Majalisar Dunkin Duniya Ta Cire Nijeriya A Cikin Jerin Kasashe 10 Da Suka Fi Cigaba A Afrika
Najeriya ta cikin jerin kasashen da suka fi ci gaba a nahiyar Afirka bisa rahoton na ci gaban bil'adama na HDI ta fitar.
Ana auna matsayin kasashe ne ta hanyoyin da suka hada da samar da ababen more rayuwa na zamani kamar kyawawan hanyoyi, ingantacciyar wutar lantarki, ingantattun hanyoyin sadarwa da tsarin kiwon lafiya mai aiki.
Sauran ma'aunai na HDI sun haDa da gwamnati mai kyau, ayyuka masu kyau, samun damar kiwon lafiya da ayyuka na zamantakewa, 'yancin rayuwa a sakata a wala, da ingantaccen tsarin ilimi.
Business Insider ya ba da rahoton cewa kididdigar ci gaban bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ita ce kayan aikin da aka fi amfani da ita a duniya wajen auna matsayin ci gaban kasashe.
An tsara shirin na Majalisar Dinkin Duniya ta yadda zai auna mutane ta hanyar HDI ba kawai ci gaban tattalin arziki ba. Ma'aunan na HDI kuma na bibiyar tsawon rayuwa, ilimi tsakanin masu manyan shekaru, samun damar hawa intanet da rashin daidaito wajen samun kudin shiga. Ma'aunin na aiki ne daga matsayi 0.00 zuwa 1.00.
Kasashen da suka zo da maki kadan a ma'aunin daga 0.00 zuwa 0.66 suna da karancin ci gaban bil'adama. Samun maki tsakanin 0.55 zuwa 0.75 yana nuna kasa mai matsakaicin ci gaban bil'adama.
Kasashen da ke da maki 0.70 zuwa 0.80 suna da babban kasa na HDI, yayin da kasashe masu girman ci gaban bil'adama ke da maki tsakanin 0.80 zuwa 1.0.
An lissafo kasashen Afirka da ke da mafi yawan maki na ci gaban bil'adama, duk da cewa suna kasa sosai idan aka kwatanta da sauran kasashe masu ci gaban tattalin arziki a duniya.
Jerin kasashen Afrika 10
- Mauritius: 0.804.
- Seychelles: 0.796.
- Algeria: 0.748.
- Tunisia: 0.740.
- Botswana: 0.735.
- Libya: 0.724,
- South Africa: 0.709.
- Egypt: 0.707.
- Gabon: 0.703.
- Morocco: 0.686.
managarciya