HAƊIN  ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Goma

HAƊIN  ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Goma
HAƊIN  ALLAH
 
   
 
         Page 10
 
 
 
 
Tana tsugunne ta dafe mararta, ta ji alamar tahowa inda take, don haka da sauri ta ɗago kanta, su kai ido biyu da Deeni ya watsa mata harara yace rai a ɓace, "Dilla ban makullin kafin ranki ya ɓaci don iskanci sai ki kama hanya ki tafi da makulli kamar da shi kika zo, tsabar kin raina min hankali." Yana masifar ya miƙa mata hannu alamar ta ba shi makullin. Cikin dauriya ta miƙe da nufin ta je ta buɗe mai gidan. Ai sai ya ƙara tunzura ya daka mata tsawa, "Wai uban me kike nufi ne da za ki barni tsaye a nan ina jiran ki ban makulli da wannan shegiyar tafiyar taki zan tsaye kamar wani Loho har ki je ki buɗe min ƙofa?" Jin masifar tai yawa yasa ta miƙa mai makullin tana cewa "Don Allah kai haƙuri ban lafiya ne."   Tsaki ya ja ya wuce ta yana ta balbalin masifa har mutane sun fara maido hankali kan su. Hawaye suka zubo mata sam bata damu da gogewa ba. Ya buɗe gidan ya shige ya banko ƙofar kaɗan ya hana da goshinta ya fashe, dama ga tsabar ciwon kai, a daddafe ta samu ta isa ɗakin ta zame falo tana numfashi ko hijabin bata cire ba ta kwanta hawaye na tsiyaya a idonta.  Tana kallonsa ya duƙa ya ɗauki furar da ta zo da ita ya zauna ya dama ya shanye tas ya aje kofin ya fice yana waƙa. Sam bai damu da jin damuwarta ba, babu ruwanshi da yi mata gaisuwa kawai har kar gabansa yake cike da taƙama da jin kai. Ita ta lura da wata uwar tsana ma dake kwance akan idanunsa tata duk sanda ya kalleta babu alamar sausauci a idonsa. Shin dama haka maza suke idan matansu suka kamasu da matan banza a cikin gidajensu? Ta ɗauka haƙuri suke ba matansu sannan su nuna nadama su dinga jin kunyar kallon ƙwayar idon matan nasu ai, amma shi Deeni sai abin ya zame ma shi hanyar bayyana mata munanan halayensa masu tada hankali da zautar da zuciya cike da saka shakku da razana taya zata iya wannan sabuwar rayuwa data tunkaro ta? Ga ciki ga tashin hankali, wane laifi ne ta aikata wanda ta samu kanta a wannan rayuwar? Tun tana ƙarama take fuskantar matsin rayuwa, bata san farin ciki ba sai zamanta gun Hajjo da Inna yau ga shi ba Inna, Hajjo tai rantsuwar bata sake shiga harkar ta saboda tozarcin da Baba yai mata, ga mijin Mama ya rasu tabbbas gata na ya ƙare ta ko'ina, mahaifiyata itama yanzu nasan ta kanta za tai domin bata da shi daman mijinta ne mai ƙoƙarin yin abubuwa yanzu shi ma babu shi, tabbas ta cika marainiyar gasken-gaske a yanzu. Haka ta kwanta har dare ya tsala kanta har zuwa yanzu ciwo yake ga zazzaɓin ya ƙi sauka cikinta sai ciwo yake ta rasa me ke damunta duniyar baki ɗaya ta sake juya mata baya, ko'ina ya kulle ba sauƙi. Sai da agogo ya buga ƙarfe sha biyu daidai ta ji motsin buɗe gidan, hakan ya tabbatar mata da maigidan ne ya dawo, wata uwar faɗuwar gaba ta ziyarce ta haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa sosai, tamkar ta ji motsin wani mugun abu. Fuuu! Ya wuce ta inda ya barta har da mugun tsaki ya sakar mata, ya shige abunshi ya kwanta, bai damu da jin ya jikin nata ba, tunda ta gaya mai bata lafiya. Kwana tai nishi tamkar zata mutu amma Deeni bai san abin da ke faruwa ba, barci kawai yake. Sai da asuba ta lallaɓa da ƙyar tai sallah ta sake komawa ta kwanta, lokacin yunwa ta taso mata, haiƙan, tasan bata da komai na ci don haka ta lallaɓa ɗakin ta ɗebo fulawa da nufin tai wainar fulawa, amma babu manja,don haka ta sake lallaɓawa ta koma ɗakin tai tsaye tana son tada shi, ya bata kuɗin mai don makwabta ana saidawa amma tana tsoron abin da zai faru, domin tasan ko sallar asuba bai tashi ya yi, baki ɗaya ibada bata dame shi ba, farkon auren idan tai ma shi magana sai ya yi sau biyu ya watsar, da tafiya ta miƙa idan tai maganar banza da ita yake, ko ya bar gidan,ko ya gyara keanciyarsa. Ta rasa yadda zatai,kawai idonta ya kai kan wayarsa dake caji, hannu tasa ta ɗauki wayar ta koma falo, Number Mama ta kira, cikin sa'a ta ɗaga, sallama za tai kawai ta ji an wabce wayar daga kunnenta, ya kashe wayar ya hau bala'in, "Wai ke wace irin marar tunani ce? In saka katin saboda ko naƙudar dare ta zo maki shi ne don rashin wadatar hankali za ki cinye su? To wallahi tallahi sai kin gane kin taɓa min katin waya. Na tsani irin wannan abin kai baka aje abu ba kasa hannu ka ɗauka kamar gadon gidanku. Ban da ma kin raina min hankali ki rasa wayar da za ki yi kiran sai wayata don kawai ki cinye min kati? To wallahi baki ci banza ba."   Wayar sai kira ake amma ya ƙi ɗaga kiran, ko shakka babu nasan Mama ce ke kirana, domin tasan ban lafiya, ga shi taga kirana da sassafe don haka ta biyo kiran amma Deeni ya yi mirsisi ya ƙi ɗaga mata kiran. Nan ya barni ina hawaye ya shige ɗakin ya koma ya kwanta yana ci-gaba da masifar duk ranar da na sake kira da wayarsa sai ya ban mamaki.
 
Cikina ya ci-gaba da wutsilniyar yunwa tamkar zai fasa cikin ya fito, tsabar wahala kukanma dainawa nayi na tsunna na dafe marata, ina jera Salatin Annabi. Ban yi awa ba, sai naji ana bubbuga ƙofar gidan, nasan Mama ta aiko a ga lafiya, nasan Deeni ya ji bugun amma ya ƙi fitowa daga ɗakin, haka nan ta miƙe tsaye na ji ban iya tafiyar a tsaye na duƙe na tafi a haka na buɗe gidan. Yayar mahaifiyata na gani tsaye da wata tsohuwa wadda na santa a gidansu , suka shigo sunata jera min sannu wata kan wata. Ganin yadda nake tafiya a duƙe yasa naji suna cewa "Haihuwar ce ta zo, Allah dai Yasa a rabu lafiya, ina maigidan yake ne?"  Cikin dauriya nace, "Yana kwance bai jin daɗi tun jiya shima bai barci ba."  Su duka suka haɗa baki gun furta "Ashsha! Allah Ya ba shi lafiya." Na amsa da sannu ina jin kunyar ƙaryar da nayi, haka ina addu'ar Allah Yasa kada ya ƙaryata ni gabansu. Muna shiga ɗakin suka ce na cire kayana na ɗaura zani aka ɗauko kujerata ta tsugunni aka ce na tsugunna na dafa ta gwiwawuna a ƙasa. Ni kam Allah kaɗai yasan yadda yunwa ke caccakar cikina da abin da ke cikin cikin, tabbas ko haihuwa nayi to yunwa ce silar haihuwar tawa, amma abin tambayar ta ina ma ne zan haihun? Rannan ma naji ance haihuwa zan amma ban ga ta inda zan haihun ba, Yau ma ance haihuwa har da na cire kaya na ɗaura zane na dafe kujerar tsugunne aka ce wai to ya zan na haihun? Tunani ya dinga bujoro min ƙarshe cikin halin jin jiki na dubi Yayar Mamata nace, "Inna don Allah ta ina ne zan haihun?"  Tai murmushi ita dai, sai tsohuwar ce tace, "Kwantar da hankalinki ko ma ta ina ne ai za ki gani da yardar Allah, mu dai fatanmu a rabu lafiya ai."  Shiru-shiru ba haihuwa ba labarinta har ƙarfe tara na safe, ga maigida cikin ɗaki ya ƙi fitowa sai ma tashin waƙa daya kunna daga cikin ɗakin mu ke ji, ina lura da yadda suke kallon ɗakin suna kallon juna ko ban tambaya ba nasan mamaki suke da al'ajabin abin da ke faruwa, matarka na nakuɗa amma ka kunna waƙa a waya.
 Can dai naga sun miƙe tsaye suna shirin  tafiya, "Tsohuwar tace, "Bari mu je za a aiko maki da magani tunda da saura sai ki sha da kunu ko koko kin ji?" Kaina na ɗaga masu kawai, "Yayar Mamata ta kawo Naira dubu taban tace, "In ji Innarki tace ko za a sai wani abu, to ki riƙe a gunki, kuma tana gaidaki, Allah Ya baki lafiya Ya raba lafiya, idan maigidan ya fito ai ma shi ya jikin."   Kaina na ƙasa na amsa da to. Na miƙe na raka su suka ce na barshi. 
Suna tafiya, na zari hijabina duk da jikina nata rawa, haka na ɗauki ƙaramin bokiti na je gidan koko da ƙosai na siya, tun a hanya nake zaƙular ƙosan ina ci.  Kamar wani zai ƙwace haka nai ta shan koko da ƙosan nan, sai da na shanye tas, sai na zame na kwanta ina maida numfashi. Canjin kuma na ɗora su kan ƙaramar kujera na runtse idona, saboda bugawar da kaina ke yi, ga ƙeyata na ciwo, sosai.
Goma dai-dai Deeni ya fito daga ɗakin, ina jin motsinshi zai ɗauki buta, ya fice ya ɗauraye jikinsa ya dawo ya wuce minti kaɗan ya sake fitowa ya sunkuya ya ɗauki canjin kokon da na siyo yace, "Dama na gaya maki baki ci katin banza ba, don haka na ɗauki kuɗin katina."  Ko ido ban buɗe ba, domin a tunanina iyakar kuɗin katin kawai zai ɗauka, yabar min sauran, sai na siyo manja na toya wainar fulawa (kalallaɓa) har cikin raina na jinjina lamarin Deeni daga kiran da ko sallama ba ai ba shi ne zai ɗauki Naira ɗari? Allah mai iko, ba komai, idan halina ne gobe ma na sake kira da wayar ko da yake wayarma asalinta tawa ce, mijin Mama ya kawo min ita kyauta, ya sai mana Ni da ita, shi ne daga yace na ba shi aro ta zama ta shi, ko dare ya yi idan na ɗauka in haska ya dinga masifar zan cinye mai caji kenan, hakan yasa ma na daina taɓa wayar kwata-kwata ta zama tashi.
 
Sai wajen sha biyu na rana na samu na tashi, ba laifi cikina ya daina yamutsawa amma idan nayi tafiya sai naji ƙasa na ƙara dim-dim, haka na daure na ɗebo fulawa na kwaɓa na saka hijabina na nufi inda kuɗin suke don na ɗauka na siyo manja, amma ba kuɗi ba alamar su.  "Hakan na nufin Deeni duka ya ɗauke kuɗin matsayin na katin wayar?" Rashin madafa yasa na zauna duk da hijabin zuciyata nata saƙe-saƙen yadda zan da fulawar dana kwaɓa, ga shi ina son cin abinci koma wane iri ne, ga ban da komai daman sai ita ta rage mana cikin kayan garar abincin da akai min daga gidanmu.
Ina cikin hakan naji sallamar yaran makwabtan Mamarmu, suka shigo da kwano a kai suka aje, shinkafa ƴar Hausa ce jalof in ji Mamana tace su gani ya jikin nawa?  Sai da nayi da gaske na maida hawayen idona, amma jin sun ce tace a gaida mata Deeni da jiki yasa hawayen zubowa daga idona.
 
Yanzu ace anyi min rasuwa irin wannan amma ina zaune cikin gida cike da tarin tunani kala-kala marassa daɗi da kan gado. Yaran su kai ta kallona, na kalle su nace, "Gidan nacan a cike da mutane ana zaman ta'aziyyar Baba ko? Mamarmu nacan nata kuka ko?"  Ƴar babbar ce taban amsa "Ita ai bata kuka amma tun jiya ake fama ta ci abinci ta ƙi ci, wannan ma nata ne ta kira mu zaure tace mu zo mu kawo maki mu ga ya jikinki yake kuma tace kada ki je Yau ƙi bari sai kin samu sauƙi sosai." Allah Sarki Mamana! Duk da tana cikin alhinin rashin mijinta gatanta ina cikin ranta. Tabbas uwa daban ce a rayuwa duk wanda ya rasa Uwa dole ai mai jaje.
 
Sai na ji nima na kasa cin abincin kawai kuka ya ƙwace min mai ƙarfin gaske. Ni da ita Mamana muna buƙatar mataimaki amma waye?
 
Yaran na zaune Deeni ya shigo fuska murtuk yace, "Ban ce ki je ko'ina ba, idan kuma kika je za ki sani." 
 
Yaran naga sun zare sun fice ko bankwana basu yi min ba.
 
Hankalina ya tashi kada su je su gayama Mamana abin da suka ji  suka gani, nasan tabbas zata ji ba daɗi dole wata damuwar ta sake kamata bayan wadda take cikinta na rashin mijinta.
 
Amma dole na sake takun zamana da Deeni, ba zan bari ba damuwata ta shafi mahaifiyata ko da wasa ba, nice yake aure don haka nice kawai zan dawwama a damuwarsa.
 
 
Allah Sarki! Mu je zuwa dai yanzu aka fara labarin.
 
Taku a kullum Haupha!!!