DA AURE NAH: Labarin Cin Amana Mai Muni Fita Ta Shida 

DA AURE NAH: Labarin Cin Amana Mai Muni Fita Ta Shida 
DA AURE NAH                
*NA*
          *HAUWA'U SALISU** 
Page 6
 
 Cikin azama yafada dakinsa ya bude takardai xuciyansa fal fargaban abunda xai gani Rayuwa mai ban mamaki 
Kaidai kaga mutum bansan adadin tsawon lokacin dana dauka ina dakon soyayyarsaba kamar yanda shi ma bai san ina sonsa ba Soyayya bata da tabbas ake cewa amma nitawa tana da tabbas dan gashi a kanta nagwanmace na yi nesa da Ahalina kawayena kodan xuciyata ta samu salama Shi ne nafara so a rayuwata amma yayi mun nisa dan kawata yake so take sonsa ina xan kai wannan kayan haushin ni Huwailat
Bana iya jure xama inuwa daya daku alhalin kuna masoya baxan iyaba Shine nafarko danaso shine na karshe a xuciyana nasan dama kowa da qaddaraisa a soyayyah toni tawace wannan a cikinku duk wadda taga wannan sako nawa taba da yai hakuri a kan rashin cika alqawarina na tafiya ni kadai boarding school ba tare da ku ba ban da yanda xan yi ne ina tsaka mai wuyane Fatana gunku kuyi mun uxuri kumanta dani ko bayan na dawo dan ba xan iya cigaba da kawance da ku ba ku yafemun nima na yafe maku 
Taku Huwailat Abdullahi 
Tunda ya gama karanta later yake tunani kenan daman saurayin kawai ta take so 
Dan haka ta gaxa bashi amsar later sa lallai biri yayi kama da mutum amma xai je gun Hafsat danjin yanda abun yake yau da dare ba xai iya bari sai Zainab ta dawo ba 
Hafsat na tafe kan hanya tana magana mi yasa haka Zainab adalci baice hakanba kin fi kowa sanin yanda Huwailat ke son Habeeb amma kika fara soyayya da shi why Zainab
 Huwailat ba ta cancanci wannan cin amanar ba daga gare ki ba tana da kirki tana son mu why Zainab 
Haka taita surutai harta isa gidansu ta iske babban yayansu kofar gida yakirata yaji daga ina take Yah Salim gidansu Huwailat kawata naje tunda muka koma school bata je ba gaba daya ya maido hankalinsa kanta dan yajima yana kaunar Huwailat furtawa ya gaxa yi dan yaga tana karatu amma yau xai furta abunda ke ransa ga kanwarsa danta tayasa neman fada gun Gimbiyar
 Mi ya faru da kika je to     ya jefa mata tambaya Yaya Ashe school ta sake ban sani ba sai hawaye Idanu ya bita da su to miye danta sake school sai akace ke ta sake bansan shagwabar banxa fa Sanin hali tashare hawayenta xata tafi ya tsaidata  shin kawar ki nada saurayi kuwa Hafsat Wani munafin dadi ya tsargu a xuciyanta tasamu hanyar da xata wankema kawarta takaicin Habeeb da Zainab cikin sauri tace bata kula samari ai tace saita kai S S 2 sannan Masha Allah ko xata iya soyayya dani kuwa Hafsat ki tuntubarmun ita idan ta dawo hutu ba damuwa Yayah xan fada mata kuma gaskiya na yi murna ta fada gida tana dariya Sai a sannan taji duk wata damuwanta ta yaye dan Yayanta ya hada komi da ake buqata ga saurayi yana da aikinsa sannan ya ma fi Habeeb sakin fuska uwa uba shi ne ya furta mata so ba ita  ce ta fara sonsa ba abun xai fi armashi
Dare na yi aka aiko kiran Hafsat bata kawo komi ba aranta  ta fito Habeeb ta hango tsaye tamke fuskaita tayi tam ta qarasa gunsa da sallama ya ansa Hafsat daxun kinban takarda wadda tasani a rudani sosai waye Huwailat take so ne hakan Budar bakin Hafsat tace Yayanah Ina gefe nace taufa.
Tun daga kansa yaji xufa ta fara wanke masa jiki cikin tashin hankali yace pls yaya hakan ya faru ne bayan tasan abun da ke faruwa Wani banxan kallo ta watsa masa tace xan shiga gida dan fada ake mun inna dade tasa kai tabarsa yana cixon yatsa nace yanxu ka fara ganima Habeeb.
Gobe ne Hutu kowa na cikin farin ciki da walwala banda Huwailat da take goge hawaye a kaikaice har Aisha ta dafa ni Huwailat miya faru kike Hawaye ranar murna da farin ciki amma kina kuka na kula yau da damuwa kika tashi ki sani ana yin abota ne dan idan ka shiga damuwa ka samu Wanda xaka amayema ita ko baku samu mafita ba ka rage damuwa a xuciyanka Idan kin yarda da maganata ki fadan damuwan sai musamu hanyar magance ta pls 
Tabbas gaskiya Aisha ta fada dan haka ta samu kanta da fadama Aisha damuwanta duka amma kin yi wauta da baki bude later ba sannan kinyi nauyin baki da baki tambayi Zainab abunda suka tattauna ba kafin ki yanke hukunci Huwailat amma idan kin koma ki fara karanta later sannan ki samu qwarin gwiwan tunkarai Zainab Hankali taji natsuwa na shiganta taima Aisha godiya in  tai mata dariya tana Mrs Habeeb ba godiya tsakaninmu ai mufa friends ne sukai dariya tare Washe gari akai mana Hutu yah Abbah yaxo daukana mukai bankwana dasu Asmau dan Aisha yar Kaduna ce Asmau yar Abuja Tunda muka shigo anguwanmu na hango Habeeb xaune maxauninsa yaci uban wanka sai fara a yake na tabe baki nace kilan ansa masu rana ne Cikin ko inkula na fada gida da gudu ina kiran mama Baba nadawo gani Tare suka fito suna dariya tsaye nayi dan ganin mama da ciki kato cikin farin ciki na fada mata ina murna Baba ya janye ni Auta baki ganin ba ita kadai ba ce Sunne kai nayi na fada dakina ina jin farin cikin xan samu qani ko kanwa nima akirani da Yayah Banjima da fitowa wanka ba Hafsat taxo na tarbeta ba yabo ba fallasa cikin nuna ban kyauta mata ba tace Bansan yaushe alaqarmu ta juya ne yaushe muka fara boye damuwanmu ga juna Huwailat ashe xaki iya canxamu akan soyayya lallai banda hankali dan xan iya sadaukar maku da komi Dan aganina kawance yafi soyayya Ashe ba haka bane Cikin jin nauyin kalaman Hafsat na tashi na dauko later nan danaje tunda nadawo rannan namikama Hafsat nace mu fara karanta wasika sannan saimu yanke hukunci Hafsat Wannanfa ta fara juya later nace tun wadda Zainab tabance randa sukai magana da Habeeb ban bude ba sai yanxu nakeson mukaranta tare Hafsat ta warware later gabana na faduwa nafara karantawa Amincin Allah ya tabbata gare ki kyakykyawar anguwarmu Lallai najima ina son tunkararki da qoqon barana amma kash kwarjininki namatuqar tasiri a xuciyana. Wanda hakan yasama nake gaxa natsuwa har saina ganki motsinki shi ne kawai ke sani fitowa a dole nai xaman ganin Gimbiyata na tafiya makaranta Karshe naga ba yanda xanyi dole tasa na yanke shawaran rubuto maki wannan later dan na samu na fadi koda Rabin abinda ke raina. 
Fatana xaki yimun adalci kiban Amanar xuciyarki.
 Daga naki Habeeb.
 Cikin sheshshekar kuka na rumgume Hafsat taya xan iya cigaba da xama inaganin Habeeb dawata suna soyayya watanma wai Zainab dinmu.
Girgixani Hafsat keyi tsaya tsaya Huwailat ba muga bayan ba jifa wani rubutunne Araina nace gara ai na ida ganin abunda xai nakasa xuciyata da kyau Huwailat kitaimakeni kada kice baki sonah pls sonki xanene a jikin xuciyana kitausayamun Habeeb naki ne inkin amince pls. 
Xanga Kawarki Zainab taban ansana fatana naji khairan Wata uwar qara nasaki na rumgume Hafsat ina godiya ga Allah murna kamar nayi hauka Hafsat tabini da dariya tana tayani murna harga Allah taji ta hakura da shigar da yayanta gun Huwailat dan tafahimci tayi xurfi a kaunarsa xata basa hakuri tanason Huwailat sosai da sosai Dan haka ta manta komi ta cigaba da tayata murna
Da Hafsat xata tafi naci kwalliya saboda nasan dole xanga Habeeb yau kam xan tsaya namaida masa da amsar later sa da bakina Haka kau akayi muna fitowa muga gansa xaune kofar gidanmu
Nace yau anci gaba kenan za mu rabasa mu wuce yai mana sallama muka gaidasa  nayi alamar tafiya bakiji ba Huwailat sai naji bantaba jin Wanda ya iya furta sunan sama dashi ba naja na tsaya ita kuma Hafsat tayi gaba abunta waitaba masoya waje  Nakallesa nayi murmushi kya kalleni mana kinyiman hijira saura kadan kiganni ai makarantai naku dan gaxa jurewa nayi iyakar tashin hankali nagansa dakya nan Allah yasamun kaunarki sosai araina sosai nakejin dadin kalamansa saidai baxan aminta ya gane ina kaunarsa da wuriba yakamata yaji abunda naji a xuciyata akan kaunarsa Kamar banjiba nayi amma dayake ance son gaskiya baya buya saigani naxaqe inata maida masa martanin kalamai ban San lokaci yaja ba saida na waiga ba Hafsat ba alamarta nai masa bankwana na shige gida Daga nan soyayya mai karfi ta shiga tsakaninmu wadda har gidanmu danasu ansani muna San junanmu Duk sanda nadawo Hutu inxan koma saimunyi kamar xamuyi hauka nida Habeeb sai anyi da gaske muke tafiya atare yakaini hakama in anyi Hutu shike daukoni mama ta haihu lafiya ta haifi yaranta biyu mace da namiji murna kamar xan hauka Habeeb yai rawan gani Dan yaima mama abun arxiqi sosai da sosai nima nasha dinkuna Bayan shekara biyu kowa yasan da soyayya tada Habeeb har manya sun shiga lamarin inda aka yanke shawaran ina gama karatuna xamui Aure naci gaba da karatuna Da Aurenah 
Hakan yaimana dadi sosai da sosai Wannan hutun daga shi baxan sake dawowa ba saina gama tunda safe na hada kayana ina jiran Habeeb yaxo daukana amma tsit hakan yasani adamuwa sosai nakoma Hostel inata kukana aka aiko kirana tunda nafito na hangosa naji sanyi a raina amma na gintse na shige bayan motar naixamana 
Murmushi yayi ranki yadade afuwan yau banda lafiya ne yanxu haka da kal naxo kuma sai motar tasamu matsala aimun afuwa baxan sakeba gimbiyar mata Cikin xunbura baki nadawo gaban amma bance kalaba muka kama hanyai gida yanata lallashina inashan qamshi Dan inasan naga ina fushi yanata ban hakuri sainaji nafi kowa Wasa wasa nadinga share Habeeb koya shigo ban masa magana saiga mamansa yaturo taban hakuri baxai sakeba Mama taita fada wai da itace bata xuwa mukarata can Daga nan dai komi yawuce muka koma kamar da so da kulawa nata qara bunqasa tsakaninmu Ranar wata juma a dasafe Habeeb yashigo ina barci yace atadoni xaiban saqo hakana fito inata xunbura bakiYace afuwan gimbiya daman gidanki xani naduba aikin da akai naga koyayi shine xanfada maki anjima kije gidansu Zainab din daga can sauna daukoki Naxunbura baki banyardaba kawai kafara kaini saikaje Auh kice nafara kaiki gidanki dai kawai Dariya nayi banceba saika dawo xanma dawo da kaina harna juya yakirani gimbiya najuyo ya Ciro wani xobe dake yatsansa yasakamun a hannuna sainadawo Yajuya yafice nima nakoma daki abuna nafara shirin xuwa gidansu Zainab Dan fara shirye shiryen bikinsu da Anas Tunda naje gidansu Zainab nakejin banajin dadin jikina Dan haka ana gama sallar axahar natafo gida Tundaga nesa na hango dinbin jama a  cike da anguwar bankawo komi arainaba na durfafi hanyar gidanmu saime su yayah nagani xaune idanu jajir na sake waigawa naga Baba gefe shima da fuskan jimami Dammm gabana yafadi towai mike faruwane 
Na dinga bin mutane da kallo kamar wata  GaulaSaiga Husna da gudu kanwar Habeeb tana kuka tafada kaina Aunty mun rasa Yah Habeeb Tashin hankali wane yah Habeeb din 
Kubiyoni Haupha danjin wane Habeeb din 
Nagode.