Gwamnatin Sokoto ta Sallami Sarakuna 15 a Jihar

Gwamnatin Sokoto ta Sallami Sarakuna 15 a Jihar

Gwamnatin Sokoto ta Sallami Saraakuna 15 a jihar da suka haɗa da Yabo, Dogon Daji, Tulluwa, Unguwar Lalle, Tambuwal, Wamakko, Illela, Kebbe da Alkalami.

Sauran uwayen ƙasar sun haɗa da Giyawa, Tangaza, Kalambaina, Gongono, Yar tsakuwa da Torankawa.

Sanarwar wadda sakataren yada labarai na gwamnan Sakkwato Abubakar Bawa ya sanyawa hannu ya ce an sauyawa Uban ƙasar Binji wurin aiki da Binji zuwa Bunkari,  in da Uban ƙasar Sabon Birni zai koma Gatawa.

Uwayen ƙasar Gagi da Kilgori da Kuchi za su yi zaman jiran kammala bincike.

Tsohon Magajin gari zai koma sarautar sa ta baya waton Sarkin Rafin Gumbi.

Haka ma sarautar ta mutum 7 an tabbatar da su cigaba da mulkinsu.