'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifin Dan Majalisa A Zamfara

'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifin Dan Majalisa A Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kasuwar Daji dake karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da Uban kasar garin Alhaji Ibrahim S/Fada Kasuwar Daji, Uba ga Dan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara mai ci Hon. Anas S. Fada Kaura. 

Rahotanni daga kauyen sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Alhamis da misalin karfe 2:30 zuwa 3:00 inda 'yan bindigar suka yi harbi biyu a saman iska kafin tafiya da shi. 

Da fatan Allah ya kubutar da shi cikin aminci.

Daga Jabir Kwaccido