HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 7
Cikin alamar firgici ta dubi ƙawarta dake niyyar yi mata ɓaran-ɓarama tace, "Jira ciki man." Baban Jiddah ya nufi hanyar gidan tamkar da shi take. Wannan karon ya zo ne ya ga yarinyarsa yaga yadda ta koma idan ta kama ya tafi da ita kamar yadda Sule ke ta ƙwaƙwa sai ya tafi da ita, daman ya yi sabon aure tuni har matar ta haihu yaro namiji sai ya kai mata ta haɗa da Jiddah ta riƙe mai. Ko da Babban Jiddah ya shige gidan sai Iyami ta dawo da natsuwarta gun baƙin da ba ko shakka silar Alawiyya suka zo. " Oga ina ji." Mai kama da Alawiyya yake magana wancan ko kallo bata ishe shi ba, ga alama zai iya naɗa mata ɗan karen duka idan tai wasa don haka ta ƙara natsuwa gabanta na faɗuwa. " Sunana Bello na zo daga Kano nine mahaifin Alawiyya, an tabbatar min da cewa da Inna Kande zata tafi garinsu ke taba ajiyar Alawiyya kafin ta dawo, amma har yanzu bata dawo ba. A takaice dai wannan Yayana ne na zo tafiya da Alawiyya, kuma ina matuƙar godiyar riƙe min ita da kikai ina maki fatan nasara a rayuwa, ga wannan ba yawa." Ya fitar da dunƙulin kuɗi masu dama ya miƙa mata. Sai dai Iyami kasa ɗaga yatsanta tai duk masifar ƙulafucinta da kuɗi, duk yadda take girmama darajar masu kima da mutunci a idon kowa, dubu-dubu abin shan iska, sai ta ji sam basu birge ta ba, ashe ma ko kyau basu da shi na jikin hoton haka nan aka zaɓi manyan munana aka danƙara su a manyan kuɗaɗe ƙarshen canji.
Bello kuwa ya ƙagara ta ce ga Alawiyya ko ga inda take ya ganta, tabbas tunda ya tafi yake kwana yake tashi da ƙaunar yarinyarsa har da ta mahaifiyarta a ransa, amma ya zai fi danginsa, iyayensa, su ne sukai karan tsaye a cikin lamarin dole ya yi masu abin da suke so. Sai ga shi ganin ya shiga matsanancin hali yasa su da kansu suka ga dacewar a rako shi ya tafi da yarinyar har ma da Uwar idan batai aure ba. Sai dai yana zuwa ya fara bincike aka gaya mai abin da ke faruwa na auren Fatima da Soja da tafiyar Inna Kande da gun Iyami data bada ta ajiya. Har gashin gunar waken da Iyami ke mata duk sai da aka ba shi labari. Tabbas danginsa sun zalunce shi, sun shiga haƙƙinsa sosai ba tare da duban girman iyali ba suka tsige shi daga cikin zuri'arsa suka tafi shekara da shekaru suka manta da ta'asar da su kai sai da suka fahimci zai iya mutuwa ko haukacewa sannan suka gane kurensu suka ce ya zo ya tafi da iyalinsa cikin danginsa su yi rayuwa cikin ahali su ma.
Iyami zufa ta karyo mata tace, "Alawiyya sun yi nisan kiwo tun jiya amma suna hanya yanzu." Sai da Yayan Bello ya tare shi kaɗan ya hana ya yanke jiki ya faɗi jin furucin Iyami. Hatta shi kanshi Yayan nashi dake ta kumburin an kai yarinya gun arniya sai da ya ji wani iri a jikinsa, tausayin yarinyar da ubanta ya kama shi. Kana da rai da lafiya cike da rufin asiri ace ƴarka mace na gun arniya ? Tabbas lamarin akwai sosa zuciyar mai imani.
"To daman takan yi nisa ne irin wannan?" Cewar Yayan Bello yana duban Iyami kamar ya rufe ta da dukan tsiya. Iyami ta haɗe miyau da ƙyar tace, "A'a yabi abokinsa na wajena ne Jiddoh." Da farko har sun zabura jin kalmar aboki amma da suka tuna bagwariya ce sai suka fahimci mace ce take nufi mai suna Jiddah, sai zukatansu su kai sanyi kaɗan. "To ina suke zuwa ne da Jiddah ɗin?" Yanzu ma Yayan Bello ne ya yi tambayar. "Ku je zuwa dare za su dawo sai ku zo." Cewar Iyami tana ƙibta idanuwa kamar Bawa yaima Sarki ƙarya. Tace haka ne don kada zawon da take riƙe wa ya kubce mata, sannan yanzu zata koma gun Baban Jiddah ta tsara shi ya fice daga gidan ita kuma bata jan burki ko ina sai motar garinsu. Ko da suka ji me tace sai suka amince suka tafi da niyyar zuwa dare za su dawo lokacin Alawiyya da Jiddah sun dawo. A nata tsarin ita kuma lokacin ta jima da yin nisa hanyar garinsu a mota.
Ko da ta shiga cikin gidan ta iske Baban Jiddah zaune kamar mai tunani, tace "Oga kina tuna me ne? Ta wurgama ƙawarta harara don ta ɗauka ta gaya ma shi ɓatan Jiddah ne. Amma sai tai mata inkiya da ba abin da ta gaya mai, sai ta ji sanyi tace ma shi, "Jiddah sun je gidan Inna Kande ita da ƙawarta Alawiyya zuwa dare za su dawo mu cigaba da gyaran gidan sabon fenti zan yi ne don haka muka fito da kayayyaki duk gidan ya watse." Murmushi ya yi jin Jiddah na gidan ƙawarta, kenan Jiddah an girma har gidan ƙawaye ake zuwa, shi kawai so yake ya ganta yaga yadda ta koma don rabon shi da ita tun tana ƙarama, yasan ta sauya ta sake kamanni amma bai san ya ta koma ba sam, hakan yasa yake son ganinta, itama ta ganshi domin yasan bata san shi ba. Iyami ta zubama lemu maganin barci ta ba shi, ya amsa kuwa ya shanye ya ɗan kishingiɗa kenan Iyami da ƙawarta suka kwashe kayan da take buƙata su kai tafiyarsu, ba ɓata lokaci Iyami ta biya kuɗin cikon mutum guda da babu mota ta ɗaga zuwa Jahar su Iyami. Sai da suka hau titi ɗoɗar ranta ya yi sanyi ta dawo cikin natsuwarta tana jin ta rabu da su lafiya kowa ya je ya nemi inda ƴarshi take ba ruwanta.
Bello kam mutane yai ta bi yana tambayar yadda Alawiyya take rayuwa, ya ji takaicin wahalar da yarinyarsa take sha, haka ya girgiza jin labarin auren Fatima, ko shakka babu ya gama aure tunda ya rasa Fatima shike nan ya yi ban kwana da rayuwar aure. Dare na yi suka sake komawa gidan Iyami su kai ta sallama amma shiru ba a amsa ba, haka ba alamar za a amsa. Hakan yasa suka yanke shawarar shiga cikin gidan da kansu don ba su san yawan adadin awannin da za su ɗauka suna tsaye gunba. Sannan da suka zo da rana magana guda su kai Iyami ta fito amma yanzu sun yi tafi goma ba alamar zata fito ko ta amsa daga cikin gidan.
Yana kwance kamar gawa sai barci yake hankalinsa kwance, sun dudduba basu ga alamar kowa ba hatta kaya babu cikin gidan hakan ya ɗaga hankalin Bello har ya kasa riƙe kansa ya tsugunna yana dafe kansa. "Yaya ta gudunmun da ɗiya wallahi ba zan yadda ba sai na nemo ta duk inda take." Shi kanshi Yayan ya amince akwai matsala tun ɗazun yaso ya fahimci babu gaskiya a lamarin matar duba da maganar matar da ta iso gun, da yadda Iyami taita zufa tana mazurai amma sai bai kawo hakan a matsayin wannan gagarumin aikin take shirya wa ba, ya ɗauka ta ruɗe ne ganinsu a lokacin da take tsaka da ganawa yarinyar azaba,ashe abun wushe nan in ji Bahillace. Salati Bello ke yi tare da kuka kamar ƙaramin yaron goge wanda kukansa ya tada Baban Jiddah dake barci magashiyan na maganin da ya sha a lemu. Shi ma a firgice ya tashi, ganin abin da ke faruwa ya ɗaure mai kai, har ya kasa tambayar me ke faruwa sai dai ya bi ɗakin Iyami da kallo a zatonsa tana ciki. Amma ganin har mutane sun fara shigowa yasa ya miƙe jikinsa duk yana mai ciwo ya isa inda mutane ke maida yadda akai shima don yana son fahimtar abin da ke faruwa a cikin gidan Iyami, kuma ina ita Iyamin take ne? Bai ganta ba duk yawan mutanen dake cikin gidan.
"Don Allah me ke faruwa ne a nan?" Cewar Baban Jiddah yana duban wani matashin yaro. Yaron ya dube shi yace, "Iyami ce ta gudu da yara guda biyu mata to a ciki akwai ɗiyar wancan bawan Allah mai kuka... Cikin magun tashin hankali Baban Jiddah ya kwashe fuskar matashin da mari yana huci yace, "Uban wa ya gayama Iyami zata iya guduwa da yaran mutane? Nasan ta farin sani tun zamanin ina samartaka ban mata kallon maci amana sam." Nan take kallo ya dawo kansu.
Maƙwabcinsu yace, "Malam sai dai kai haƙuri amma yau kwana uku da Iyami tai mana bankwana tace zata koma Jaharsu domin a can zata aurar da Jiddah." Daram! Rass! Gabansa ya yanke ya faɗi. Jagwab ya zauna zufa na keto mai ta ko'ina. "Amma Iyami kin yaudare ni kin ci amanata, tabbas sai na rama abin da ki kai min komin daren daɗewa sai kin gane cewar duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, dole ki gane wanene Uban Dawa! Tabbas kin yi wauta kin aikata zunubin da baki iya gyara shi indai da gaske na amsa sunan Uban Dawa to Iyami za ki kasance cikin tararrabin rayuwa, da ƙunci da zullumi na iyakar rashin haɗuwata da ɗiyata Jiddah! Bai sake kallon kowa ba ya fice jikinsa na tsuma kamar ɗan bori.
Bello kuwa ya yanke jiki ya faɗi ba numfashi.
To fa!
Ko ya kenan?
Ya labarinsu Jiddah ne?
Taku a kullum Haupha!!!!