Bayan Kama Musa Kamarawa, an samu raguwar harin ‘yan bindiga a gabascin Sakkwato

Bayan Kama Musa Kamarawa, an samu raguwar harin ‘yan bindiga a gabascin Sakkwato

Matsalar tabarbarwar tsaro ta ta’azara a gabascin Sakkwato in da kusan kullum sai an kai hari a yankin in da ‘yan bindiga ke cin karensu ba babbaka, shekarrun  baya, an yi fama da tashin hankali da salwatar rayuwar mutanen yankin, an hana su noma da kiyo wanda su kadai ne suka dogara da su.

Matsalar ta haifar da 'yan gudun hijira da zawarawa da marayu masu tarin yawa, abin da ya kai ga duk wanda ba a yankin yake ba an daina zuwa duk wani da yake da wata madafa ya bar yankin tare da iyalansa domin tseratar da rayuwarsa da iyalansa.

Lamarin ya ta'azara a gabascin Sakkwato ana cikin haka sai labari ya watsu an kama Musa Kamarawa yana hannun jami'an tsaro, bayan nan sai ga bidiyo Musa yana bayanin dangantakarsa da jagoran 'yan bindiga na yanki wato Bello Turji wanda ya ce amininsa ne.

Musa Kamarawa dan shekara 33 an haife shi a garin Kamarawa karamar hukumar Isa dake jihar Sakkwato, a hoton bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta in 'yan sanda ke yi masa tambaya kan zargin da ake yi masa na mu'amala da miyagun makamai da hulda da 'yan bindiga da  masu makamai yana sayar musu.

Ya yi bayani ya ce mahaifiyarsa ta fito cikin zuri'ar tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa wadda yaya ce a wurinsa.

"Turji babban dan ta'adda ne dake dajin Kagara har zuwa Fakai, ya shahara awurin garkuwa da mutane da kisan mutane da satar shanu a arewacin Nijeriya, shi aminina ne yana kirana ina kiransa babban aminina ne.

"In sun yi garkuwa da mutane suna kai su daji in da gidajensu suke sai an biya kudin fansa, suna rike manyan bindigogi akwai AK 47 da wadda ake daurawa a mota da wata kundu da ake harbin jirgi da ita, dukkansu suna rike duna," a cewar Musa Kamarawa.

Daga bayyanar wannan ne sai abubuwa suka sauya a yankin in da 'yan bindigar suka shige gashi kamar yadda mutanen yankin ke fadi.

"A Gaskiya tun bayan kama Musa abubuwa sun sauya a yankin namu domin 'yna bindigar sun rage kai mana hari duk da suna shigowa amma ba kamar baya ba, shekaran jiya ma sun tafi Lugu, har dayan ya kashe dan uwansa, a baya da suke zuwa su tayar da gari gaba daya amma yanzu mun yi kusan wata daya ba wani gari da aka tayar sai dai shiga na sunkuru, domin har yanzu suna nan cikin dajin da suke  zaune," a cewar majiyar.

Ya ce kamen ne ya sanya Turji ya rubuta takarda sulhu domin wanda yake idonsa yana hannu, hakan ya sa ya sauya wurin fakewa don bai san shirin jami'an tsaro ba.

A Wannan satin sai ga wani bayani ya fita jami'an tsaro sun kama Dan tsohon gwamnan Sakkwato Honarabul Sagir Attahiru Dalhatu Bafarawa kan binciken da ake yi wa dan uwansa Musa Kamarawa abin da ya musanta.

Sagir ya ce labarin an shirya shi ne domin a bata masa suna "Ba wani kama ni da aka yi kan wai ina tare da 'yan bindiga, ka ganni yanzu ina tare da iyalina cikin kwanciyar hankali ina harkokina na yau da kullum.

"Labaran da ake yadawa domin a bata min suna ne da wasu makiya ke yi, kan haka nake kira ga mutanen Sakkwato da Nijeriya su jefar da wannan labari na karya da wasu bata gari suka shirya," a cewarsa.

A bayanin da makusancinsa Alhaji Abubakar Sambo ya baiwa manema labarai ya ce Sagir wanda Kwamishina ne a ma'aikatar kula da muhali ta jiha ya shawarci jami'an tsaro su binciki lamarin d on fitar da wadan da suka bayar da labarin na karya.   

 Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni Idris Muhammad Gobir ya nuna har yanzu yankin na fama matsalar tsaron "halin da yankin Sakkwato ta gabas yake ciki babu dadi, duk da yanda al'amurra suke na kai farmaki a wurin baki da ba su yankin za su ga ya ragu amma mu 'yan gida da mukasan in da mutanenmu suke da halin da suke ciki mun san ba dadi, a duk garin da yake yankin Sabon birni da suka gudu a garinsu ba wanda ya dawo, har yanzu da nake magana da da kai a wannan rana ta Talata ta wannan satin sai dai mutane suka baro garinsu, da marecen ma na hadu da mutane suna barin garuruwansu a tsakanin iyakar mu da karamar hukumar Goronyo."