DUHU DA HASKE: Fita Ta 13
shiru yayi na ɗan lokaci, kallon faruk yayi yace "to muje gidan nasu mana mu duba ta tare" faruk ya girgiza kai yace "no kaje ka dubata zanji dasu mr chang zan basu hakuri har tazo dan nasan idan taji shine babu abinda zai hanata fitowa koma menene" da sauri yace "to shikenan kaje kaji dashi bari naje" yace "saika dawo"
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 13*
~Kwance take akan gado tana rawan sanyi hakoranta suna haɗuwa sai kankame jiki take tana kara jan bargon tana rufa har kanta, amai taji yana zuwa mata da sauri ta tashi zata sauka akan gadon kawai taji aman yazo, jini take amarwa akan farin bedsheet ɗin dake kwance me taushi akan gadon, ji tayi kirjinta yana zafi jikinta yana zufa, ammi wacce ta fita domin kawo mata maganinta ta buɗe kofan ta shigo hanunta rike da glass cup cike da ruwa da kuma maganin a ɗayan hanunta, faɗuwa glass cup ɗin yayi a wajen ya tarwatse, cikin ihu tace "manal"
da gudu ta watsar da maganin taje kan gadon tana tiketa, tayi aman jini sosai kafin ta ɗago tana haƙi tana kallon Ammi, cikin tashin hankali ammi tace "bari na kira dr habib"
bata musa ba ta koma ta kwanta tana cigaba da rawan ɗari, kiran wayan dr habib tayi tace "kazo yanzu jikin manal ya tashi kuma da alama yayi worst domin tana aman jini sosai, ka taimakeni dr ka taimakeni"
yace "okay ina zuwa"
kifa kanta tayi akan ƙafan manal ta fashe da kuka kamar zata shiɗe, manal dake cikin bargo ta miko hanu tasa hanunta cikin nata ta damke, man sai safa da marwa yake a cikin company ya rasa abinyi, manal tana yawan gaya musu batason abinda zai ɓata tsakaninta da wanda suke harka dasu na kasar china wato mr chang, sai kiran wayanta yake ba kakkautawa yana shiga amma bata ɗauka, yana tsaye ya rasa abinyi yaji an dafashi, da sauri ya juyo faruk yace "man mr chang fa yace idan ba'ayi wannan zaman yau ba zaiyi resign da company ɗin m.u.m kuma madam tace koda wasa bataso ta rabu dasu ina ganin sai kaje gida kaga ko meya hanata fitowa dan shima yanzu yanata kiranta bata ɗauka, kuma yace koda wakili ne ta tura suyi wannan zaman"
shiru yayi na ɗan lokaci, kallon faruk yayi yace "to muje gidan nasu mana mu duba ta tare"
faruk ya girgiza kai yace "no kaje ka dubata zanji dasu mr chang zan basu hakuri har tazo dan nasan idan taji shine babu abinda zai hanata fitowa koma menene"
da sauri yace "to shikenan kaje kaji dashi bari naje"
yace "saika dawo"
motarshi ya shiga da sauri ya fita, gudu yake akan titin yana kara gwada number ɗinta ko zata ɗauka bata ɗauka ba, cikin jin haushi ya aje wayan, a kofan gidansu yayi parking ya fito yana knocking, ammi wacce ta kasa zama ganin manal tana kara yin aman ta fito da gudu ta mayar Dr habib ne, da kanta ta buɗe gate ɗin a rikice tace "Dr kazo da sauri zata mutu..."
ganin Abdool tsaye yana shirin gaisheta taja hanunshi da sauri kamar ma bata cikin hayyacinta tace "yawwa gara da kazo ka taimakeni manal zata mutu"
Binta yake yana kallonta da mamaki, ɗakin manal ɗin ta kaishi suna shiga tana amai sosai ta ɓata gaban riganta, zaro ido yayi yace "madam?"
tare da ammi suka karasa wajenta, tana ganinshi ta mika mishi hanu riketa yayi yace "madam"
aman ne ya tsaya cikin galabaita tace "Abdool zan mutu"
da sauri yace "ba zaki mutu ba"
idonta cike da hawaye tace "koda banda lafiya babu me zuwa wajena sai ammi"
kuka take yi me taɓa zuciya, dr habib ne yayi sallama ammi tace "shigo"
shigowa yayi ya fara dubata, man ya cire bedsheet ɗin daya ɓaci da jinin ya fitar waje ya bawa me aikinsu, ammi ta juya hotonshi ta yadda ba zai gani ba, allura yayi mata sannan ya kalli ammi yace "ciwon manal yana karuwa ku rinƙa kula da ita ku daina barinta ita kaɗai akwai matsala babba idan ana barinta ita kaɗai tunani yayi mata yawa sannan wannan rashin dariyan nata shi yake kara ciwon idan so samu ne kuyi mata aure"
shiru ammi tayi sai sharan hawaye da take, shi kuma Abdool ya zauna a gefe yana kallonta tana bacci cikin nutsuwa, har Dr ya tafi babu wanda yayi magana, a cikin bacci tayi juyi ta turo baki sannan taci gaba da baccinta, sun ɗau lokaci kafin ya turawa faruk text "yana nan?"
faruk yayi reply da "eh"
baiyi magana ba ya tashi zai tafi cikin muryan ciwo tace "Abdool"
da sauri ya juyo yace "na'am madam"
da hanu tayi mishi alaman yazo, zuwa yayi ya tsaya yana sunkuyar da kai, ta mika mishi hanu tace "ɗagani"
ɗagata yayi ta zauna tana kallonshi tace "me yasa kazo?"
yace "dama mr chang ne yazo kuma yace idan bai haɗu dake ba wannan shine last chance, na kira wayarki kuma baki ɗauka ba shiyasa nazo"
a hankali tace "to yanzu idan ka tafi me zakace mishi?"
shiru yayi, tayi murmushi tace "zakace banda lafiya?"
gyaɗa kai yayi, ta nuna mishi gefenta tace "zauna"
zama yayi ta ɗau waya ta kira numbern mr chang, cikin sanyin muryan rashin lafiya tace "unfortunately I won't be able to attend but my manager will be representing me"
tana faɗan haka ta sauke wayan, man da mamaki yake kallon ta, a hankali ta sauka akan gadon cikin ciwo da rashin karfin jiki da jinin daya ɓata mata gaban riga taje cikin wardrobe nata ta buɗe, ciro wani kayan data ɓoye na dady tayi sannan tazo babanshi, tashi yayi dan ganin me take shirin yi, a hankali ta durkusa kasa ta mika mishi kayan tace "will you be my manager?"
da sauri ya kalleta sannan ya kalli jinin dake gaban riganta tunawa yayi da abinda Dr ya faɗa, a hankali yasa hanu akan kayan da take mika mishi ya haɗa da hanunta ya ɗagata, tissue dake gefe ya yaga ya goge mata bakinta duk inda jini ya ɓata a fuskanta a hankali ya jijjiga kai yace "not only your manager but also your caregiver"
murmushi ammi tayi cikin hawaye tace "zaka kula da ita da gaske?"
a hankali yace "insha Allah"
manal tayi dariya kaɗan sannan tace "wannan kayan mahaifina ne yanzu nake so kasa dashi zaka je kayi representing ɗina"
zai yi magana tace "no please Abdool"
tausayi take bashi a hankali ya karɓa, ta nuna mishi toilet tace "shiga ka canja"
shiga ciki yayi ta koma bakin gadon ta zauna tana rufe ido domin kirjinta ciwo yake mata, tana zaune a wajen ya fito cikin manyan kayan shadda ne me kyau maroon da hula maroon, yayi kyau sosai kasancewar bai saba sa manyan kaya ba yasa hulan bai zauna akanshi yadda yake so ba, murmushi akan fuskanta ta tashi zuwa wajenshi tayi mishi alaman yayi kyau, sunkuyar da kai yayi badan yaso ba yasa kayan, gyara mishi hulan tayi sannan ta lumshe ido ta buɗe akanshi, yace "zan tafi"
tace "Abdool"
tsayawa yayi, taje ta buɗe drower ɗinta ta ciro sabon makullin mota tazo gabanshi ta mika mishi hanunta tace "bani makullin motarka"
yace "me zakiyi da ita?"
tace "bani mana"
bata yayi ta rufe a hanunta, sabon makullin mota ta bashi sannan tace "wannan naka ne wa kai na siyawa sabida ka zama manager kasan komai ya dawo kanka na company, fitowa da wuri tashi bada wuri ba, sannan zaka iya yin tafiya zuwa kasashe da dama a koda yaushe ka zauna cikin shiri domin kaine zaka rike company ɗin m.u.m"
girgiza kai yayi yace "gaskiya ki barni da motata a matsayin da nake ma a company ina aiki ina samun kuɗina ya isheni"
girgiza kai tayi tace "Abdool kokarinka yasa na baka wannan matsayin ba wai sabida wani abu ba kuma ka cancanta"
girgiza kai yayi yace "gaskiya banaso ki bani makullina kawai."
bashi tayi ta juya tana sharan hawaye rike kirji tayi tace "kullum saina faɗa miki ammi harta kyautan da zan bawa mutane basason karɓa a hanuna"
jikinshi yayi sanyi sosai yace "zan karɓa"
murmushi tayi da sauri ta juyo tana share hawaye tace "da gaske zaka karɓa?"
jijjiga kai yayi ya mika mata hanu, danka mishi makullin tayi, yace "na tafi"
ammi tace "Abdool"
tsayawa yayi, tace "Allah ya maka albarka ya kareka da kariyanshi ya tsareka da sharrin kowane sharri"
ido manal ta zuba mata, shiru tayi yace "ameen"
fita yayi jikinshi a mace, duk abinda ya karɓa ba dan kanshi yaso ya karɓa ba sai dan mummunan rashin lafiyan da yaga tana dashi, motar ya kalla wanda tace shine nashi, mota ne me matukar tsada dallele fari jikinshi a mace ya shiga, da gudu yake tuka motar har ya isa company, da sauri ya shiga ciki, da mamakinshi tun daga bakin kofa yaga sunyi decoration yana shiga yaga an tsara wajen faruk ya kalla wanda yake mishi dariyan farin ciki, cake sukazo wajenshi dashi sukace "muna tayaka murnan zama manager sannan munji daɗi da kaine ka zama manager mun tabbatar zamuji daɗi mu samu walwala a company ɗinnan"
cak ya tsaya yana kallonsu faruk yazo yaja hanunshi sauran suna biye dasu ya kaishi tsararren office ɗinshi dake kusa dana manal a saman office an rubuta ABDOOL da manyan harufa buɗe mishi sukayi faruk yace "madam ta kiramu a waya ta faɗa mana komai"
shiga yayi yana kallonsu sunki barinshi yayi magana, kujeranshi faruk ya nuna mishi yace "wannan shine kujeran manager"
zaiyi magana faruk ya zaunar dashi, wata da suke kiranta da husna tazo da cake ɗin gabanshi da karamin wuƙa ta mika mishi, yace "wai me kukeyi haka ne?"
faruk yace "mu yanka cake"
sa mishi wuƙan yayi a hanu suka yanka cake duk sukayi tafi sukayi ihu, a hankali yace "nifa ban..."
faruk yace "dan Allah kada kaki matsayin da Allah ya baka idan kayi haka baka kyauta ba, Allah ne ya zaɓe ka a cikin mutane dayawa sabida yaga kyawawan halinka ya baka matsayi dan Allah kada kaki yadda da ƙaddara kaji?"
a hankali ya sunkuyar da kai yace "to amma faruk..."
husna tace "ya abdool yadda kake bawa kowa farin ciki a wannan company muma zamu so mu ganka cikin farin ciki kodan madam da take taƙura mana ka karɓi wannan matsayin ka rike hanu biyu sannan ka mana alkawarin ba zaka mayar ba"
a hankali ya kallesu duk sunyi kalan tausayi, murmushi yayi yace "na karɓa"
ihu sukayi suna tafi, faruk yace "mr chang zai shigo yanzu"
fita sukayi su duka faruk ne ya yiwa su mr chang ido, koda suka shigo Abdool ya nuna musu waje suka zauna su uku sanye da bakaken suit.
manal tana zaune a bakin gadonta tayi wanka ɗaure da towel a jikinta, computer ta janyo ta ɗaura akan cinyarta tana kallon duk abinda yake faruwa daga lokacin da suka fara shagalin har lokacin dasu mr chang suka shigo, cikin nutsuwa yake musu bayani banda murmushi babu abinda take yi, gyara zama tayi ta jingina bayanta da jikin gadon duk da tana jin ciwon amma taji sauki da take ganinshi,
Ameesha cikin wani irin gudu ta isa gidansu man kamar zata kife kasa ta shiga ɗakin umma Imran dasu Anty suna tsaye a kan umma dake kwance flat akan gado bata motsi, cikin tashin hankali tace "umma umma ki tashi mana na kira wayan man tun ɗazu baya ɗauka"
Imran idonshi cike da hawaye ya zauna akan stool na kusa da gadon ya dafa kanshi, Anty tace "kawai tana tsaye ta yanke jiki ta faɗi? meya ɗaga mata hawan jinin?"
Imran ya girgiza kai kawai ya kasa magana, Anty kiran man ta fara da wayarta yana shiga baya ɗauka, ameesha kara kira tayi kusan kira ishirin tayi mishi wurgar da wayan tayi tace "ya zamuyi? man bai ɗauki waya ba"
Imran yace "ko zamu je mu kirashi?"
tashi tayi ta share hawaye tace "ka zauna dasu Anty ni zanje na kirashi"
da gudu ta fita, napep ta tara ta mishi kwatance tace "dan Allah kayi gudu"
gudu yake da ita banda murza yatsun hanunta ba abinda take yi, a kofan company ya sauketa ta fita da sauri tana laluben kuɗi a aljihu.
manal dake kallonsu ta juyo da camera zuwa waje domin ganin abinda yake faruwa, huci ta fara lokacin da idonta ya sauka akan Ameesha wacce take laluben kuɗin da zata biya me mashin, wayarta ta ɗaga ta kira me gadi, cikin kakkausan murya tace "zan tura maka wani hoto kada ka barta ta shiga company je watsapp yanzu"
kashe wayan tayi atake ta tura mishi hoton yace "to madam"
tana bashi kuɗin bata tsaya jiran canji ba ta juya da gudu zata shiga cikin company me gadi ya tare kofa, da sauri tace "dan Allah nazo neman Abdool ka taimaka na shiga ko ka kiramin shi"
girgiza kai yayi yace "babu me shiga ki koma inda kika tashi"
da karfi tace "ka buɗemin kofa mahaifiyarshi ce batada lafiya"
kallonta yayi yaga tana huci kamar zata kai duka, yace "okay bari na shiga na kirashi ki tsaya anan"
tace "to kace mishi ameesha ce tazo umma babu lafiya yazo mu kaita asibiti"
yace "okay"
shiga ciki yayi ya rufe kofan ya barta a waje, safa da marwa take tana murza hanunta ta kasa nutsuwa, riga da wandon jinx ne a jikinta sai rigan sanyin data ɗaura a waist nata baƙi, tayi kyau kamar ka sace ta, manyan idanunta sun cika da hawaye ɗan karamin bakinta sai rawa yake, karan hancinta yayi jajur sabida sharan hawaye da take yi akai akai, tsayawa yayi ganin kiran madam yana shigowa, da sauri yace "madam tace....."
cikin bada umarni tace "kace mata yace yana meeting baison haɗuwa da kowa yanzu"
yace "amma fa madam mahaif...."
ji yayi ta katseshi tace "mahaifiyarshi babu lafiya kwarai naji ka koma kace mata yace yana meeting baison haɗuwa da kowa"
shiru yayi, a tsawace tace "ko bazaka faɗa ba?"
a hankali yace "zan faɗa"
kashe wayan tayi, ya kasa tafiya na tsawon minti biyar kafin ya buɗe kofan, da sauri tazo tace "ina yake? yana zuwa ko?"
girgiza kai yayi yace "yana meeting yace bayason haɗuwa da kowa a halin yanzu"
cikin razana ta kalleshi, sannan ta girgiza kai tace "karya ne ba man bane ya faɗi haka ka buɗemin kofa kafin nayi maka ihu anan"
yace "shine"
tace "karya ne"
wayarshi ya buɗe ganin message ya shigo, video ɗin man yana zaune dasu mr chang ya gani manal ce ta turo mishi tace "ka nuna mata"
ameesha tureshi tayi da karfi zata shiga yace "kinga"
tsayawa tayi tana kallon wayar, ganin man tayi zaune a kyakkyawan office sanye da shadda me tsada yana juyi akan kujeranshi da aka rubuta manager suna tattaunawa da wasu fararen fata sanye da bakaken kaya suit, baya tayi bata buɗe kofan ba, tace "wan...nan ba... man ba...ne shi bada kayannan ya ya..fita ba"
cikin in ina tayi maganan ya matso mata da wayan yace "gashi kina ganinshi kuma ai shine manager ɗin wannan company kinga motarshi can"
buɗe kofan yayi yadda zataga motan taga an rubuta "ABDOOL MD"
a jikin motan, shiru tayi cikin shock take tsaye a wajen, yace "bai jima da dawowa daga gidansu madam ba ya jima acan shiyasa yayi late ɗin meeting ɗin"
cikin shocking ta buɗe bakinta da yake rawa, idonta ya tsaya da hawayen tace "m..ma.manal kenan?"
gyaɗa kai yayi yace "kwarai ai kullum yana zuwa idan yazo sai an kusa tashi suke dawowa tare"
a hankali ta juya baya ta fara tafiya, bata ce komai ba sai tafiya take kamar batada lafiya, hawayen sun tsaya, zuciyarta yana harbawa da sauri da sauri, duk maganan da ya faɗa mata yana dawowa kanta, saita tuna idan suna waya sai yace ana kiranshi har dare idan ta kirashi sai taji yana waya ta zaci ko aiki ne yasa hakan har tayi bacci sai safe suke haɗuwa, har ta hau kan kwalta bata sani ba, saura kiris wani mota ya bigeta bataji ba kuma bata gani ba tafiya kawai take, sauke glass yayi yace "ke makauniya ce? ki matsa akan hanya dalla"
matsawa tayi akan hanyan taci gaba da tafiya, tsayawa tayi ganin zata ɓata lokaci ta tari napep tayi mishi bayanin zai kaisu asibiti sannan ta shiga, har kofan gida ya kaisu ta fito ta shiga gidan da sallama, Anty da Imran da fahad har suna rige rige wajen tambayan "ina Abdool?"
a hankali tace "ban sameshi ba may be wani waje ya tafi"
Anty tace "ina zaije ya bar wayanshi?"
tace "mu fita da ita me mashin yana jiranmu a waje"
tare suke rike umma suka ɗagata har waje zuwa napep ɗin, kulle gidan sukayi suka shiga napep ɗin su duka, tafiya sukayi ameesha sai ɗauke kai take tana share hawaye "ai shine manager kullum tare suke tafiya da madam sai an kusa tashi suke dawowa, yace bayason ganin kowa yana meeting"
toshe kunne tayi tace "no.no..no"
Anty tace "ki nutsu ameesha zata samu sauki insha Allah"
city hospital ya kaisu ameesha ce ta yiwa likita magana sukazo da gadon suka ɗaurata akai tareda su Imran suke turawa har zuwa bakin kofan emergency room, suna tsaye su duka a bakin kofan kowa yayi shiru, ameesha sai kai kawo take yi, sun jima sosai sun kai awa biyu kafin aka buɗe kofan ameesha data zauna a kasa tayi tagumi ta taso da sauri har tana tuntuɓe tace "ya jikinta Dr?"
yace "da sauki amma kunyi late na kawota asibiti hakan yasa jikin yayi weak sosai, tanada hawan jini me karfi sannan abu kaɗan zai iyasa ta faɗi ƙasa ba fata ba zata iya kama struck wato shanyewan ɓarin jiki sai an kiyaye"
ameesha tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un me yake damun umma daya kawo mata hawan jini? tunanin me take?"
Imran yace "zamu iya shiga?"
dr yace "eh amma idan ba zakuyi surutu ba dan hayaniya kaɗan zai iya kawo mata matsala"
sukace"to dr"
shiga sukayi duk jikinsu a mace musamman ameesha wacce har yanzu take cikin shock.
man sun jima suna meeting kafin suka tafi, saida aka tashi ya fito da sauri dan yasan yayi late ameesha zatayi ta jiranshi, yana fita ya shiga motar da aka bashi yayi hon zai fita megadi yace "yallaɓai?"
tsayawa yayi, megadi yace "ɗazu wata naga tana binka kuma sai kaga kuna tafiya tare da ita, daga baya naga tazo tace min wai mamanka babu lafiya zanyi magana naga ta juya a zafafe ta tafi"
da sauri yace "meesha?"
yace "ban san sunanta ba amma naga kuna tafiya tare tana jiranka anan..."
fita yayi da gudu yake driving zuwa gida, manal dake tsaye a gaban mirror ta kira wayan megadi tace "well done ka tsira da ranka"
kashe wayan tayi yabi da kallo, a kofan gida yayi parking yaga basa nan, juya motan yayi zai tafi gidansu ameesha yaji makocinsu yace "Abdulrahman"
tsayawa yayi yace "mutanen gidanku naga sun tafi asibiti da mamanka"
ido waje yace "yaushe?"
yace "da jimawa kuma naji sunce wa me napep city hospital zai kaisu"
da sauri yace "na gode"
tada motan yayi da gudu ya bar kofansu kamar zai kife da motan haka yake driving, city hospital yaje yayi parking da sauri ya fito ya fara nemansu, saida ya samu dr yace "ina neman waɗanda aka kawo yau?"
yace "ai sunada yawa wanne daga ciki?"
yace "babbar mata da yaro karami da kuma wani ɗan babba sai yarinya budurwa..."
da sauri yace "Ameesha sunanta?"
yace "eh su"
yace "okay ga can ɗakinsu"
da sauri da gudu yaje, knocking yayi kafin ya tura kofan ya shiga, tsayawa yayi a bakin kofa yana kallon umma dake bacci hanunta ɗaure da drip duk da akwai fanka amma ameesha tana fifita ta, jiki a mace ya fara takowa har zuwa wajenta, hanu yasa ya taɓata yace "umma"
ameesha ɗauke kai tayi daga kallonshi, da sauri ya kalli ameesha yace "me yasa baki gayamin ba kika tafi?"
idanunta da suka rikiɗe suka koma jajur ta kalleshi dasu, batayi magana ba yace "ba magana nake miki ba?"
murmushin da yafi kuka ciwo tayi sannan ta tashi tana gyarawa umma drip ɗin, fita zatayi ya rike hanunta, tace "sakarmin hannu"
yace "ba zan sake ba saikin faɗamin meyasa baki fadamin ba kika tafi?"
juyowa tayi tazo har gabanshi ta tsaya, cikin idonshi ta kalla sannan s fusace tace "ban faɗa maka ba? kana can kana meeting shine zan faɗa maka? kana can kana zuwa gidansu manal kana yin late shine zaka samu daman zuwa wani waje me amfani...."
cikin tsawa yace "shout up meesha, kina bibiyana kina zargina ne kenan?"
tace "ba bibiyanka nake ba"
yace "bibiyana kike mana baki yadda dani ba"
Imran yace "yaya, meesha dan Allah kuyi hakuri karku fara haka"
share hawaye tayi tace "yaushe zanje ina bibiyan wanda yake bibiyan wata"
cikin zafin rai ya juyo da ita yace "meesha ban bibiyi kowa ba kisan me zaki faɗi"
"shiyasa aka baka manager?"
cikin tsawa yace "ban karɓa saboda so na ba"
tace "bakaso shiyasa ka karɓi kayan babanta kasa?"
cikin zafin rai ya nunata da yatsa yace "meesha ki iya bakinki"
itama ranta yana tafasa tace "idan naki fa? zaka dakeni ne?"
dunƙule hanu yayi ta matso tana hawaye tace "dakeni mana, dakeni Man"
hanunshi daya dunkule ta warware hanun ta fara marin fuskanta dashi tace "da dukan kayimin zanfi jin sauki akan naje kiranka kazo umma babu lafiya kace bakada lokaci"
a fusace cikin tsawan da yasa umma ta gama buɗe idonta jin abinda yake faruwa kamar a mafarki yace "karya kike yi"
ba ita kaɗai ba har Anty dasu fahad saida suka kalleshi, a fusace ta fita daga ɗakin ta turo kofan gauu, umma tace "me nakeji haka man? wa kake yiwa tsawa?"
shiru yayi tace "wa kake yiwa tsawa nace?"
baiyi magana ba tace "in dai ameesha ce kasan ba zan karɓa ba ko? wannan yarinyar data shigo rayuwarku itace takeso ta fara haɗaku faɗa?"
yace "ammi babu fa ruwan manal a wannan faɗan...."
cikin tsawa tace "ka rufemin baki, nifa dama kallo ɗaya na yiwa yarinyar naji na tsaneta, to tun wuri ka san abinyi ko ka aje aikin ka fita a harkan yarinyar ko kuma kasan yadda zaka rinƙa lallaɓa ameesha ta yadda ranta ba zai rinka ɓaci ba"
shiru yayi tace "jeka bata hakuri"
a hankali ya juya ya fita, tana zaune a waje ta haɗa kai da gwiwa tayi shiru, a gefenta ya zauna ya jingina kanshi da bango yayi shiru shima, sun jima a haka kafin yace "am sorry"
bata ɗago kai ba tace "ba komai bazan iya fushi da kai ba, amma inaso ka faɗamin gaskiya"
hanunta ya rike ya fara irga mata duk abinda ya faru, a hankali ta share idonta tace "na sani zuciyata tana faɗamin gaskiya dannewa nake, nasan ba zakayi komai babu dalili ba"
yace "ki yafemin"
a hankali tace "na yafe maka"
yace "you are the best friend a wannan duniyan"
shiru tayi, saide zuciyanta yana zafi kawai dannewa take sabida ga umma babu lafiya kada abin yayi mishi yawa, da haka suka zauna har dare.
washe gari ameesha ce ta tafi gida tayi musu breakfast tazo dashi, tun daga nesa taga motar da take ganin manal a ciki, fitowa tayi daga napep tana rike da flasks ta shiga cikin ɗakin, tsayawa tayi turus ganin manal zaune a kan kujera tana yiwa umma sannu, umma amsawa kawai tayi ta rufe ido kamar me bacci, a hankali ta karasa ciki ta aje flaks ɗin tace "fahad ina man?"
manal cikin murmushin da take mata tace "yaje karɓo magani"
shiru tayi, manal ta kalli umma wacce take ɗauke kai tace "to umma zan tafi Allah ya kara sauki"
umma tace "ameen"
shigowa yayi yace "meesha har kinzo?"
tace "yes"
manal tace "rakani zan tafi"
aje maganin yayi ya rakata, baiji daɗi ba da yaga babu wanda yayi farin ciki da ganinta, ita kanta manal zuciyanta tafasa yake ganin umma sai ɗauke kai take, a hankali tace "family ɗinka basa farin cikin ganina"
yace "no ba haka bane kinsan a asibiti ne kowa baya yanayi me daɗi"
tace "to shikenan tunda kai kana farin ciki idan ka ganni hakan yasa nake jin dadi a raina"
tausayi ta bashi, ta shiga motan yace "kinashan maganinki?"
a hankali tace "eh"
yace "kada kiyi wasa da magani kinji?"
a hankali tace "to"
tafiya tayi yana ɗaga mata hanu, komawa ciki yayi ameesha tana zaune a gefen umma tana cin Irish, zama yayi kusa da ita yasa hanu suka fara ci tare, danne damuwanta tayi ta taɓa gashinshi daya taru tace "yau gashinka yayi yawa sosai"
yace "eh kitso nakeso kimin"
dariya tayi tace "waye zaiwa namiji kitso? wannan gashin naka da uban laushin ina zai kamu"
yace "ai bai kai naki laushi ba"
tace "karya ne"
zame hulan kanta yayi zai taɓa gashinta ta kauce tace "karka taɓamin kai"
ganin haka ya tashi ya zame ribbon ɗin kanta, girgiza kai take tana matsawa nan take gashin ya baraje ya rufe mata fuska saida ya taɓa, ɓata rai tayi tace "nika bayamin gashina umma tamin parking me kyau ka warware"
yace "to kawo na kame miki"
kame mata yayi sukaci gaba da surutu umma dake kwance sai kallonsu take a ranta tace "Allah ka karesu daga kowane sharri"
*Jiddah Ce...*
08144818849
managarciya