauma kamar kullum ta gama shan kuka ta fito ciwon kai takeji kamar zata faɗi tana tafiya, man ne ya shigo shima ya ɗau laptop nashi daya manta zai fita ameesha ta faɗi a jikinshi, laptop ɗinne ya faɗi ya tarwatse wani irin huci yake yi yana kallonta, zatayi magana taji ya wanketa da mari, zuciyanta yana tafasa tace "kai wani irin mara imani ne man? ko dai haɗa baki kayi da manal duk abinda ya faru sabida ta dawo cikin rayuwarka dan naga ka fara janta a jiki"
cikin bakin ciki yace "kin manta wannan Amal ce ba manal ba? kuma koda manal ce tafi min ke sau dubu tunda bata tura wanda ya taimaketa da sharrin da yafi kowane sharri muni a duniya gidan yari ba"
cikin ihu tace "kada ka kara gayamin wannan maganan man"
yace "idan na kara fa?"
gabanshi taje ta tsaya ta kamo hanunshi ta fara dukan kanta dashi tace "ka kasheni tunda ka tsaneni ka kashe ni man"
tureta yayi ta faɗi kasa ya fita a gidan, bata kara motsi ba sai kallon sama da take, taji azaban ciwo duk yadda taso tayi magana bakinta ya kasa furta komai, Amal ce ta fito daga ɗaki tace "Ameesha meya sameki?"
ganin ta kasa magana tayi murmushi tace "bari na ɗauko miki magani"
fita tayi daga ɗakin taje ɗakinsu man yazeed yana kwace akan gado tace "ina alluran dana baka? yanzu ya dace ayi mata"
yace "amma manal ina tsoro"
tace "karka damu har a gama auren kafin zata tashi ta fara tafiya karka damu bani"
alluran ya ɗauko mata ta karɓa ta fita, inda ameesha take kwance tayi mata a jijiyan hanu, nan take taji jikinta ya saki, ta kasa motsi sai kallo kawai take bin kowa dashi, manal ta jata a kasa zuwa ɗaki ta kwantar da ita akan gado sannan tace "bye ameesha kin fita a rayuwar man yanzu daga shi sai manal tashi kawai zasuyi rayuwa karki damu jim kaɗan zan ɗaukeshi daga wannan gidan kamar a baya"
murmushi tayi ta fita, da gudu taje cikin mota ta nufi company ɗinsu man, shiga tayi ta fara neman man a firgice yace "menene?"
tace "ameesha bata magana bata motsi"
yace "ina ruwana?"
ta zube kasa tace "dan girman Allah kaje ka taimaka mata dan Allah"
hanunta ya rike suka fita tare a motarta suka tafi, suna zuwa gida yaga yadda ameesha take kwance yace "wannan shine karshe duk wani me sharri a yadda kike a kwance haka ameesha zan auri Amal"
durkusawa kasa yayi ya mikawa Amal zoben hanunshi na karamin yatsa yace "will you marry me?"
tace "amma ameesha"
yace "forget about ameesha will you marry me?"
a hankali tace "yes"
murmushi yayi yasa mata zoben, kallon ameesha yayi yace "yadda kikeji haka shima Abba yake ji a ranshi, da ciwo wanda ka yadda dashi yaci amananka"
tana kwance tana kallonsu idonta a bushe bakinta ma haka.
haka take rayuwa a kwance babu me kulawa da ita sai imran da fahad, duk sun zama shiru shiru sabida rashin lafiyan ameesha ga kuma auren da man yace zaiyi na Amal a wannan juma'a, Imran yace "watakila Allah baiyi zamuji daɗi ba a duniya shiyasa hakan yake faruwa dama kowa da irin ƙaddaranshi wasu me kyau wasu marar kyau Allah dai yasa muji daɗi daga karshe"
fahad ya amsa da ameen,
manal tace "momy kin cika uwa domin kuwa komai yana tafiya daidai da yadda muka tsara kuma ance Abba ba'a ma bari a ganshi, hakan yasa man ya kara jin tsanan ameesha a ranshi a tunaninshi wacce aka yadda da ita taci amana, sannan an rufe gidan marayu yanzu babu komai, kuma daga karshe gado zai zama naki domin a dole kece zaki gaji komai, ammi ko zuwa part ɗinnan batayi tayi matukar fushi da ameesha wannan wasan namu yayi sosai momy.
momy tace "a koda yaushe mune zamuci kowane wasa"
tace "Abdool na manal ne ita kaɗai"
_jiddah Ce...
managarciya