Daga Babangida Bisallah, Abuja.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya taya kiristoci murnar zagayowar ranar bikin Kirsimeti da suke yi don tunawa da ranar da aka haifi Yesu Kiristi.
Lawan ya ce baya ga shagulgula da farin cikin zagayowar ranar, ranar Kirsimeti tana tuna ma 'yan adam rayuwa mai sauki da sadaukarwa irin ta Yesu Kiristi.
Ya ce dalili ke nan da wannan lokaci ya zama na nuna soyayya ta zahiri da fatan alkhairi ta hanyar taimaka ma mabukata da makwabta.
Sai dai Lawan ya bukaci yan Najeriya da su aikata abubuwan da za su habaka zaman lafiya a yankunansu kamar yadda wannan lokaci ya ke koyarwa.
Mai baiwa shugaban shawara akan aikin jarida Ola Awoniyi ne ya bayyana sakon shugaban majalisar a wata takardar manema labarai da ya fitar yammacin yau Juma'a dan taya mabiya addinin kirista murnar wannan ranar.
Ya cigaba da cewar "Yesu Kiristi ya kasance mai nuna soyayya, sadaukarwa, adalci da zaman lafiya wanda dukkan su kyawawan dabi'u ne da kasar na take bukata a yanzu fiye da duk wani lokaci a yayin da muke fuskantar manya manyan kalubale don tabbatar da dimokaradiyya da cigaba.
"Don haka, ina bukatar dukkan mu da muyi duba da irin muhimmanci wannan rana don mu rungumi wadannan kyawawan dabi'u domin amfanin kasar nan da jama'a baki daya.
"Mu cigaba da addu'ar neman zaman lafiya a Nijeriya da kuma aikata ayyukan da zasu mai da kasar nan babbar kasar da muke bukata.
"Kalubalen da muke fuskanta a yanzu suna bukatar cigaba da bada hadin kai, goyon baya da fahimtar dukkan yan Najeriya don ganin gwamnati tayi nasara.
"Bani tababar hadin kan da ke tsakanin bangaren majalisa da na zartaswa a tafiyar da aikin gwamnati yana samar da kyakykyawan yanayin siyasa don samar da hanyar warware wadannan kalubalen da amfani da damar makin da muke da su".
Shugaban majalisar ya taya murna ga dukkan yan Najeriya a bisa bikin Kirsimeti da sabuwar shekara mai zuwa.