INA HUJJAR TAKE: Labarin Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Biyu

*SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)*

INA HUJJAR TAKE: Labarin Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Biyu

Nuratu Kabir Maska shi ne sunanta, mahaifinta Malam Kabir sai mahaifiyarta Salamatu suna zaune ne a cikin Maska ƙauyen Funtua jahar Katsina.

 

Malam Kabir manomi ne wanda ke noman rani da damuna, yayi aure da matarsa Salamatu tun zamanin ƙuruciya, yana noman hatsi sosai haka yana noman kayan lambu irinsu kayan miya da sauransu, hada rake (Karan sha) duk nomawa yake.

 

Yaronsu na farko Hafiz sai da yayi shekaru goma sha biyu basu sake samun haihuwa ba, har sun fidda rai sai kuma ga haihuwar ta jiyo inda Salamatu ta haifi wani yaron amma kafin suna ya koma, (rasuwa) daga nan sai Salamatu ta dinga samun ciki yana zuɓewa akai-akai.

Hakan yasa iyayenta nema mata maganin gargajiya don samun sauƙin matsalar.

 

Bayan shekara guda kuwa sai ga ciki ya bayyana jikin Salamatu wanda cikin ikon Allah ta haifi yarinya mace kyakkyawar gaske, ranar suna na zagayowa aka raɗa mata suna Nuratu sunan mahaifiyar Malam Kabir kenan, hakan yasa Salamatu ke kiranta da suna Lantai.

 

Nuratu na da shekaru biyu aka yayeta daga nan sai haihuwa ta tsaya kwata-kwata daga Yayanta Hafiz sai ita kawai.

 

Nuratu tun tana ƙarama yarinya ce mai kazarniya da ƙiriniya sosai wanda duk gidansu babu mai irin halinta.

 

Hafiz sosai yake son Nuratu don ma bata jin magana duk yadda ya kai ga kauda mata kai sai tayi abin da zai daketa .

 

Dayake Malam Kabir mutum ne mai sanyin hali kuma bai son tauye kowa, Hafiz na tasawa yace zai kai shi makarantar almajirci a Ɗanja sai Salamatu ta nuna bata son karatun nan na nesa da gida sai ya fasa, daga ƙarshe ya sashi makarantar islamiyya da boko.

 

Nuratu na tasawa rigimarta na ƙara yawa, tana da shekaru uku cif amma idan tai wata ɓarnar sai ka rantse da Allah wani ƙaton yaro ne yayi ta.

 

Suna zaune cikin aminci saƙon rashin lafiyar mahaifiyar Malam Kabir ya riske su, daya ke ita tana can wani ƙauye dake Ɗan dume mai suna Nasarawar daji, tana aure bayan mutuwar mahaifin Babansu Nuratu tayi aure can.

 

Su duka suka shirya suka nufi Nasarawar daji don gano jikin nata, sai dai suna isa suka iske mutane dafifi alamar ta amsa kiran Ubangiji.

 

Sosai mutuwar ta daki Malam Kabir domin ita kaɗai ce ta rage ma shi sai sauran dangi domin shi kaɗai ne ta haifa hakama mahaifinsa shi ne kawai ɗa gunsa har ya rasu.

 

Sai da suka shafe kwanaki takwas kana suka shirya suka juyo zuwa Maska, sai dai cikin ikon Allah kafin su kai ne motarsu tayi hatsari mutane da dama suka rasu a nan take ciki hada Malam Kabir da Salamatu, su Nuratu da sauran wasu ne aka nufi asibiti da su cikin sauri don ceto rayukansu.

 

Ko da aka kai su asibiti aka saka cigiyar ƴan'uwan waɗanda suka mutu, har Allah yasa labari ya iske Baba Kande mahaifiyar Salamatu, su ne suka je asibitin suka amshi gawarsu Salamatu suka tafi da su Hafiz domin su ba wani rauni suka samu mai muni ba.

 

Tun daga lokacin zaman Nuratu ya koma hannun Kakarta Inna Kande sai dai kuma ta taso cikin wani irin mugun gata wanda babu wanda ya isa ya dungureta  sai Inna Kande ta ji dalili.

Yayanta Hafiz kawai take shakka duk ƙauyen Maska da kewayenta, shima don bai raga mata duk da turaja da faɗan da Inna Kande ke yi duk sanda taji kukan Nuratun.

 

Sai da ta kai shekaru bakwai amma bata zuwa islamiyya bata zuwa boko ko da yaushe tana zaune kan cinyar Inna Kande tana yi mata tatsuniya ko tana bata labarin da.

 

Sai da Hafiz yayi da gaske sannan ya kaita islamiyya ya kaita boko sai dai sam bata zuwa sai fa idan yana garinne take zuwa shima a makare.

Kasancewar yanzu yana Funtua yana karatu yasa Nuratu ke abin da taga dama ita da Inna Kande.

Sai dai yana zuwa zai fara da tambayar Inna Kande "Nuratu na zuwa makaranta kuwa ? Duk da Inna Kande bata son a taɓa mata Lantai kamar yadda take kiranta amma bata ɓoye ma shi rashin zuwan Nuratun makaranta sai dai ta ce, "Bance ka daketa ba ka dai mata nasiha kawai kuma ka dinga ba da kuɗin tararta ana bata duk sanda zata je shi ne magana."

 

Ko da yaushe haka suke sai ya samu sa'ar kamata yayi mata duka ya kaita makaranta yace duk sanda ta sake fashin zuwa makaranta a je gidan a ɗauko ta ai mata dukan tsiya.

 

Lokacin daya koma Funtua Malamin islamiyyarsu ya aiko yara yace su kira masa Lantai ɗin ƙin zuwa tai, don haka washegari sai yace a ɗauko ma shi ita kamar yadda Yayanta yace.

 

Aikuwa sai ga yara ɗuu sun je za su ɗauke ta su kai ma Malam.

 

Inna Kande na Sallah taji hayaniyar yaran da masifar da Lantai ke yi akan duk wanda ya taɓa ta sai ta ci mai uwa yasa ta sallame sallar ta fito don jin abin da ke faruwa.

Ko da yaran suka gaya mata saƙon Malam sai Inna Kande ta gyara mayafinta ta dubi Lantai ta ce, "Ba ke yake nufi ba ni yake nufi tunda ni ce mai gidan yi zamanki ni su kai ni naji dalilin kiran."

 

Aikuwa Lantai ta kwanta tana yi ma yaran gwalo, da tsokanarsu wai su ɗauki Inna Kande Idan ba ƙarya ba.

 

Ko da yara suka ga da gaske Inna Kande take sai suka ruga, suka bar Inna Kande, ta kuwa bisu a hankali har makarantar tun kafin ta shiga ajin take tambayar Malamin daya aika a kamo Lantai kamar wata ɓarauniya.

 

Cikin natsuwa Malam Ali ya bayyanawa Inna Kande yadda sukai da Hafiz Yayan Nuratu.

 

Ta kuwa ja uban tsaki ta ce, "Na ɗauka wani ƙaton laifi ne tayi wanda daga nan wajen mai gari za a nufa da ita ai, ashe ma abin da bai zama dole bane yasa kake son cutar min jika to kayi arziƙi yau daka sake ka bugeta sai na lahira yafi ka jin daɗi."

 

Malam Aliyu yayi juyin duniyar nan amma Inna Kande ta rufe idonta ta ce duk randa Lantai ta zo makaranta a koya mata, randa bata zo ba su koyawa yaran gari ba matsala, inda matsalai take dai shi ne a dakar mata jika anan za a matsala."

 

Ko da ta dawo gida ta sake maimaita ma Lantai kamar yadda ta gayama Malam Alin don haka Lantai ta daina zuwa islamiyya sai tasan Yayanta zai zo sai ta je.

 

Makarantar boko kuwa wani Malami mai nacin tsiya ne ke takura mata tun ranar da Yayanta ya kaita ya gane ta motsi kaɗan ya aiko kiran Nuratu Kabir kamar shi ne ya raɗa mata sunan, bayan ita ko nashi sunan bata sani ba, amma shi ya riƙe nata sunan sarai.

 

Ranar da tayi fashin zuwa makaranta na kwana biyu, data je ba ƙaramin mugunta yayi mata ba, yasa ɗebo ruwa yasata sharan tsakar makaranta sannan ya hanata komawa gida yin tara ga yunwa tana ji amma yace babu inda zata tunda take fashin zuwa makaranta.

 

Ranar tayi kuka iya kuka ta kira sunan Inna Kande har babu adadi amma Malamin nan yayi biris da ita yayi ta sabgar gabanshi batare da ya kulata ba.

 

Wani ƙarin takaicinta ma yadda a gaban idonta ya siyo rakenshi yayi ta sha yana rubutun gulma a takardu ko ya sammata har ya shanye abinsa bai bata ko da ɓalla guda ba.

 

Itama sai ta rayama ranta tabbas ba zata ƙyaleshi haka ba da zagin dayake ta mata wai jaka daga yace ta rubuta sunanta ta ce bata iya ba, shi ne yake ta ce mata jaka.

 

 

Ko da aka tashi sai da yara kowa ya tafi gida sannan Malam Muntasir yace Nuratu ta tafi gida.

 

Ai kamar tana jira tana fita ƙofar office ɗin ta fara kwaɗa ihun "Inna Kande yunwa zata kashe ni wayyo ni Lantai."

Yana jinta yayi banza da ita ya gama abin da zai ya fito ya isketa zaune ƙasa sai kuka take tana harba ƙafafuwanta ya taɓa ta ya wuce yayi kamar bai san ta ba.

 

Wata yarinya ƴar unguwarsu ta aika wai ta ce ma Inna Kande ko ta zo ko ta ga gawarta.

 

Ai kuwa ba jimawa sai ga Inna Kande sai haɗa hanya take tana sababin idan aka kashe mata yarinya ba zata yadda ba.

Duk abin da ake Malam Muntasir na kallonsu har sanda ta aiki yarinyar ya gani bai san abin da ta ce ba sai da yaga tsohuwar ya fahimci kiranta tayi.

 

Inna Kande ta cicciɓeta suka tafi tana cewa kin gama makarantar tunda ba ta zuwa aljanna bace ba daga yau baki sake zuwanta."

 

Suna wucewa ya fito da wayarsa ya kira wayar Yayanta daya ba shi yace ko da wata matsala ta samu a kira shi.

 

Sosai yayi ma Hafiz bayanin matsalar Nuratu data Inna Kande, Hafiz ya ba shi haƙuri yace yau yana hanya gobe shi zai kawota makarantar da kanshi.

 

Suna komawa gida Lantai ta shantake ita ala dole tasha wahala tasha yunwa makaranta don haka bata lafiya.

Inna Kande ta dinga sintiri tana tsinema karatun bokon sai ga Hafiz ayam ya shigo gidan.

 

Ai da gudu Nuratu ta tashi ta ware kamar ba ita ba,  ba kamar da taga yadda ya shigo ba fara'a ga bulala mai baki biyu sai duk su duka suka sha jinin jikinsu hada Inna Kanden.

 

Sai da yayi kamar zai zaneta Inna Kande nata faɗa sannan ya aje bulalar ya shaida mata duk cikin watan nan idan ta sake bata je makaranta ba sai ya zaneta , ya tabbatar mata da gobe da kanshi zai kaita makarantar yasa a zaneta tunda bata zuwa so take ta zama jakka.

 

Ai washegari tunda safe ta shirya kafin ya tashi barci ta nufi  makarantar.

Lokacin data je babu kowa makarantar ko ina a rufe yake duka azuzuwan sai ta koma ƙofar office ɗin malamai tai zamanta tana wasa da ƙasa.

Inna Kande kuwa kasa jurewa tayi saboda tsabar tausayin Lantai ta iske Hafiz ɗakinsa yana barci taita masifa tana cewa bai samun ladar maraya tunda yake uzzurawa marainiyar Allah ta'ala ,ga shi tunda asubar fari gudun masifarka ta fice ta nufi makaranta."

 

Cikin barci yake jin abin da Inna Kanden ke cewa don haka ya ƙyaleta ya cigaba da neman komawa barcinsa ai kuwa Inna Kande ta ce "Tunda Lantai ta gama barci gidan nan kowama ya gama shi maza ka tashi ka ɗebo mana ruwa babu sun ƙare."

Dole ya tashi ya fita ya janyo ruwan duk da a rijiya yake ya shirya ya nufi makarantarsu Nuratun.

 

Lokacin daya je har sun shiga aji kai tsaye office ya nufa ya kira Malam Muntasir ɗin shi kuma ya kira Nuratun.

 

Ko da sukai ido huɗu da Hafiz sai ta fara leƙe taga ina ya aje bulalar ?

Ya fahimci me take nufi sarai ya shareta ya dubi Malam Muntasir yace, "Duk ranar da Nuratu bata zo makarantar nan ba kai mata bulala ɗari ni ma ka kirani ta waya zan zo nayi mata bulala ɗarin."

 

Malam Muntasir ya zaro ido waje yace, "Duk wanda akaima bulala ɗari mutuwa yake fa?

Hafiz ya yamutsa fuska yace, "Ai tunda bata son karatun gara ta mutu mu huta da ajiyar jaka cikin gidanmu."

 

Nan dai su kai ta tsorata ta sai da ta gama tsorata sannan yace mata kullum ta zo zata amshi kuɗin tara hannun Malam Muntasir duk randa bata amsa ba alamace ta bata zo ba a ranar zata mutu.

 

Idan akwai abin da Nuratu ta tsana bai wuce mutuwa ba don haka tun daga lokacin take zuwa makaranta sai dai ta tsiro da zuwa a makare.

 

 Wannan shi ne labarin Nuratu (Lantai)

 

 

 

   Cigaban labarin.

 

Sosai Lantai ta maida hankali tana koyan karatun Hausa gun Musa duk sanda ta dawo daga makarantar boko abinci kawai take ci ta fice gun Musa indai yana nan ya koya mata karatu.

 

Littafin kuwa kullum sai ta kalleshi yafi sau ɗari a rana, idan  Inna Kande ta ɗauka ta zabura ta amshe ta ce, "Ki jira na gama koyar karantashi nan zan dinga karanta maki shi."

 

Hatta makaranta sai aka samu sauƙinta don kan lokaci take zuwa kuma ta daina barci idan ana darasi ta daina guduwa daga tara taƙi dawowa duk ta bari ita dai burinta ta iya karatu ta karanta littattafin nan na mace mai hawaye wanda zuwa yanzu ta iya rubuta sunan labarin haka ta jima da riƙe sunan daram a bakinta.

Sai dai duk abin har zuwa yanzu bata iya rubuta sunanta ba sai dai ta iya rubuta suna littafin harda na marubucin duka zata iya rubutawa ba tare da ta kalla ba.

Malam Muntasir kanshi ya fahimci yadda ta sauya sai ya ɗauka jakar da yake kiranta da shi ne yasa tayi zuciya take maida hankali yanzu domin ko a jarabawarta ta ci maki fiye da rabi abin da bata taɓa yi ba kenan a makarantar.

 

Ita kuwa Lantai bata da burin da ya wuce ta iya karanta rubutun Hausa don kawai ta karanta labarin matar nan da take zubar hawaye a jikin bangon littafin.

Sannan ta ji sunan littafin an rubuta INA HUJJAR TAKE ?

hada alamar tambaya kamar yadda Musa ya koya mata, shin me ake tambaya ne da akai wannan alamar tambayar a ƙarshen sunan littafin ? Sannan Musa ya gayamata littafin na soyayya ne, me ye soyayayar ma wai ? Kai gaskiya ta ƙagara ta iya karatu ko ta ga amsar tambayoyinta.

 

Ko da yaushe tunaninta kenan da burinta akan wannan littafi da take ta ajiya tana son ta iya karatun Hausa don kawai ta karanta shi.

 

 

Cikin ikon Allah sai ga shi bayan wasu watanni Lantai ta iya karatun Hausa ta iya rubuta sunanta dana mahaifinta harda na Yayanta lafiya lau.

 

Sai dai a lokacin Musa ya gayama kada ta karanta littafin har sai ta gama primary school ɗin ta idan ba haka ba yace karatun bacewa zai yi .

 

Jin hakan yasa ta ɓoye littafin sai dai ta ɗauko ta karanta sunan littafin dana marubucin ta maida ta aje har suka fara jarabawar fita primary ɗin suka gama bata karanta littafin ba amma ta  jima da haddace yadda kalar rubutun sunan littafin yake a idanunta.

 

 

Sai bayan sun kammala jarabawa ne, lokacin tana da shekaru goma sha uku sannan da kanta ta ga dacewar karanta labarin ko da kuwa Musa bai amince ta karanta ba.

 

Ranar da zata fara karanta labarin da wuri ta gama yi ma Inna Kande duk wani aikin da take mata, ta siyo mata goronta ta jawo ruwa daga rijiya ta yi girki duk Inna Kande nata mamakinta bata dai tanka mata ba, sai da ta shimfiɗa tabarma sannan ta dubi Inna Kande ta ce, "Don Allah tunda na gama yi maki komi kada ki tanka min yau na yafe duk wani labari naki da tatsuniya ni ma yau karatu zan yi mai girma wanda nake ta jiran lokacin yinsa shekaru masu dama sai yau lokacin yayi."

 

Inna Kande ta taɓe baki ta ce, "Ke dai kika sani, ai daman ba son surutun nake ba kece mai sani yinsa, bari ki ga ma na kunna rediyo ta naji abin da duniyar take ciki ni."

Ta janyo rediyonta ta kunna ta kishingiɗa tana saurare.

 

Cikin ɗoki Lantai ta buɗe shafin farko na littafin inda ta ci karo da sunan labarin da shekarar da aka buga labarin 2006.

 

Tiryan-tiryan Lantai ta fara karanta labari batai wani nisaba ta rufe ta fara sharhi ita kaɗai akan abin da ta karanta.

 

Sai tayi-tayi sai ta aje tayi sharhi ta sake karantawa.

 

Ai tafiya na nisa sai ga Lantai da kuka wi-wi kamar an ce ta taho Inna Kande ta mutu.

 

"Allah Sarki abin tausayi wayyo Allah ya za ki yi kenan ?

 

Sai kuka take tana tambayar da babu wanda zai bata amsar ta.

 

Inna Kande ganin yadda Lantai ta dage tana ta kuka tana surutai yasa ta amshe littafin tana mitar "Ina amfanin irin wannan abu ? Kamar karatun dole da za ki dinga yi kina kuka ?

 

Lantai dai sai kuka take tana goge hawayenta domin labarin ya bata tausayi sosai yarinyar labarin ta bata tausayi tabbas ƙaddara ce ta soyayya ta faɗa ma yarinyar .

 

Sai da tai ta rantsuwa ta daina kukan sanan Inna Kande ta bata littafin amma tana fara karantawa sai ta sake fashewa da kuka sosai ta ruga ɗaki ta rufo.

 

Inna Kande ta dubi ɗakin ta ce, "Sai dai ki cinye kanki ko Yayanki da wannan kukan ba dai ni ba, kuma yau littafin nan a masai zai kwana."

 

 

Mu je zuwa dai .

 

Haupha 

 

 

*SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)*