Babban Buri:Fita Ta Tara

Babban Buri:Fita Ta Tara

BABBAN BURI


MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH


SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.


بسم الله الرحمن الرحيم


FITA TA TARA.


~~~~Na jima zaune a gurin sannan naga shigowar mota a cikin gidan , hankalina kacokan na mayar a kanta iname addu'ar Allah yasa su ɗin ne.
Ganin shi ɗin ne kuwa saida wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ga suɓucemin iname godiya ga Allah daya dawomin da ƙanwata lafiya.

Tare suka jero suna tafe suna fira kace dama sunsan juna ne, abin ya bani mamaki sosai da sosai ganin yadda A'isha take murmusawa wacce ko kaɗan bata da fara'a balle magana, takan share awa 3 ba tare da tace da kowa komai ba , baki tayi ta kallon mutane.

Sam ban kula da isowarsu guna ba sai da naji magana a cikin kunnena "Mekike tunani ne, ko kin zaci na sayar maki da ƴar ƙanwarki ne?".

Saurin ɗago kaina nayi ai kuwa idanuwana sai cikin nasa da hanzarina na ɗauke nawa a kansa iname aikawa A'isha harara a ƙasan ido.

Ba tare dana ce dashi komai ba na miƙe na yi shigewata sashen Hajiya Inna ina cewa "Mama ya kamata muyi gida hwa ganin su Ahmad kaɗai ne muka baro a cikin gida."

Kin koyi gaskiyaKhadeejah, kin ganni harna manta kuwa.

Lokacin suka shigo ɗakin  suna dariyar dana rasa ta mece , wata hararar na wurgawa A'ishah, sannan nayi ƙwafa na ɗauki jakkata sannan na yi wa Hajiya Inna sallama na koma bakin ƙofar shiga sashen nayi tsaye.

Basu jima ba suka fito wannan karon harda Hajiya Inna dashi kanshi uban gayyar.

Na zaci a ƙafa zamuje sai naga munja birki a dai dai gurinda ya yi parking ɗin motarsa, harna fara zarar idanuwa na zaci shine zai kaimu sai naga ya kira Baban Gida direba ya miƙa masa key ɗin mota kan ya ce "A'isha ta yi masa kwatancen gidanmu.

A haka Mama da Hajiya Inna su kayi sallama kamar karsu rabu, muka ƙame a cikin mota sai gida.

Munyi mamaki sosai na ganin iyayen kayan da ake fito mana dasu a cikin motar AAS Wurno, kallon A'isha na yi iname zare mata idanuwa yayinda ita kuwa sai faman shan mur ta keyi.

A haka aka shigar mana da kayan cikin gida sosai Mama ta dinga yiwa A'isha faɗa akan meyasa bata gaya mana abinda ke cikin motar ba, ko lokacin da yake sayan kayan bata hana sa ba.

Haƙuri ta dinga bawa Mama ganin yadda ranta ya ɓaci.
Yayinda su Ahmad sai tsalle su keyi suna faɗan za suci taliyar yara da kwai, kujifa.

Haka muka tattara kayan muka ajiye gefe da zummar idan Baba ya dawo a nuna masa duk abinda ya zartas a kan kayan shine za'ayi dasu.

Anan tsakar gidan muka zauna muna yaba karamci da mutunci irin na Hajiya Inna.
Ganin Mama bata tambayeni sauran masu gidan ba ya sanya ni kama bakina na tsuke domin kujewa faɗan Mama ba faɗan abinda ba'ayi ba.

Bayan sallar isha'i muna ɗaki nida A'isha naji Mama nayi wa Baba bayanin kayan da muka dawo dasu.
Kira mukaji ya kwalawa A'isha nan da nan ta hau zare idanuwa kamar wacce tayi wa sarki ƙarya.

Faɗa sosai shima Baba ya yi mata kan ya ce "gobe idan naje gidan nayi masu godiya ga mutanen gidan sosai da sosai".

A wannan daren ma haka nayi ta juyi nice bacci be ɗauke ni ba sai guraren subahin, abin yanzu harya zaman mani jiki.

Yauma kamar kullum ina kammala abinda nake yi na doshi gidan aikina , haka kawai nake jin gabana na faɗuwa , duk takun da nayi da faɗuwar gaba tare dashi haka na dinga ji har lokacin dana isa gidan.

Gaisawa na yi da mutanen dake bakin get  kamar yadda na saba a ko wanne lokaci kana na nufi cikin gidan.

Babban kitchin ɗin gidan na nufa kai tsaye, ganin jiya banyi aikin komai.
Gaisawa na yi dasu Yahanazu kan mu fara aikinmu na haɗawa mutan gidan break fast.

Muna kammalawa na nufi sashen Hajiya Inna, har lokacin gabana naci gaba da faduwa.

A uwar ɗakinta na iskota yau can na nufa bayan mun gaisa take tambayata yasu A'isha, suna lafiya ƙalau na bata amsa sannan na gaya mata saƙon Baba harma da Mama.

Murmushin kawai ta yi ta ce "bakomai yiwa kaine".s
Sannan tace "dan Allah Hadeejatu duba ɗakin Shalelena idan yana buƙatar gyara ko gyara masa shi.

Miƙewa na yi sannan na doshi ɗakin nasa.

Zaune yake photuna ne yake kallo yana faman sharce zufar dake yi masa tarara kamar ba na'urar sanyaya ɗaki a cikin ɗakin, yayinda idanuwansa su kayi jazur dasu.

Jin sallama a bakin ƙofar ɗakin ya sanya sa saurin mayar da photunan jikin ma'ajiyar su sai dai be kula da wani photo wanda ya faɗi ƙasa ba, yayi azamar miƙewa ya yi cikin uwar ɗakin.

Sallama na yi har sau biyu naji shuru , jin kamar bakowa a ɗakin ya sanya ni sanya kaina gaba ɗaya cikin ɗakin, tsayawa ƙarewa ɗakin kallo na yi na mintuna a ƙalla uku, idanuwana ne suka sauka a saman photon dake yashe a gurin.

Isa gurin da yake na yi iname sanya hannu da niyar dauko photon.

Ɗan jim nayi kamin na miƙa hannu na ɗauko sa.

Zaune na kai iname ƙarewa mutanen dake cikin photon kallo, ɗayan dai na fahimci waye , domin kuwa ina ganin photonsa a ɗakin Hajiya Inna, ɗayan ne idanuwana suka kafe a kansa yayinda gabana ya ci gaba da faffatniya, zuciyata kamar ta tsaga ƙirjina ta fito, na kasa ɗauke su akansa, sai nake ga kamar nasan fuskar kamar kuma gizo ne take yimin.

Jin amshe photon da akayi a hannuna yasan yani saurin ɗago kaina domin ganin waye?, haɗa idanuwa muka yi dashi nayi saurin ɗauke kaina a kansa.
Sannan cikin rawar murya na gaidashi, kallona yake yi yana kallon photon ganin ba amsar da yake nema ya sanya shi takowa a hankali yazo gunda nake tsaye ƙafafuwana na neman kaini ƙasa.

Ganin yazo dai_dai setin da nake har ina jiyo saukar numfashinsa ya sanya ni saukar da kaina ƙasa iname wasa da gefen hijabin da nake sanye dashi.

Miƙomin photon ya yi yana me kafeni da mayatattun idanuwansa, girgiza kai na yi ba tare dana amsan ba.
Tsinkayo muryar sa na yi a can ƙasan moƙoshi "ƙarɓi mana".
Ƙara girgiza kaina na yi  iname jan ƙafafuwana zuwa barin ɗakin , harna samu damar isa bakin ƙofar ya dakatar dani ta hanyar cewa "ji mana", mamakin sane ya sanya ni saurin juyowa ina kallonsa.

Murmushin gefen baki ya yi man kana ya ƙara takowa ya ƙaraso guna ya ce "ina zuwa kuma?", Nuna masa Parlour na yi ba tare da nace dashi komai ba.

"Nasan uzurine ya shigo dake ai ba haka kawai kika shigo ɗakin ba ko?".
Gyaɗa kaina na yi kana cikin sarƙewar murya na ce "Hajiya Inna ce tace nazo na gyara ɗakin, kana kuma Babanmu ya ce ayima godiya sosai sosai."

Ni kaina nayi mamakin irin yadda na samu zarafin yin wannan maganar a gabansa.

Shafa kwantanccen gashin kansa ya yi sannan ya ce "bakomai mune da godiya".
Sannan ya ratsa ta gefena ya fice daga ɗakin.
Nauyayyiyar ajiyar zuciya na sauke lokacin dana ga ficewarsa a ɗakin kana na zube ƙasa ina sauke numfashi da ƙyar kamar wacce ta yi gudun fitar rai.....

Za mu cigaba a gobe.....

ƳAR MUTAN BUBARE CE