DUHU DA HASKE: Fita Ta 11

DUHU DA HASKE: Fita Ta 11


DUHU DA HASKE


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 11*


                 ~Ameesha itama kwanciya tayi akan gado bayan tasa kayan bacci, juyi take akan gadon tana kallon wayarta ko zai kira, a hankali ta lumshe ido ganin bai kira ba, da kyar ta samu bacci ya ɗauketa, sai washe gari ta shirya taji yana hon a kofar gidansu, fitowa tayi tareda fahad ta zauna a gaba tace "good morning"
cikin son ganin ta kalleshi yace "morning princess ya kika tashi?"
a hankali tace "lafiya ƙalau"
Imran yace "good morning"
tace "ya kake"
tafiya suka fara fahad ya gaishesu, a school ya ajesu fahad sannan suka tafi, a hankali tace "akwai maganan da nakeso muyi"
yace "okay"
tace "dama inaso na faɗa maka wani abu"
yace "okay menene abin"
tana wasa da yatsunta ta rasa ta inda zata fara tace "man ina s..."
wayarshi aka kira ya ɗauka, gani yayi sunan boss yana yawo da sauri ya ɗauka yace "good morning boss"
muryanta kasa tace "ya kake?"
yace "ina lafiya ya jiki"
"da sauki yau ba zanje aiki ba inaso ka kula da komai na company duk wani abinda kasan inayi to kayi yau ko ɗaya banson ayi ɓarna ko wani abinda ba daidai ba"
da sauri yace "okay madam"
kashe wayan yayi ya kalli ameesha ya mata signal tareda cewa "guess what?"
girgiza kai tayi ya mika mata hanu suka tafa yace "yau madam ba zata zo wajen aiki na tace ta bar komai a hanuna zamu tafe tare dake yau tare zamuyi aiki saiki tayani ko?"
gyaɗa kai tayi tana murmushi tace "to ya zanyi da ɗan lukutin wajen akinmu?"
yace "zanji dashi"
a kofan wajen aikinsu ya tsaya yace ta ɓuya a motan, ɓuya tayi ta ya shiga yayi fuskan tausayi ya gaishe da mutumin da yake ta hararanshi, mutumin ya amsa yace "yau ameesha ba zata samu zuwa wajen aiki ba cikinta kanta kafanta na ciwo sai gobe zata zo, bayan wannan sai me zaka kara akan maganan da zakayi?"
shiru yayi jin mutumin ya faɗi duk abinda zai faɗa, a hankali yace "eh sai gobe zata zo"
tsaki yaja yace "kullum magana ɗaya kaima kamar ita kake baku girma kamar yara fitamin da gani"
da sauri ya fita ya koma motan yace "muje muje"
saida sukayi nisa ta ɗago kai tace "ya yadda?"
gyaɗa kai yayi yace "yes"
har cikin company ya shiga da ita suka fita ya rike hanunta da jakanta data rataya, tayi kyau cikin riga da wando kamar kullum palazoo da top sai hula me faɗi akanta da takalmi canvas, shiga yayi duk masu aikin suka zuba mishi ido yace "yau kun san me?"
sukace "no"
yace "madam ba zata zo ba zamuyi shagalin birthday ɗin Ameesha ta cika shekara 21"
murna suka fara da shike duk sun san ameesha kullum tana zuwa kofan jiranshi kuma tare suka fara ganinsu, ameesha cikin murna tasa hanu a baki ta manta yau birthday ɗinta, yaje frij na manal ya kwaso musu sauran drinks ɗin ya fita ya siyo musu snacks dasu cake da yayi order tun a gida a rubuta happy birthday meesha, yazo ya fara haɗa musu party da taimakon ameesha, akan kujeranshi ya zaunar da ita yace "kema gobe zaki zo neman aiki anan kuma zaki samu by god grace kullum saiya zama muna tare"
murmushi tayi tace "to bani jakan na rike domin takadduna suna ciki"
bata yayi ta rataya, 
shagali suke yi sun maida company yau kamar wajen party.

kwance take akan gado tayi shiru cikin blanket, ba wani rashin lafiya take ba amma tana jin jikinta so weak, a hankali ta yaye bargon ta tashi domin shiga toilet, rigan bacci daidai gwiwa ne a jikinta fari sal, gashinta tayi kitso biyu yayi kyau sosai, tasa hanu akan handle ɗin sai kuma ta tsaya, ji tayi tanason ganin yadda suke gudanar da aiki a company, komawa tayi bakin gado ta janyo laptop ta ɗaura akan cinyarta, buɗewa tayi ta shiga vootage ɗin data saita da cctv dake company, zaro ido tayi ganin Abdool yana yanka cake da wannan yarinyar a cikin company ɗinta, ɗauko cake ɗin yayi yasa mata a baki tana dariya ta rike hanunshi tana ci, sauran suna tafi suna mata waƙan happy birthday to you, murnan da yake kan face nata zai nuna maka yadda taji daɗin birthday da Abdool ya haɗa mata wannan shi ake kira surprise, fita yayi daga wajen ita kuma tana bawa kowa cake a baki tana murmushinta me kyau, shigowa yayi da manyan kwalaye ya durkusa kasa a gabanta yace "your birthday gift"
karɓa tayi ta buɗe ganin sabon waya babba me kyau da kuma sabon agogo da takalmi snicker ta aje a gefe ta durkusa a kasa itama ta rungumeshi, murmushi yayi yana kallon bayanta ganin sun fara zama too emotional faruk yace "let's continue with the party"
tashi sukayi suka fara shagali.

manal huci take yi tana kallonshi ya ɗau crown me kyau a cikin ɗayan kwalin golding ya sawa Ameesha, dariya take yi sosai tana jin daɗi tace "thank y..."
rufe mata baki yayi yace "kin manta? babu godiya tsakaninmu" 
tana huci da sauri ta tashi ta cire rigan jikinta tasa dogon riga bata tsaya yin komai ba ta yafa mayafi kawai tasa dogon takalmi domin bata iya tafiya da flat shoe, fita tayi daga gidan a fusace ammi tana kiranta ko kallonta batayi ba, gateman yana ganin haka ya buɗe mata gate, sharara gudu ta fara tana huci kamar ta tashi a iska, da wani irin gudu ta shiga company tayi parking wani dake aiki a waje ya shiga da gudu yace musu ga madam tazo, man da ameesha suka fara tattara wajen cikin sauri da taimakon sauran mutanen suka tattara, hanun meesha ya rike ya ɓoye kwakayen ya zaunar da ita a kujeran masu neman aiki ta rungume jakanta saide bata cire crown ɗin ba, da sauri ya koma wajen zamanshi ya fara latsa laptop, kowa yana kallon laptop kamar ba abinda sukayi, karan takalminta sukaji babu wanda ya ɗago, a bakin kofa ta tsaya tana kare musu kallo, da mamakinta taga sun gyara ko ina sun nutsu, wani kallo ta aikawa ameesha take taji cikinta ya ɗibi ruwa, kallon Abdool tayi tace sannan ta kara kallon sauran tayi gyaran murya, duk suka tashi suna mata sannu da zuwa da gaisuwa, bata amsa ba ta shiga office ta nuna batasan komai ba, tana shiga ta aika a kira masu neman aiki, saida mutane biyu suka shiga kafin akazo kan ameesha, a tsorace ta kalli abdool yayi mata alaman taje kada taji tsoro, jijjiga kai tayi a hankali ta fara tafiya ta rike takaddunta gam, ta cikin computer take kallon duk abinda sukeyi har zuwa lokacin data fara knocking, bata amsa da wuri ba saida ta jima a wajen tana knocking kafin tace "yes"
juya baya tayi akan kujeran har ameesha ta shigo ta zauna tace "sannu madam gani"
juyowa tayi a hankali tana kallonta daga kasa har zuwa sama, takaddan data rungume ta kalla sannan tace "suna"
da sauri tace "Ameesha"
tace "bakida baba ne?"
da sauri tace "Ameesha Ibrahim"
tace "matakin karatu"
tace "secondary"
kara kallonta tayi a wulaƙance sannan ta jijjiga kai a hankali, tace "me kika karanta?"
da sauri tace "Art"
hanu ta mika tace "takaddu"
mika mata tayi da sauri cikin girmamawa, karɓa tayi tana kallo a hankali, ta jima kafin ta ɗago kai, tashi tayi tazo gabanta, tana kallon cikin idonta tace "takaddunki yayi kyau amma kin san me zaisa ba zan ɗaukeki aiki ba?"
girgiza kai tayi, murmushin gefen baki tayi tace "sabida gaba ɗaya bakiyi kama da mata ba, kinfi kama da maza domin kullum cikin dressing nasu kike kuma kina tare dasu, meyasa ba zakiyi rayuwarki ke kaɗai ba saikin shiga harkan maza?"
shiru tayi, gani tayi ta matso da takaddun daidai fuskanta, zaro manya manyan idanunta tayi ganin ta yaga takaddun tayi pieces dasu ta watsa mata a fuska tace "fita ba zan ɗaukeki aiki ba"
idanunta cike da hawaye tabi takaddun da kallo, cire crown ɗin kanta tayi tace "sam baki dace da wannan crown ɗinba, bakya kama da sarauniya kinfi kama da ɓarauniya me sata abin company tayi birthday dashi"
kallonta tayi zuwa yanzu hawaye sun gama wanke mata fuska har zuwa gaban riganta, karɓan crown ɗin tayi ta maida kanta cikin hawaye tace "ban damu ba dan duniya sunce banyi kama da sarauniya ba, na yadda ni middle class ce, tunda Abokina ya bani sarautar na karɓa hanu bibbiyu nasan ya tsallaka mata high class dayawa ya bani sarautar sabida a wajenshi na fisu"
durkusawa tayi kasa ta kwashe takaddun data yayyaga cikin kuka ta fita, tana ganin Abdool ta share hawayen tana kakalo murmushi ta ɗaga mishi hanu tace "saika dawo na tafi"
da sauri ya tashi yaje gabanta ya tsaya ganin tana sunkuyar da kai ya ɗago fuskanta yana kallonta baice komai ba, da sauri ta kawar da kai tana maida hawaye tace "bari naje"
rike hanunta yayi ya kalli takaddun da suke a yage yace "me tayi miki?"
da sauri tace "ba kom..."
kuka ne yaci karfinta ta zare hanunta ta fita da gudu, binta yayi da kallo yana ganin tana share hawaye tana gudu, cikin zafin nama ya nufi office na manal babu ko knocking da kafa ya hankaɗa kofan ya shiga, turawa yayi gau, a firgice ta ɗago kai daga zaunen da take akan kujeranta me juyawa ta kalleshi, gabanta ya faɗi ganin wani irin kallo da yake aika mata sannan yana nufota gadan gadan cikin tsananin ɓacin ran da tunda ya fara aiki anan bata taɓa ganin koda rabinshi a tare dashi ba, cikin in ina tace "me..me..ya faru?"
akan kujeran da take ya dira hannayenshi duka biyu ya sata a tsakiya fuskanshi kusa da nata sosai, idanunshi sunyi jajur alaman yana cikin ɓacin rai, cikin kakkausan murya yace "me kike tambaya? me?"
a tsawace yayi maganan, zatayi magana ya nunata da yatsa ya girgiza ta akan kujeran a firgice tasa hanu biyu ta rike hanun kujeran tana kallonshi da dara daran idanunta, yace "kin san waye kika taɓa kin san ita ɗin wacece a rayuwata? me kika gaya mata!!!!?"
a tsorace tace "ban..ban..."
ya daka mata tsawan da yasa jikinta ya fara rawa yace "kin san wacece ita? akanta zan iya barin aikina koda biliyan ɗaya nake karɓa a kowane sati, kuskuren da zaki tafka a rayuwa shine ki kara taɓa ameesha a ranan zan nuna miki ke karamar ƴar iska ce, kin san wahalan da tasha kafin ta samu takaddunta?"
ya kara girgiza kujeran kamar zai kifar da ita, yace "kin sani?"
watsi yayi da kayan dake gaban table nata,
batayi magana ba ya riko hanunta da mugun karfi yace "kin sani?"
kara tayi cikin jin zafi tace "ash abdool ka sakeni da zafi"
yace "ki bani amsa"
girgiza kai tayi tace "A,a"
sakinta yayi yace "ba zaki sani ba sabida baki taso cikin wahala ba kin taso cikin wulaƙanta mutane kina ganin hakan shine jin daɗi, to bari na gaya miki wani magana idan baki sani ba, Ameesha macece da ko namiji ba zai iya jarumtar da tayi ba a cikin rayuwar family ɗinta da kuma nawa, da ni kika kira kika yayyaga takadduna kika min duk wulaƙancin da kikaga dama zan ɗauka amma banda Ameesha tafi ƙarfin wannan matukar ina wajen, kin fahimta?"
a tsorace jikinta yana rawa tace "eh"
sakin kujeran yayi ya fita daga office ɗin ya rufe kofan "gauuuu"
toshe kunne tayi domin kamar zai ɓalla kofan, a tsorace ta kalli kofan lokacin daya fita, da sauri taje ta ɗauko ruwan sanyi a frij tazo ta zauna tasha, rufe ido tayi tana sauke ajiyan zuciya kamar wacce tayi gudun minti talatin.

yana fita ya shiga motarshi yabi bayanta, har ta shiga napep ta tafi gida, duk wani gift daya siya mata saida ya ɗauko mata, gidansu yaje yayi sallama ya shiga, anty dake zaune akan sallaya taga ameesha ta shigo da gudu tana kuka sai kuma ga man, tana gani ya wuce da kwali baiyi magana ba, ɗakinta ya shiga ya kalleta ta kwanta tana kuka akan gado, zuwa yayi ya zauna kusa da ita, jin kukan yana yawa yace "idan kinaso zuciyata ta buga kici gaba da wannan kukan"
a hankali ta tashi ta share hawayen, murmushi tayi tace "raina bai ɓaci ba kawai de ina kuka ne"
rungumeta yayi domin tanada son ɓoye damuwa bada garaje take bari asan tana cikin damuwa ba, yace "karki damu ba zan kara kiranki inda za'a wulaƙantaki ba nima na aje aikin"
da sauri ta janye tace "ka aje aiki kuma? sabida me?"
ganin hankalinta ya tashi yace "bance na aje ba so nake na kwantar miki da hankali kiyi hakuri haka boss namu take muma hakuri muke da ita"
karɓan kwalin hanunshi tayi tace "gaskiya na tsorata na zaci zata kamamu muna shagali fa Allah ne ya taimakemu"
yace "hmm dako saita samu tsallen kwaɗo mu duka harda ke"
dariya tayi tace "zan gudu na barka"
sauka yayi yana ɗaga kafanta ya ɗaura akan cinyarshi yana sa mata takalmin, ganin ya mata daidai kuma ya mata kyau yace "wow ya kika gani?"
tace "gobe dashi zanje aiki"
yace "nima zan siya kalanshi muyi anko"
hanu ta mika mishi suka tafa, hira suka fara kamar ba abinda ya faru, manal da kyar ta saisaita kanta ta koma gida, koda taje ɗaki ta shiga bata yiwa ammi magana ba, toshe kunne tayi tana tuna tsawan da yayi mata, a ranan da kyar ta samu bacci, washe gari man daya kai ameesha wajen aiki komawa yayi gida baije aiki ba, manal da tazo bata ganshi ba sai taji jikinta yayi sanyi, wasa wasa har kwana biyar baizo aiki ba, ameesha idan an tashi saide ta ganshi a kofa yana jiranta yace mata yana tashi da wuri yanzu, ya hana kowa faɗa mata baya zuwa aiki, manal wacce take zaune akan kujeranta tana juyi hanunta ta dafa kai tana kallon pop ɗin saman ɗakin, idonta akan computer tana kallon duk masu aikin kujeranshi take kallo yau sati ɗaya kenan baizo ba, sai taji company ɗin yayi shiru babu wani abin cigaba ko walwala, duk da bata saba walwala ba amma taji wani kala, cikin sanyin jiki ta koma gida, da dare sai juyi take akan gado kusa da Ammi bacci yaki ɗaukanta, cikin juyin da yafi sau a irga ta rungume ammi tayi shiru kamar me bacci, Ammi wacce rabonta da samun isasshen bacci tun mutuwan Dady tace "manal?"
cikin sanyinta tace "na'am"
ammi tace "me yake damunki a cikin kwanakinnan bakya bacci?"
shiru tayi kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace "ammi meyasa ake damuwa da mutum idan ba'a ganshi ba?"
tace "so"
shiru tayi, smmi ta kunna wutan ta juyo ta kalleta tace "soyayya ne zaisa ki kasa bacci akan wani, idan kuma baki yadda ba ki gwada zuwa ki ganshi koda sau ɗaya ne, idan kinji farin ciki kinyi bacci to kin kamu da so"
a hankali ta rufe ido bata amsa mata ba, murmushi kawai Ammi tayi dan ta lura tana yawan tunani, washe gari tasa dogon riga dubai ta yafa mayafi siriri sannan tasa glass a idonta tasa dogon takalmi, ammi tace "ga breakfast"
girgiza kai tayi tace "banjin yunwa"
fita tayi bata jira taji me zata ce ba, cikin class take tafiya harta buɗe mota ta shiga, fita tayi ta nufi company ta kalli wajen zamanshi yauma baizo ba, shiga ciki tayi ta dafa kanta, waya aka kira na company ta ɗauka ta kara a kunne, cikin sanyin muryanta tace "yes nice"
shiru tayi tana sauraran abinda ake cewa, sannan tace "okay deal"
aje wayan tayi ta buga jikin table na gabanta tace "ta ina zan fara nemanka? gashi ana buƙatan zane kala ɗari biyu"
dafa kai tayi kamar tayi kuka sai wani tunani ya faɗo mata, da sauri ta kira numbern faruk tace "shigo"
bs jimawa ya shigo yace "gani madam"
cikin rashin fara'anta tace "kasan gidansu Abdool?"
yace "eh na sani"
ta bashi takadda da biro tace "rubutamin address"
rubuta mata yayi sannan yace "sune a farko"
ta karɓi tskaddan kawai ta tashi, tsintsan kanta tayi da gyara fuskanta a madubi sai kuma ta fesa turare tayi murmushi, fita tayi tana kaɗa makullin mota a hanu har ta shiga, fita tayi tana driving cikin kwarewa tana duba address ɗin.

Ameesha ta kalli agogo yau an tashi musu da wuri tace "ya zanyi da man? ko dai zanje na sameshi nace yau shi kaɗai zai tafi nikam na wuce ne?"
sai kuma tace "gaskiya gara naje"
sauri ta fara akan titi ta saba da tafiyan sauri bata damuwa har taje company ta shiga ciki domin nemanshi, wani ta samu tace "please ina neman Abdool"
yace "Abdul ai yayi sati baya zuwa aiki"
tace "amma kasan wani abdool nake nema?"
hotonshi ta nuna mishi tace "wannan fa"
yace "na sani mana yayi sati baya zuwa aiki tun ranan da akayi birthday ɗinki anan bai kara zuwa ba"
da sauri tace "na gode"
fita tayi ta kira wayanshi ya ɗauka cikin nauyin bacci yace "darling"
a hankali tace "meyasa bakazo aiki ba?"
yace "banda lafiya"
kafin tayi magana ya kashe wayan, napep ta shiga zuwa gidansu.

manal cikin kankanin lokaci ta isa gidan da aka tabbatar mata shine nasu, kallon gidan tayi na talakawa ne a hankali tayi knocking, ba'a buɗe ba, ta kara yin knocking, Imran dake kwance cikin busy ɗin falonsu ya ɗaura kai a ƙafan umma yana karatu yaji ana knocking kallon umma yayi yace "nasan ba Ameesha bace dan tana wajen aiki"
umma tace "to jeka duba mana"
tashi yayi, gajeren wando ne a jikinshi ya buɗe kofan, manal ce tsaye tana ganinshi tayi mishi murmushi, waro ido yayi cike da mamaki yake kallonta, umma dake ɗinka safan sanyi wa ameesha tace "imran waye ne?"
baiyi magana ba ta tashi zuwa wajen domin ganin ko waye, ido huɗu sukayi da manal wacce take tsaye tana murmushi, a hankali tace "sannu da zuwa"
cikin murmushi tace "yawwa"
ganin sun tsaya basu bata hanya ba kuma basu ce ta shigo ba Imran sai leƙa abdool yake, tace "zan iya shigowa?"
a hankali umma ta matsa mata, Abdool daya tashi a bacci yanzu ya ɗau brush ya fito dashi a bakinshi, wando three quarter da riga armless a jikinshi, gashinshi kamar na mace ya barbaza sabida bacci, idonshi a lumshe yace "Imran waye yazo?"
Imran ya juyo yana mishi alama ya tattara ɗakin kafin ta shigo, waro ido yayi ganinta a tsaye bakin kofa tana murmushin da yake kara mata kyau sosai, da sauri ya juya ganin wandon dake jikinshi ya koma ciki domin sa jallabiya, umma tace "shigo"
ƙafan hagu tasa zata shiga sai kuma sukaga ta koma da baya tasa ƙafan dama tace "salam"
umma ta nuna mata wajen zama tace "zauna"
a hankali ta zauna tayi shiru tana kallon Imran dake tattare kayan ɗakin, da gani kanin abdool ne domin suna kama sosai,
umma ta kawo mata ruwa tace "ga ruwa"
karɓa tayi tasha sannan tace "na gode"
ajewa tayi tace "ina wuni"
umma tace "lafiya amma saide ban ganeki ba"
a hankali tace "sunana manal daga wajen aikin Abdoool"
tace "laaaa kece? dan Allah kiyi hakuri bari na kawo miki abinci"
shiru tayi umma ta shiga kitchen tareda Imran ta zuba mata shinkafa da waken data dafa tun na safe Abdool baici ba, Imran ne ya kawo mata lokacin abdool ya fito daga ɗaki sanye da jallabiya brown, yayi kyau sosai musamman da gashinshi ke harharɗe, a nesa da ita ya zauna yace "sannu da zuwa"
tace "kayi mamakin zuwana ko?"
yace "eh"
kallonshi tayi sai taji duk wani damuwan da take ciki ya kau, tace "nazo na baka hakuri akan abinda ya faru kuma ina rokonka ka dawo aiki"
yace "bani zaki bawa hakuri ba wacce kika yiwa zaki bawa hakuri"
zatayi magana ameesha ta ɗaga murya tun daga bakin kofa ta fara ƙwala mishi kira "maaaaaaaan maaaaan ina kake? yau saika......"
turus ta tsaya a bakin kofa ganin manal ta sauko kasa wajen abincin ta fara zubawa, ɗago manyan idanunta tayi tace "Imran zan samu tumatir da attarugu?"
Imran yace "eh"
da sauri yaje kitchen ya ɗauko mata tumatir da attarugu ya aje mata da karamin wuƙa, murmushi tayi tace "thanks"
wani kallo ta aikawa ameesha tace "shigo mana ko bakiyi farin cikin zuwana bane?"
a hankali ta shigo ta zauna kusa da man, kafin tayi magana manal ta kalli man tace "zan samu ruwa?"
gyaɗa kai yayi ya tashi domin kawo mata ruwa, umma da Imran sun tafi ɗaki domin bata waje taci abinci, a hankali ta ɗauki wuƙan ta fara caccakawa akan attaruhun kanta a kasa, a tsorace Ameesha take kallonta, ɗago ido tayi ta ɗau Attaruhun ta fara ci, babu ko alaman jin zafi a tare da ita saide idonta yayi jajur tana kallon ameesha dasu, cikin tsoro ameesha take waro ido, saida ta cinye duk attaruhun batasa komai a bakinta ba, Abdool yazo da ruwan ya mika mata, karɓa tayi da mugun mamaki ameesha take kallonta ganin ta aje ruwan bata sha ba, cikin kakkausan murya da jajayen idanunta tace "kiyi hakuri"
ameesha a tsorace ta kalli man zata tashi yace "tana baki hakuri"
manal ta dunkule hanu da karamin wuƙan a hanunta tace "kiyi hakuri da abinda ya faru"
gani ameesha tayi hanunta yana jini, a firgice tace "hanunki?"
ɗaga mata ɗayan hanun tayi tace "ina baki hakuri ki maida hankali akan hakurin ba jikina ba"
man bai kula da abinda take yiba, ameesha tace "ba komai ya wuce"
tashi tayi tana murmushi ta ɓoye hanunta dan kada yaga jinin tace "na gode zan tafi office amma zaka dawo bakin aiki?"
murmushi yayi ganin ta bawa ameesha hakuri yace "yanzu ma zan tafi ki jirani zan fito"
a hankali tace "ina mota"
shiga ɗaki yayi ita kuma ta kalli ameesha kallon dako ita bata san name bane, sannan tayi murmushin gefen baki ta kalli umma data fito yanzu ta ciro kuɗi daga aljihunta na rigan, dubu ɗaɗɗaya ne sabbi dal bunch biyu ta aje a kusa da umma tace "to umma ga wannan ba yawa, na gode na tafi"
umma tace "a,a bamason haka dan Allah kada kiyi haka"
murmushi kawai ta fita bata jira umma ta karasa maganan ba, a hankali tace "mun gode"
 ficew tayi daga ɗakin, motarta ta shiga ta ɗauko ruwan dake cikin gora cikin azaban da harshenta yake ta fito dashi waje ta fara zuba ruwan, babu sanyi ta kama gefen riganta tana gogewa wasu zafafan hawayen azaba suna zubowa.

Ameesha ganin ta fita kalli kuɗin sannan ta kalli umma wacce itama take kallon kuɗin da mamaki, bin man tayi da gudu zuwa ɗaki, ya cire jallabiyan yana shirin sa kaya me kyau ameesha tace "man wannan matar fa hankalina baya kwanciya da ita kamar fa muguwa ce da wuya idan tanada imani...."
sa rigan yayi ya rufe mata baki yace "koma menene tunda ta sauke kai tazo har gida ta baki hakuri ai shikenan saimu kalli kirkin da tayi mu zubar da rashin kirkinta ko?"
girgiza kai tayi ya cire hanunshi a bakinta yana sa takalmi tareda ɗaukan wayarshi tace "ba hakurin zaka duba ba abinda yasa ta bada hakurin zaka...."
yace "kai princess kada ki zama me korafi mana ban sanki dashi ba"
zatayi magana yace "na tafi"
fita yayi ta bishi har waje tana kokarin fahimtar dashi har ya buɗe motan ya shiga, kallo manal ta bita dashi sannan tayi mata murmushin gefen baki ta kuma haɗa fuska taja motan suka tafi, ameesha cikin damuwa da jin haushin man da ya kasa fahimta ta juya zata tafi Imran yace "nima hankalina bai kwanta da ita ba"
da sauri tace "kaima ka gani ko? kaga me na gani a tare da ita? amma shi man ya kasa ganewa"
yace "ba komai bata isa tayi komai ba sai abinda Allah yayi"
tace "hakane amma mu kare kafin wani abin ya faru"
yace "addu'a"
tace "ys gama komai"
tafa hanu sukayi yadda suka saba.

a mota yaga tayi shiru yace "ya jikinki?"
a hankali tace "ba sauki"
yace "me yasa?"
tace "aini kullum cikin rashin lafiya nake kwana ban taɓa kwana ɗaya cikin jin daɗi ba"
shiru yayi, sannan yace "amma meyasa?"
tace "banida kowa sai ammi idan kaga na ɗaga waya to da masu aikina ko wanda nake aiki tare dasu nake magana ko kuma Ammi haka nake rayuwa babu kawa babu kowa"
kallonta yayi yaji tana bashi tausayi domin innocent face gareta bata magana sosai, yace "to kiyi kawaye mana"
tana kallon titi yana kallonta tace "ban iya ba saide idan zaka koyamin"
yace "shikenan zan koya miki domin Dr a gabana yace idan baki samun farin ciki za'a iya rasa ki"
murmushi tayi tasan hakan zai iya faruwa domin ko ita kanta tana jin hakan a ranta, tace "amma da sharaɗi"
gyara zama yayi yace "ina jinki"
tace "da kai kaɗai zanyi abota sannan duk wani damuwata zan rinƙa faɗa maka, kuma zanso nima na fara yin waya kamar kowa naji yadda akeji nima inaso nayi dariya a rayuwata banson zama irin na gidanmu da nakeyi kullum cikin ɗacin rai"
yana iya hango damuwa a tare da ita, a hankali yace "na amince"
badan komai ba sai dan ya ceto rayuwarta daga shiga matsala.
murmushi tayi ta mika mishi hanu irin na yara a tv idan zasuyi alkawari haka taga sunayi tace "promise"
yasa hanun a nata ya sarke sannan yace "promise"
a takaice tayi murmushi tace "thanks"
daga nan har suka isa company bata kara cewa komai ba, rashin magana a jininta yake, koda suka fito fuskanta kamar kullum ta mayar kamar bada ita suka gama hira ba, kallonta yayi yace "idan kina dariya kinfi kyau"
murmushi tayi tace "ban saba ba kullum haka ammi take cewa"
a tare suka shiga ciki suna ganinta suka tashi tayi musu alama su koma su zauna, office ta wuce man kuma yayi musu gaisuwa sannan ya zauna a mazauninshi yana buɗe laptop ɗinshi daya jima be buɗe ba, zama tayi akan kujera tana kallonshi ta cikin computer ko kyafta ido batayi, yau cikin farin ciki ta wuni.

*Jiddah Ce....*
08144818849