Jirgin Soja ya kashe 'yan bindiga sama da 80 a Katsina
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta kashe sama da ƴan bindiga 80 tare da ƙona babura 45 waɗanda ƴan fashin ke amfani da su a jihar Katsina.
Wata sanarwa da rundunar sojin sama ta Najeriya ta fitar a yau Litinin, wadda ta samu sa hannun daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarunta, Edward Gabkwet, ta ce an kai harin ne a wata maɓuyar ƴan bindiga da ke ƙauyen Gidan Kare a ƙaramar hukumar Faskari da ke jihar ta Katsina.
Katsina na cikin jihohin Najeriya da ke fuskantar matsalar ƴan fashin daji masu kisa da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Sanarwa sojojin ta ce ta kai harin ne ranar Asabar a lokacin da ta samu rahoton cewa ƴan bindiga kimanin 100 sun kai hari a wani ƙauyen da ke da nisan kilomita biyar daga Gidan Kare, inda suka riƙa ƙona gidajen al'umma.
Ta ƙara da cewa da misalin ƙarfe 9:40 na daren ranar ne jirgin rundunar ya yi ruwan wuta a kan ƴan fashin dajin waɗanda suka taru a kusa da dabar Kuka Shidda, inda bayanai suka tabbatar da cewa an kashe sama da ƴan bindiga 80 da ƙona babura 45
managarciya