Ambaliyar Ruwa Ta Kwashe  Gidaje 350 Da Kayan Abinci a  Sakkwato

Ambaliyar Ruwa Ta Kwashe  Gidaje 350 Da Kayan Abinci a  Sakkwato

 

Ambaliyar ruwan sama ta kwashe gidaje 350 da kayan abinci na amfanin gona a kauyukka uku dake cikin karamar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato.

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta jiha Abdullahi Ghani ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen yanki suna a tagayare kan rashin muhalli.
Ya ce lamarin ya faru ne a satin da ya gabata kuma kauyukkann da abin ya shafa Runji da Makera da Shiyar Ajiya.

Mai baiwa gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal shawara  dake kula da hukumar Alhaji Zubairu Magaji ya ce gidaje 250 ne suka fadi a yankin gaba daya, kan sanadin mamakon ruwn sama da ke sauka a jihar Sakkwato.
Yana ganin ba wata rayuwa da aka rasa sai dai an yi hasarar dimbin kayan abinci da ruwa suka tafi da su.

Ya jajantawa mutanen yankin tare da ba su tabbacin tallafin gwamnati nan ba da jimawa ba.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Ibrahim Lawal ya yabawa gwamnatin jiha kan kula da su, ya kuma roki gwamnati ta bayar da kayan agajin gaggawa cikin lokaci domin mutane sun rasa godajensu kuma ba wani abinci da za su ci suna cikin halin neman taimako.