LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 13&14

5:00pm suka fito Ameenatuh tayi musu sallam tayi part ɗin su Mama bayan yake hukuncin da Umma tayi na barin gidan a daren yau zasu bar garin gaba ɗaya ta yadda duk nacin Babansu Ameenstuh ba zai ƙara ganinsu ba har abada

LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 13&14

LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 13&14

*ZAINAB SULAIMAN*
       (Autar Baba)

 



 

P13 &14

ƙanƙame Ameenatuh Umma tayi sosai tana wani irin kuka da ƙyar muryarta take fita tace"wallahi bakisa isa ki ƙetare abunda nace ba dole ki bi umarni na bazaki taba auren abokin Babanku ba wallahi" da sauri Ameenatuh ta ɗago tana kallon Umma kan a hankali kuma ta maida kallonta ga Khadija wacce kusan tare wani shock ya dirarmusu,tun kan tayi magana Khadija tace "Umma kina nufin abokin wannan mutumin ne zai auri sister?,to kuwa ya mutu ba'ayi masa biyayya ba wallahi Aunty Ameenatuh gara naga mutuwarki da naga aurenki da Alhaji sabo saboda ko ba komai zan iya jure jarabawar da Allah ya ɗora mana da na jurin ganinki matsayin matar Alhaji Sabo saboda nasan duk duniya wannan mutumin bashi da wani aboki da ya wuce Alhaji Sabo haka shima Alhaji sabo bashi da wani aboki da ya wuceshi,gara ma tun farko karma a bashi fuskar raina mutane,mai ya sa ni akanmu mai yake bamu wanda in bashi bazamu iya rayuwa ba  ni na daɗe da sanya wa kaina banida wani uba da yawuce ku ke da Umma haka kema baki da Mahaifi,Mahaifin mu ya riga da ya rasu haka Umma take cemun duk sanda na tambayeta"tsaki Ameenatuh taja a fili a zuciyarta kuwa addu'a take Allah yasa mutuwarta ita tafi zama alkairi a gareta fiye da rayuwarta,Umma kuwa kai kawai ta girgiza kan tace "dan Mahaifi Mahaifinku ne kuma biyayya ta zama dole amma duk da haka wallahi bazata auri wannan mara hankalin ba abu da na sanshi na fiku sanin Alhaji sabo duk da bansan in da kuka sanshi ba"tashi Ameenatu tayi ta ɗauro alwala ganin haka yasa duka suka tashi jiki ba kwari,


5:00pm suka fito Ameenatuh tayi musu sallam tayi part ɗin su Mama bayan yake hukuncin da Umma tayi na barin gidan a daren yau zasu bar garin gaba ɗaya ta yadda duk nacin Babansu Ameenstuh ba zai ƙara ganinsu ba har abada,

girkin dare suka fara kiciniyar ɗorawa duk da suna cikin matsananciyar damuwa amma hakan bai hanasu aikinsu ba,

a ɓangaren Ameenatuh kuwa da kyar take iyayi komai kafafunta da ƙyar suke ɗaukarta yayin da ruwan hawaye suka kasa tsagaita fitowa daga cikin idanuwanta,zuciyarta ta gaza tunanin mafita ba shiri nutsuwar ta ta bar gangar jikinta kanta ya sara zazzabi ya dirarmata,da ƙyar ta ƙarasa aikin dan ma girkin ba yawa Mama da Mijinta ne kawai da kuwa Hammad baya cin abincin dare,


Tana gamawa ta shiga daki tayi wanka ta dauro alwala dan gabatar da sallah magrib, tana idarwa ta tashi ta ƙara shan magani dan zazzabin ya sauka amma kan da saura ta zuba kayanta a a viva tana jiran lokacin tafiyarsu,

A can ɓangaren su Umma ma haka ta kasance jiki ba kwari suka gama aiki suka koma ciki suka haɗa kayansu suna jiran lokacin tafiya,


Abu Hammad da Oum Hammad kuwa sunacan suna tattaunawa akan lamarin dan sosai Oum Hammad ta girgiza da jin lamarin,


9:00pm suka fika fito domin kuwa haka suka tsara sai a ta ko wanne ɓangare an samu tseko domin kuwa Umma suna fitowa ita da Khadija sukayi kiciɓis da Abban Hammad tare da Hajiya Nana sunyi tsaye falo  kowa yayi shiru yana tunanin mafita,sallama suka musu sannan Umma tayi musu bayani kan zasu koma asalinsu duk da bata faɗi asalin nasu ba,har ta gama maganar ta bai tanka mata ba bai kuma daina kallonta ba sai dai idanunsa da suka kasance na mazan fama sai gashi yana fitar da kwalla,ba zato bare tsammani miƙewar da Umma zatayi sai ji tayi an cakumota ƙamƙam haka ya rungumeta yana fashewa da kuka kamar ba namiji ba,mamaki ne ya ƙamar da Umma,tun abun yana bata mamaki harya fara bata tsoro Khadija kuwa bakintama yaƙi rufuwa gaba ɗaya,


a can gurin Ameenatuh ma 9:00pm ta fito sai dai tan buɗe kofar sukayi karo da Mama tana kokarin shigowa"ina zakije  haka da kaya Ameenatuh?"Mama ta fada cike da mamaki ganin Ameenatu cikin shirin barin gidan "dama zamu koma garin Kakannin mu ne yanzu zanje nayi muku sallah munaso mu fita da daddare ne saboda tsaro" wani kallo ta juya tayiwa mai gidan nata kafun tace "Malama wuce ki rakani gurin Babarki"haka suka sanyata gaba tana tafe suna binta a baya kamar wacce tayi musu sata,


A falo suka nemawa kansu gurin tsayuwa kamar yadda sukaga kowa yayi sai Umma idanunta tunda suka shigo akan Maryam yake  itama hakan Umma da tun shigowar Mama ta sauke idanunta akanta kallon su Ameenatuh tayi irin kallon tuhumar nan kafin taƙara maida idanunta akan Baba ta ya saita tsayuwarsa a bayan Mama,


"Khadija ko mafarki nake ne!? Ameenatuh dan Allah kuce mun ba mafarki nake ba kamar yadda na sa ba!!"amon muryar Mama tajiyo tana faɗin "Mairamu ba mafarki kike ba Mairamu   muɗin ne dai iyayen..."ai tunkan Mama ta rufe baki Umma tayi wani kukan kuran ta dira gaban Mama tana mai rungumota sukayi baya luuu ba shiri Baba ya tarosu,


Sun jima suna rungume da juna suna gursheƙen kuka mai tsuma zuciya,su dai Ameenatuh sai suka zama ƴan kallo yayin da  idanuwansu suke ambaliyar ruwan hawaye,


gurin zama Baba ya nuna musu su duka ƴan falon anan haka Hammad ya shigo da sallama ganin iyayensa ka kakaninsa sunyi curkocurko shima sai ya samu gurin shima ya zauna kama yadda yaji kakansa yana bada umarni,

"ya isa haka Maijidda dan Allah ki tsahirtawa mutane"dagowa Umma tayi ta kalli Mahaifin nata tana murmushin yaƙe wanda akace yafi kuka ciwo kafin ta rarrafa gareshi ta riƙe kafarshi sosai ta ƙara fashewa da kuka tuni ƴaƴanta da Mahaifyarta suka mara mata baya Hajiya Nana kuwa idanuwanta ambaliyar hawaye kawai yake ba ƙaƙƙautawa Allah ya sanya mata tausayi sosai,a hankali Baba  ya janye kafafunsa daga hannun Umma yace"kinga ku nutsu banson shirme da shirita" shiru sukayi da kukan sai dai hakan bai hanasu zubda hawaye ba,


"Ah Alhamdulillah munayiwa Allah godiya da ya ni'imtamu da ganin ƴar uwata Maryama,Muhammad  wannan itace ƴar uwata da muke baka labari ni da Mama"da mamki da farin ciki Hammad yake kallon Umma Baba kuwa ya watsa masa harara,


"Alhamdulillah nayi farin ciki kuma naji daɗi,Maryama na san zuwa yanzu duniya ta biyar da ke to Alhamdulillah ko yanzu nasan kinsan ilimin rayuwa,sannan dama ni can na yafe miki kawai na barki ne duniya ta biyar da ke"Baba yayi maganar yana wani kauda kai,rasa inda Umma zata sa kanta dan farin ciki tayi ba shiri ta ɗane Baba ta rungumeshi tana kuka mai tsuma zuciya,Baba kam baima san lokacin da ya fara shafa bayanta alamun rarrashi har  tayi shiru tana lafe a ƙirjinshi,


sosai akayi hirar yaushe gamo Umma kuwa tana maƙale kusa da Abban Hammad dan ya kafa ya tsare,Ameenatuh da Khadija kuwa misalta irin farin cikin da suka shiga zaiyi wuya suna nane da kakanninsu a haka ake ta hirar,


sai 12:00am suka farga suka yiwa juna sallama Mama,Baba da kuma Hammad suka tashi dan barin part din zuwa nasu,Baba suka ga ya dakata ya juyo ya kalli Umma yayi murmushi irin nasu na manya sannan ya koma falon gaba ɗaya yace"naji Uban ƴaƴanki yazo yana buƙatar ƴarsa"Abba ne yayi karab yace"Maloho ba mara lissafi wallahi ko da uban wa..." saurin katseshi Baba yayi ta hanyar daga masa hannu sannan yace"ku tabbatar in yazo karɓar ƴarsa kun bashi abarsa banason rigima da tashin hankali,ke Maryam ai bakamata m ki ja ya ja ba tunda kinga illar rashin biyayya ki bar yarinyar tayi biyayya indai ba saɓa umarnin ubangiji bane in kuma ba haka ba zakiyi na dama lokacin da bata da amfani"yana gama faɗa ya juya suka bar part ɗin....


ayi hakuri da  wannan,

kar kuma a manta taku har kullum mai ƙaunar ku a koda yaushe AUTAR BABA CE tana sai da DATA mai in ganci ta kowanne network cikin sauki da rahusa za'a iya tuntuɓarmu ta whatsapp number mu 08129935490.