HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 37

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 37

HAƊIN ALLAH:

  

    Page 37


Kasa natsuwa Alawiyya tai, sai take ganin da ace ita ce da yanzu ta isko inda Jiddar take, hakan yasa ta koma hanyar ƙofar gidan tana kallon motocin dake wucewa cike da zumuɗin murna.
Da yake ɗan gari ne direban nasu Jiddah wanda Alƙali ne ya bata shi tare da gidan da suke zaune saboda ta gaya mai daga nesa ta zo shari'ar bata san kowa ba sai Yayanta daya rakota. Hakan yasa ya bata gida mai kyau da mota har da direbanta, ya ce hatta ɓangaren abinci da abin sha karsu damu duk ya ɗauke masu.
Ita dai taji daɗin hakan amma ta lura da yadda abokin tafiyar ta ke ta haɗe rai yana basarwa bata san dalilin hakan ba daga taimakonsu da Alƙali ya yi sai fushi yake.4


Suna isa gidan tun kafin direban ya gama gyara fakin ɗin motarsa Jiddah ta buɗe motar ta fice, abin da yasa tai taga-taga kenan zata faɗi ƙasa.
Lokaci guda Mustapha yai hanzarin fitowa daga motar ya riƙe ta daidai lokacin da Dr Falsal ya rugo da hanzarin sa don kai mata ɗauki, amma ganin wani ya riƙe ta sai ya buɗe ɓangaren direban ya cigaba da yi mai masifa yana zaginshi har da cewa da ya sake ya kada ta wallahi da sai ya ba shi mamaki.

Duk abin da ke faruwa ba wanda ya san me yake sai Mustapha, domin tuni Alawiyya da Jiddah sun haɗe sun fashe da kuka sun nufi cikin gidan suna rungume da juna.

A hankali Mustapha ya taka ya isa gaban Dr Falsal ya ba shi hannu suka gaisa, ya dube shi fuska ba walwala ya ce, "Tun a kotu na so na gabatar maka da kaina, saboda ka gabatar da Ni gun matarka kafin zuwanmu gareta tare da Princess sai ban samu damar hakan ba. Ni ne wanda zan auri Jiddah nan da lokaci kaɗan, kuma Ni ɗin Yayanta ne domin Jiddah jinina ce."
Ya saki hannun Dr Falsal ya nufi cikin gidan yana murmushin da shi kaɗai yasan me yake nufi da shi.

Suna zaune sun haɗe kai sai kuka suke Daddyn Alawiyya yana ta ba su haƙuri Mustapha ya shiga Dr Falsal na biye da shi a baya kamar ɗan jagora.

Kai tsaye hankicif ɗinsa ya janyo daga aljihu ya tsugunna gaban Jiddah ya ci-gaba da goge mata hawayen fuskarta yana cewa, "Sorry Princess ki daina kuka kada kanki ya zo yana ciwo ga kuma abin da ke gabanki. Ya dubi Alawiyya ya ce, "Haba Madam bai kamata ba ki biye wa Princess ba kui ta kuka a lokacin da godiya ga Allah ya kamata Ku ba yi ba, na ɗauka zan shigo in iske kun yi sujjada ga Allah ta nuna godiyar sa daya haɗa ku a lokacin da kuka cire rai da ganin juna?"

Alawiyya ta dube shi, duk da tana cikin yanayin kuka ta ji daɗin ganin shi tare da Jiddah alamar cewa shi ne mijinta da Daddy ya gaya mata a waya.
Tabbas tasan yana kulawa da Jiddah domin kallo guda ta fahimci yadda yake matuƙar kaunar Jiddah a idanunsa.

Dole su kai shiru, musamman da Jiddah da Mustapha ke tsugunne a gabanta saura kaɗan shi ma ya fashe da kukan ga dukkan alama.

Sake goge mata wani guntun hawaye da ya zubo ya yi, ya ce, "Don Allah Princess ki daina kuka idan ba so kike nima na taya ki kukan ba, kin san ban san kina kuka ko?" Ya ƙare tambayar da jefa mata wani marayan kallo.

Dole ta natsu amma suna riƙe da hannun juna kamar wasu yara ƙanana.

Alawiyya ce ta dubi Jiddah sosai ta sake fashewa da kuka tace, "Jiddah na jima cike da kewarki na neme ki na neme ki yadda baki tunani, sosai na damu kan ki dare da rana safe da yamma sai na zubar da ƙwalla na rashinki a tare da Ni, kukan ban san a wane yanayi kike ba nake dare da rana. Jiddah ina kika shige bayan mutumin nan ya so sace mu daren da muka bar gidan kallon wasan kwaikwayo a Kano?"

Jiddah ta sake fashewa da kuka sosai, ga mamakinsu sai suka ga shi ma Mustapha ya fashe da kukan kamar yadda take kukan.
A cikin kukan ta bata labarin kaf abin da ya faru ga rayuwarta bata ɓoye mata komai ba.

Babu wanda bai zubar mata da hawayen tausayi ba, musamman inda ta zo faɗin rasuwar Uncle Salim kowa sai da ya yi shasshekar kuka, tabbas Jiddah ta yi matuƙar basu tausayi.
Mustapha kuwa sai ya ji babu abin da yake so irin suna komawa ya aureta ya killace ta a gidanta ita kaɗai ya cigaba da wadata ta da rayuwar farin ciki ya goge mata mugun tabon da take yawo da shi na baƙin munafukin mijinta. So yake ya nuna wa duniya tana da gata ita ce ma kamar kowace mace koma ya ce tafi mata da dama gata.

Kuka yake kukan baƙin ciki da nadamar me yasa ya yi nauyin baki tun Jiddah na ƙarama bai fito fili ya nuna yana sonta ba? Me yasa ya yi nauyin bakin da Jiddah ta faɗa hannun mutumin banza? Ko da yake ya ɗauki hakan matsayin ƙaddarar rayuwarsu shi da ita domin shima ba abin da ya tsinta a rayuwar aurensa sai tashin hankali da ɓacin rai ko da yaushe cikin matsala yake ko da yaushe cikin nadamar aure yake.
Tabbas ya fahimci cewar soyayyarsu baki ɗaya ita ce ake kira da "HAƊIN ALLAH" saboda Jiddah ta bayyana irin mafarkin da take wanda shi ma yana yinshi tun kafin ya yi auren farko, sai dai shi ma bai taɓa ganin fuskar ko wacece yake gani suna rayuwar farin ciki ba. Kuma ko bayan aurensa duka na matansa uku bai daina wannan mafarkin ba sai ya ɗauka kawai don ya saka ma ranshi rayuwar farin ciki ne a gidansa yasa yake mafarkin farin cikin a barcinsa.

Dr Falsal kuwa zuciyarsa tamkar ta fashe don jin zafin abin da akai ka Jiddah, ji yake da ace yana da dama ba abin da zai hana shi kama Deeni ya ɗaure har igiya tai rara don ubansa.

Alawiyya ta ja ajiyar zuciya ta dafa Jiddah ta miƙe tsaye ta juya bayanta tace, "Na rantse da Allah ko da sama da ƙasa za su haɗe sai na je duniyar Deeni na nuna mai ƴancin ki na nuna mai gatanki , na nuna mai ko wacece Jiddar Iyami ƙawar Alawiyya!

Tabbas ba zan ƙasa a gwiwar bankaɗa rayuwarsa cikin baƙin cikin da ninka wanda ya bankaɗa ki!

Tabbas zai fahimci cewar ba kowace mugunta ake yi a zauna lafiya ba, wata muguntar idan akayi ta hambuɗe jin daɗin mutun take har lahira!

Waye Deeni? Wa ke gare shi? Waye zai tsaya mai? Me yake da shi? Tabbas lokacin amsar hukuncin sa ya yi kamar yadda na hukunta waɗanda suka azabtar da rayuwa a baya haka shima zan manta su Afnah nayi mai hukunci daidai da watsewar sa.

Ke bari ta Deeni hatta Safiya sai na gano duniyar da take na yi mata nata hukuncin cin amanar da tai maki.

Jiddah ina yafiya ina kauda kai haka zalika ina barin halas don kunya amma a kanki ban san ko da kalma guda ba daga jerin su ba.

Lallai ne duniyar farin cikinki ta buɗe yayin da ta baƙin cikin duk wanda ya saka ki a damuwa zata kama.

Jiddah sai dai ki yi haƙuri amma a wannan karon a wannan lokacin ba ruwana da dangantaka ko jini kan hukunta duk wanda hukunci ya zo kansa a kanki...

"Tabbas ina bayanki , Ni ma na shirya tsab domin nema wa Princess haƙƙinta, dole ne Princess tai farin ciki, baƙin cikin ya isa haka, ya isa haka! Yana magana yana kuka yana dukan kujera.

Dr Falsal shi da Daddy sai su kai shiru domin abin ya fi ƙarfinsu. Dr Faisal ya ja ajiyar zuciya ya dinga magana a zuciyarsa, da lissafin abin da zai fissheshi kan matsayar sa da Jiddah masoyiyarsa ta  HAƊIN ALLAH. Domin da ya yi niyyar zai gayama Jiddah yana sonta zai aureta a yanzu a gaban kowa, sai kuma yaga bai kamata ba, yana da kyau ya fara samun zuciyarta da amincewar ta sannan sai ya tunkari matarsa da wannan babban al'amari da ya tunkare shi a rana guda, ko da yake ai kowa yasan wannan shi ne ake kira da HAƊIN ALLAH, sun jima suna neman juna ba su gana ba, sai bayan wasu shekaru masu dama, wanda kuma ya bayyana ɗaya a gidan aure ɗaya kuma babu aure, tabbas ba zai bar wannan damar ba. Ko da yake ai taimakonsu ma zai idan ya haɗa su aure gida guda za su ji daɗin yin abin da ya kamata kuma komai nasu sai yafi daɗi da kyau suna gida guda tare da juna hakan ma babbar sa'ar rayuwa ce su kai ai. Kamata ya yi ma su gode mai su zama masu yi mai alheri saboda wannan kyakkyawan aiki da ya yi masu mai daɗin gaske. Murmushi ya saki na samun gamsuwa da tunaninsa.

Alawiyya ta zauna tana duban Jiddah tace, "Bari na baki nawa labarin bayan rabuwarmu Ni ma, domin na shiga gararin rayuwa da masifa tare da tashin hankali iyakar nawa nima, sai dai Ni nawa ya sha bambam da naki, labarin saboda Ni na sha wahala ne a hannun dangin mahaifina saboda gunsu ta na tashi , wanda wahalar ce tasa na bi dare na gudu uwa duniya a can ne na gamu da mahaifina yana nema na shi ma.

      Kano 

Tun da ya fito daga gidan Hajjo ya rasa inda za shi, saboda bai san kowa ba a garin, kuma bai da ko waya balle ya kira danginsa ya ji ko suna da ƴan'uwa a Kanon ya je gunsu.

Haka yai ta yawo ga yunwa ga ƙishirwa na azabtar da shi, ganin ba Sarki sai Allah yasa ya fito da ƴan kuɗinsa ya nemi abinci ya ci ya sha ruwa ya kwanta ƙasan wata rumfa don ya huta gajiyar dake jikinsa. Nan da nan barci ya kwashe shi. 

Ashe rumfar wata mahaukaciya ce ya kwanta yana barci bai sani ba, ita kuma ta tafi neman yarinyarta da wani mutum ya ƙwace mata, kun san mahaukata da son ƴaƴansu, don haka tana dawowa taga Deeni kwance wajenta sai taga kamar wanda ya ƙwace mata yarta ne, don haka ta samu ƙaton dutsenta ta sauke mai shi a fuska. 

Kawai azabar zafi ya ji wadda bai san ko ta miye ba da farko sai daga baya sai ya fahimci ashe ransa ne ke niyyar fita, domin ance mai duk lokacin da rai zai fita ciwo na musamman ke ziyarar mutum wanda bai taɓa jin irinsa ba.

Hakan yasa ya ɗauka ajalinsa ne kawai ya zo, don haka ya sadaƙar kawai.
Ita kuma mahaukaciyar ganin ya ƙi tashi ya ruga kamar yadda duk wanda ta jefa yake rugawa sai ta ɗauka ko wani abun zai sake ƙwace mata don haka ta sake ɗaukar wani tsohon kwano dake aje cikin tarkacen kayanta ta buga mai shi.

Tabbas daman yasan shi da shiga aljanna sai Jiddah ta yafe mai, domin Allah bai yafe haƙƙin wani akan wani daman ya sha ji gun Malamai.

Mutane ne suka lura da abin dake faruwa, suka yi hanzarin shiga tsakaninsu suka ƙwace shi lokacin duk Deeni ya gama galabaita sosai jini duk ya ɓata mai jiki, a haka ne wani ya samu damar ɗauke sauran kuɗin dake jikin Deeni.

Bayan kowa ya watse daga gun ne Deeni ya lallaɓa ya tashi ya isa gefen wani gajeri da mutane ke ta gyare-gyaren motoci, mashina, yana isa ya nemi taimakon abin da zai ci, da yake sun riƙe da yadda mai shagon ke son taimakon mutane hakan yasa suka ba shi abinci da ruwa suka kawo ƴan canji suka ba shi , ya yi godiya sosai ya kama hanyar komawa gidan Hajjo.

Hajjo ta ɗauka Deeni ya tafi don haka ta zauna tana ta jajanta lamarin har tana cewa ba mamaki ba ko wani mugun abin ya ƙunso ya kawo wa Jiddah Allah Ya ƙaddara bata nan don mugun nufinsa ya koma kansa.

Jin sallamarsa yasa Hajjo zabura ba kamar data ganshi cikin mayuwacin hali duk jini a jikinsa. Cike da tashin hankali take cewa, "Yau naga ikon Allah! Wata masifar ka je ka kwaso ka dawo min nan kuma? To wallahi na rantse da Allah ka zo ka fice min daga gida kafin na kira a zo a fitar min da kai daga gidana kafin ka haifar min da wata tsiyar, domin kai duk inda kake ba a saka ran ganin alheri ka zama abin da ka zama, don haka ba dai gidana ba wallahi can ka je ka nemi inda matar taka take ku daidaita amma ba dai nan gidan ba."

Deeni ya tsugunna hawaye na zubowa kamar ba Deeni ba, ya dinga ba Hajjo haƙuri, yana cewa, "Don Allah ki yi haƙuri Hajjo ki ban dama na zauna a nan na jira zuwan matata, sai mu tafi tare don Allah ki min wannan alfarmar don Allah."


Hajjo ta zaro idanuwa waje tana ƙare mai kallon mamaki, kamar kuma na tsoro tace, "La La La! Wallahi ba zan lamunce ba, ka manta lokacin da Jiddah ta haihu muka je suna wulaƙancin daka zuba mana ne? Kiri -ƙiri ka dinga tsallake mutane don azabar rashin kunya da nuna mana kai tataccen marar mutunci ne ka dinga kwana cikin ɗakin yarinyar jego ka hana uwarta kwana da ita cikin gata da mutunci kamar yadda ake ma kowace yarinya?"

Deeni ya sake sadda kansa ƙasa yana cewa, "Wallahi duk sharrin shaidan ne Hajjo, amma yanzu mun rabu insha Allah ba zan sake hakan ba, idan ma kin ce ta dinga dawowa nan gunki tai wankan jegon wallahi da kaina zan kawo maki ita na rantse maki da Allah Hajjo ba zan karya alƙawarin nan ba."

Hajjo ta sake haɗe rai sosai ta dube shi tace, "Wai ni kam ko kaima ka fara ƴan shaye-shayen nan ne Deeni? To idan ba ɗan shaye-shaye ba waye zai maganar da kai? Allah na tuba ko miji Jiddah ta rasa ai gwara ta ƙare rayuwarta tana gadin masallaci da dai ta koma gidanka."

Deeni ya dubi Hajjo ya ce, "To don Allah ki kira min ita a waya naji me zata ce, sai na tafi idan tace na tafi, duk da nasan da wahalar gaske JIDDAHH ta ji na zo har Kano gunta batai farin ciki ba."


Hajjo ta taɓe baki ta fito da wayarta ta kira wayar Jiddar sai dai har ta tsinke bata ɗaga ba, don haka ta kira ta Mustapha tana shiga kuwa ya ɗauka. "Yawwa, don Allah ka ba Jiddah wayar nan na kira layinta bata ɗauka ba, tai ma Deeni magana ya bar min gida wai zai jiranta har ta dawo a nan gidan su tafi tare Ni kuma ba zan yadda da hakan ba."


Duk lokacin da aka ambaci sunan Deeni tafasa zuciyarsa ke yi, duk lokacin da akai maganar Deeni jin tsanarsa yake ƙara ji, duk lokacin da ya tuna shigár saurin da Deeni ya yi mai haushi yake ji ba kamar da ya aure ta ya kasa yi mata adalci abin yafi yi mai ciwo sosai.  Hajjo tace, "Kana jina kuwa Mustapha?" 

Deeni ya dubi Hajjo da alamar damuwa fal a fuskarsa ya ce, "Wai waye wannan Mustapha da yake tare da ita ne? Ko rannan fa shi kika kira madadinta, wa ya bata ikon tafiya da wani ƙato har wani gari?"

Hajjo dai bata tanka mai ba, amma da yake wayar a amsa kuwwa take Mustapha ya ji abin da Deeni ya ce, shi ma a matuƙar fusace ya ce, "Kai Sakarai tsaya matsayinka ba ruwanka da harkata, idan ka sake ka ce zaka yi min sakarci tabbas Ni ba irin Salim bane ba tsab zan koya maka hankali.

Kuma daga yanzu kada ka sake ambatar sunan Jiddah balle nawa a bakinka, domin daga Ni har Jiddah babu sa'anka, shawara guda zan baka ita ce ka ruga ka ɓoye domin gatan Jiddah ya bayyana ta ko'ina wanda yana gab da yi ma hukunci iyakar abin da ya shuka mata.
Kuma ka sani Jiddah ta barka kamar yadda tabar cikin mahaifiyarta don haka kai ta kanka kafin lokaci ya ƙure maka."


Hajjo ta amshe, "Yo shima ai yasan ƙarya ce ace Jiddah zata koma gidansa, ta koma ya ida kashe ta ko? Ban taɓa ganin mugun miji macuci ba irin shi ba, shi ne yanzu zai kwaso jiki duk dauɗa wai ya zo maida Jiddah. To wannan karon ko ubanta bai isa ya ce zai iko da ita ba ya maida ta gidanka ba, idan kuwa ya ce zai maidata to kotu ce zata raba mu da shi."

Duk Mustapha najin me tace, don haka ya ƙara da cewa, "Hajjo maza ya bar gidan nan kuma kada ki sake kirana don Allah kan shi." Ya kashe wayarsa yana jin matuƙar takaicin Deenin.

Jiddah na tsaye yake wayar da farko ta ɗauka da iyalinsa yake wayar sai kuma ta fahimci a kan ta yake wayar, kawai ta yi mamaki da taji ya ambaci Deeni ba dai Deeni ne ya dawo maidata ba? Tabbas wannan lokacin zata ba iyayenta mamaki idan har suka ce za su maidata gidan Deeni.  Lokacin ya sauya, ya kamata ta fara ƙwatarwa kanta ƴanci tun a gun iyayenta kafin ta je ga kowa, waye Deeni? Ita daman can ba don shi take ba, kawai tayi biyayya ne ta aure shi don kawai ta zauna lafiya da iyayenta, duk da cewar akwai zaɓin ranta a zuciyarta amma haka ta manta da shi sai dai a mafarki kawai take ganin soyayya ba a zahiri ba. Juya wa tai ta koma ba tare da ta ce komai ba, da kallo Mustapha ya bita kafin shi ma ya koma cikin falon don suna zaune ne aka kira shi, yasan jin ya ambaci sunan Hajjo yasa ta biyo shi.

Hajjo ta dubi Deeni tace, "kunnenka ya jiye maka abin da aka ce, don haka ka ga shigewa ta ɗakina idan ka so ka tafi idan ka so ka zauna nan tun da taurin kai zaka nuna min irin yadda kake nuna ma jiddar."

Ta shige ɗakinta ta turo ta bar shi zaune a nan ya rasa mafita, jiki a sanyaye ya tashi ya fice daga gidan yana jin matuƙar takaicin rayuwarsa.

Bai san inda za shi ba haka bai da ko sisi balle ya nufi tashar mota, abin ya yi mai yawa shege da hauka. Ƙarshe ya nufi kasuwa ga jikinsa ba ƙarfi ya dinga neman dako yana yi ya samu ya tara kuɗin mota ya koma gida ya jira zuwan Jiddar yasan ta tana da haƙuri kuma tunda take da shi bata taɓa neman ya sake ta ba, don haka yasan idan ya maidata zata koma cikin farin ciki.
Sai da ya yi sati uku sannan ya haɗa kuɗin motar a tasha yake kwana shi ma da ƙyar ya samu aka bar shi yake kwana a tashar.

Ranar da zai tafi sai da ya dinga zubar da hawaye, duk ya yi baƙi ya rame ya fice hayyacinsa ba lallai bane ka gane shi farat ɗaya ba, saboda ya sauya talauci ya ce mai salamu alaika ga alama kuma ya amsa sallamar.

Cikin mota haka ya dinga hawaye har aka sauka, kai tsaye gidansa ya nufa ya iske wani tashin hankalin domin ɗaki guda ya faɗa kuma an sace ƙofofin an ɗauke mai abubuwa da yawa hadda katifarsa da sauran abubuwan amfaninsa.
Sai kukan ya tsaya kawai ya zauna ya yi shiru yana kaf rayuwarsa da Jiddah a cikin gidan, kenan dai alhakin Jiddah ne ke bibiyarsa? Kenan Jiddah bata yafe mai ba shi yasa bala'i ke tunkararsa ko da yaushe? Yanzu ina zai ga Jiddah ya nemi afuwa gunta? Tabbas yana buƙatar ganin Jiddah don ta yafe mai duk abin da ya yi mata su koma da rayuwarsu cikin aminci da kwanciyar hankali, zai dinga kula da ita iyakar ƙarfinsa ba zai sake mata abin da bata so insha Allah.

Haka Deeni ya koma rayuwa a cikin ɗaki guda tal ba katangu ba komai sai wannan ɗaki guda, duk abin duniya ya dame shi ya rasa aikin da zai samu ko na abinci ya dinga samu sai dai kullum yana bin gidajen danginsa wani gidan a ba shi wani gidan ai kamar ba a san da zuwansa ba.

Duk wanda yasan Deeni idan ya ganshi yanzu sai ya tausaya mai, domin ya koma kamar mahauci tsabar wahalar rayuwa, icce ya ke zuwa daji ya yo da ƙyar yake samun mai siyen iccen wani lokacin ma bai samun mai siyen iccen sai dai ya kawo gida ya aje kuma sai yara su sace shi.

Iyakar ganin rayuwa tabbas yana ganin rayuwa abin ba a cewa komai sai dai abi shi da Allah Ya kyauta..
Yanzu kwata-kwata babu ma maganar wani aure a gabansa domin bai da abin yin auren bai da inda zai aje matar, hakan yasa ya fara shawarar ɗibar gidan ya saida ko kuma ya saida gidan baki ɗaya ya samu ko na ƙasa ne ta siya ɗan ƙarami sauran kuɗin sun ishe shi ya biya sadakin Jiddah ya sai mata ƴan kayan fita biki ya bata su zauna ta ci-gaba da sana'arta tana samun kuɗaɗen ci da su cikin kwanciyar hankali.

Wannan shawarar ya aminta da ita, don haka ya saka gidan a kasuwa nan da nan kuwa aka saida shi aka ba shi kuɗin ya ce a samar mai ƙaramin gida zai siya kamar yadda ya yi shawara kafin ya saida gidan.

Sai dai yana kwance cikin dare ɓarayi suka diro mai su kai mai dukan tsiya suka amshe kuɗin gidan duka sukai tafiyarsu suka barshi a kwance rai hannun Allah.

Sai da asuba mutane suka shigo su kai mai jaje suka fice kowa na cewa alhakin matarsa ne ke bibiyarsa wasu ma cewa su ke kaɗan ya gani ai.
A hankali Deeni ya koma shiru-shiru marar magana ya daina zama cikin mutane ya daina aikin komai sai zama ɗakin mahaifiyarsa kawai, sai wanda ya ga Allah cikin mutanen gidan kawai ke ba shi abinci wani lokacin.

                

             KADUNA


Alawiyya ta dube su duka tace, "Lokacin da muka rabu da ke na ruga ban zame ko'ina ba sai wani shago dana gani a rufe na shige na runtse idona tsabar tsoro yasa barci ya kwashe Ni ban sani ba, sai da safe gari ya waye sannan naga wasu mutane a gabana suna min kallon mamaki, Ni kuma na bi su da kallon tsoro domin na ɗauka wasu ya kira min su kama Ni. Sai dai a hankali na fahimci ba wancan mutumin bane domin naji suna tambayata daga ina nake? Ko buki muka zo na ɓace? Ina ne gidanmu? Hakan yasa na fasa kuka na kama kiran sunanki domin sai a lokacin hankalina ta komo jikina na tuna kuma baki tare da Ni, don haka na tashi da gudu ina kuka ina kiran sunanki sai wannan mutumin ya sa sauran suka riƙe Ni suka ban kalaci na ƙi ci duk da ina jin yunwar amma na kasa samun natsuwar cinsa tunani nake kada ace mutumin ya kama ki don haka na kasa samun damar cin abincin da suka ban. Ganin hakan yasa suka ce na ci abincin su kuma za su je su nemo min ke. Sai a lokacin naci abincin ina kuka duk da hakan, bayan  na gama ci ne ya tambaye ni daga ina nake ? Nace mai gada gidan marayu muke Ni da ƴar'uwata muka gudo neman iyayenmu saboda ance mana iyayenmu na da rai sune suka kai mu ajiya gidan marayun.

Intakaice maki labari sai da muka wuni muna nemanki bamu ganki ba har lokacin tashi ya yi gun aikinsu ba ki ba labarin ki don haka sai na saka a raina kema kin yi wani wajen ban ji a jikina ba cewar wani abu ya same ki ba.

Da suka rufe shagon ne wanda naji suna ambata da yaron Oga ya dubeni sosai ya ce, " Ya sunanki?" Na amsa ma shi da "Alawiyya ita kuma ƙawata Jiddah sunanta." Daga wane gidan marayu kuka fito? Sanin cewa ban san wani gidan marayu ba yasa nace mai daga Lagos muke, amma Yau kwanan mu biyar nan garin."
"Kwana biyar a ina kuke kwana to?" 
Na ce mai a cikin masallaci muke kwana da asuba kafin Ladan ya kira sallah mu ke ficewa daga masallacin."

Girgiza kanshi ya yi ya ce "Mu je na kai ki gida, amma sai dai ki sani nima ɗin kamar ki nake domin ba nan ne iyayena suke ba, daga almajiranta na samu uban gida mai mutunci ya maida Ni yaronsa a garejin nan to yanzu bai nan ya tafi neman wani abu kuma zai jima bai dawo ba, idan kin amince zan kai ki gidansu ki zauna nima a can nake zaune kafin ya dawo asan abin yi." 
Ban da mafita don haka na amince muka tafi gidan tare, tun daga waje nagane gidan mutane da dama ne a ciki ganin yadda mutane ke fitowa wasu na shiga, ko da muka shiga gidan sai zatona ya zama gaskiya, domin naga ƙofofi kashi daban-daban a cikin gidan, ƙofar wani gida muka shiga, a mamakina shima ƙofa uku ce a cikinsa.
Muna shiga cikin gidan da sallamarsa ina biye da shi a bayansa, wata mata dattijuwa na zaune ga alama abinci take rabo ta ɗago kai ta kalle mu ta ci gaba da abin da take.
Har ƙasa ya duƙa ya gaidata sannan ya yi mata bayani na ya tsince Ni ne a shagon Oga shi yasa ya kawo Ni nan kafin Oga dawo.

Dattijuwar ta watsa mai harara tace, "Ban san baka da tunani ba sai Yau, kai ban da rashin tunani me zai sa ka ɗauko yarinya haka kawai ka kawo mana ita a gida wai ka tsintso ta? To nan gidan marayu ne da zaka kawo min ajiyar yarinya? To ba dai nan gidan ba, tun kafin duhu ya ida maza ka kama gabanka ka maida ta inda ka ɗauko ta... Wani dattijo ne ya yi sallama ya dube ta ya girgiza kai sannan ya dube ni ya ce, "Wai ni Saude yaushe za ki san Annabi ya faku ne? Yanzu ko abin da ya faru ga Autanki bai ishe ki ishara ba? Yanzu ke ba za ki zama mutunniyar kirki ba ko Allah Ya dubi halayenki ya amsa maki addu'arki ta bayyana maki inda Autanki yake ba? Haba Saude miye don kin riƙe wannan yarinyar? To idan ke ba za ki riƙe ta ba Ni na amshe ta zan riƙe ta, don haka ta zauna da miyau na a cikin gidan nan."

Ya shige wani ɗaki yana yi ma Saude fatan shiriya.

Harara ta banka mana mu duka ta girgiza kai tace, "Ka kyauta Mansur dama don kasan da cewa ya kusa shigo wa gidan shi yasa ka kawo ta, to ta zauna gata ga gidan nan indai nice ta zauna mu gani." Fuu ta shige ɗaki ita ma aka bar mu tsugunne Ni da Mansur da sai yanzu na ji sunansa ma.

Dattijon ne ya sake fitowa ya ce, "Mansur je ka abinka, Allah Ya yi maka albarka Yasa ka gama lafiya, ka barta nan zata ci gaba da zama muga abun da hali ya yi ɗin, ai ɗa na kowa ne."

Mansur ya dube ni sosai da alamar tausayi ya ce min, "Alawiyya ki yi haƙuri don Allah ki zauna lafiya da mutanen gidan nan, ka da ki yi rashin ji ko ki raina mutane ki zama kina bin kowa yadda yake so, za ki ji daɗin zama a gidan kin ji ko? Sannan insha Allah zan dinga taimaka maki nima da abubuwa sosai da yardar Allah za ki gane iyayenki wata rana insha Allah."

Wani ɗaki aka ce na shiga, na shige jikina sanyi ƙalau ina tunanin yanzu kuma wace rayuwa ce zan yi a cikin gidan nan? Ko wace rayuwa kuma Jiddah ke yi yanzu haka ita ma a inda ta samu kanta? Tabbas indai Jiddah na garin nan to zan cigaba da neman ta har na ganta, ba zan yadda mu rabu da juna da Jiddah ba, dole mu rayu waje guda gida guda saboda mu ɗin kusan ƙaddararmu guda ce.

Washegari sai ga Mansur da kayan gwanjo kusan kala biyar ya kawo min, har da takalma da hijabi, sai ga maigidan shi ma ya kawo min wasu kayan.
Sai dai duk abin nan matar gidan ko kallo ban ishe ta ba, abu biyu ke haɗa Ni da ita harara da tsaki sune kawai abin da take bina da su.

Nan da nan labari ya kacame a cikin gidan an kawo baƙuwa a sashen Inna Saude ba a san inda danginta suke ba, sai ga gidan na cika da mutane sun zo ganin baƙuwa.

Daga nan sai gulma ta fara tashi wasu na cewa ai Mansur ƙarya yake ɗiyarsa ce ta yawon ta zubar kawai ya samo ya kawo ta nan ya yi ƙarya, wasu kuwa cewa su ke Inna Sauden aka raina da aka bata riƙon shegiya.

Nan da nan na shiga matsananciyar rayuwa a gidan, yaro da babba kowa ya raina Ni, ban da ikon taɓa abu sai a ce na aje shi tun da na iyayena bane ba.

Inna Saude tafi kowa takuramin tafi kowa nuna min tsana tafi kowa nuna min tsangwama. Babu yadda magidan bai ba amma ina abin ya fi ƙarfinsa, dole tasa nake zuwa Gareji ina wuni gun Yaya Mansur saboda idan ba can ba babu inda nake samun sauƙin rayuwa.

Dama kin san na ƙware da iya aiki tun horon Iyami don haka aikin abincin gidan sam bai damu ba, nakan gama komai kafin ta ankara na gama duk wani aikin da nasan nawa ne a cikin gidan.
Sai kuma ta tsiro da cewar sai na dinga bin sauran gidajen cikin gidan ina masu shara da wanke-wanke ina ɗebo masu ruwa kullum tunda abincin da nake ci ai daga hannun ɗan'uwansu yake fitowa
Hakan yasa aiki ya ƙaru sosai a guna, kaf gidajen da ke cikin rukunin gidan nan babu mai tausaya min sai Inna Fattu da ɗanta guda ɗaya Faisal sune kawai ke matuƙar nuna min tausayi suke matuƙar taimaka min ta hanyar sakani karatu duk da sai da akai tashin hankali gun kai Ni makarantar boko da islamiyya amma haka suka daure na cigaba da zuwa.

Sai kuma Inna Saude ta ce ita ba zata amince ba, talla zata dinga ɗora min ta gyaɗa da goro tunda ba iyayen da za su sai min kayan aure gare Ni ba idan na tashi aure ko da yake waye ma zai auri shegiyar da ba a san ko da mutum guda ba a cikin iyayenta ba? Na kan yi kuka na gode wa Allah duk lokacin da Inna Saude ko wasu suka kirani da suna shegiya.

A haka dai na yi shekaru biyar a gidansu Inna Saude cikin mayuwacin halin gaske, ban da gata ban da mai min gata sai su Faisal da mahaifiyarsa suma sai da Inna Saude ta shiga ta fita ta raba mu , amma ta kasa raba Ni da Faisal duk da cewar Faisal jikanta ne amma ta kasa raba Ni da shi, ko da yaushe cikin kulawa da Ni yake.

Ban kuka sai idan bai nan, da ya dawo zai shigo shashenmu tunda Ni an hanani zuwa sashensu, haka Inna Saude zata dinga mai faɗa amma ya yi kunnen uwar shegu da ita ya cigaba da koya min karatu ko ya tambaye ni abin da nake so.
A hakan kullum dai na je nemanki, ko da yaushe sai na ba Faisal labarinki babu wanda bai san labarin Jiddah ba a waɗanda nake shiri da su.

A gefe guda kuma na dage da zuwa makaranta domin ban manta da alƙawarinmu ba na zama manyan Lauyoyi ba don kawai mu dinga hukunta iyayen dake haihuwar yara suna watsi da su ba, da mazan da ke auren mata suna wulaƙanta su har su saka su tsallake yaransu kan dole su bar gidan su kuma ba iya riƙe yaran za su yi ba.

Hakan yasa ko da yaushe nake gaya ma su Yaya Mansur Ni fa Lauya zan karanta, ina son na zama Lauya, ina son na ganni da kayan Lauya.

A cikin taskun musgunawar Inna Saude da sauran masu tsoron ta na gama primary na shiga Secondary har a lokacin ina fuskantar barazana sosai gun Inna Saude da sauran mutanen gidan har ma dana waje wasu da dama da sunan shegiya suke kirana.
Tun abin na damuna har ya daina damuna na haƙura amma na saka a raina duk sanda na gama karatu zan bazama duniya neman Jiddah da iyayena sannan zan zama babbar Lauya na dinga kare marassa ƙarfi na dinga bi ma yara haƙƙinsu gun iyayensu.

Lokacin da na gama Secondary lokacin Allah ya yi wa mijin Inna Saude rasuwa, a lokacin kuma Faisal yana ƙasar waje karatun Likitanci, don haka sai komai ya tsaya min, na gama karatu ina son cigaba ban da wanda zai saka Ni makaranta haka zalika abubuwa da yawa sai ƙara faruwa suke a gidan.

Hatta kai ta kawo ba a bani abinci a gidan duk da cewar nice ke girkawa amma ba a ban, ina ji ina gani Inna Saude zata kira almajiri ta ba shi abinci ga Ni ina jin yunwa amma bata ban. Sai dai na je gareji gun Yaya Mansur ya sai min abincin, to shi ma da yake ya yi aure an kai ma matar zugata wasu ma suna ce mata aurena zai sai ta tsane Ni don haka bata bari ko da wasa Yaya Mansur na zuwa gida balle ya ban wani abu idan na je kuma gidansa jikin garejin yake tana yawan leƙowa tana gani na zata fito ta dinga masifa tana zagina sai na bar wajen.

Ban san ya akai ba, sai aka wayi gari shi ma Yaya Mansur bai san gani na dana je yake kora ta ya ce ba zan kashe mai aure ba na kama tsagina.

Ƙarshe dai ya zazzage Ni ya tara min mutane ya ce kada na sake nuna na san shi ma.

Hakan yasa naga dacewar haɗa kayana na kama gabana ba mamaki na gano mahaifiyata ko mahaifina.

Cikin dare kuwa na haɗa na kayana nabi dare na gudu na bar gidan ina kuka ban san ina zan je ba.

Tashin farko naji baki ɗaya Kano ta fice daga raina, sai na ke jin kuma duk yadda akai ita ma Jiddah tabar Kanon don haka zaman Kano ya ƙare gareta ita ma.

Ina zuwa tasha na rasa motar da zan hau sai naji ana ambatar Sokoto, don haka sai na ji na amince da zuwana Sokoto kai tsaye na shige motar ina jin na yi bankwana da Kano har abada a raina.


Lokacin da muka isa Sokoto na rasa inda zan sauka sai na tambayi gidan mai unguwa, aka nuna min gidan kai tsaye na tafi, na ji tsoron kada in sake faɗawa gidan mutane irinsu Inna Saude amma kuma sai zuciyata ta dake na isa gidan cike da ƙwarin gwiwata.

Tsoho ne sosai mutumin bayan mun gaisa na ba shi labarina duka ban ɓoye mai ba, ya tausaya min sosai ya ce , "Tabbas kin sha wahalar rayuwa yarinya, insha Allah za ki ɗaukaka kuma za ki haɗu da iyayenki da yardar Allah. Amma ina so ki sani Ni ban da mata balle na she ki wajena amma zan kai ki gidan babban Hakimi insha Allah can za ki zauna lafiya ba tare da wata matsala ba, saboda gidan ɗan'uwana ne.

Haka akai kuwa, ya shirya muka nufi gidan  babban Hakimi bayan mun gaisa ya gaya mai komai kamar yadda na gaya mai, Hakimi daman tunda na zauna yake kallona yana murmushi yana lashe baki ya ce, "Ai ba komai nan ne ma ya kamata ta cigaba da zama ai, kuma zai saka ta makarantar boko ta cigaba daga inda ta tsaya ɗin.

Sosai naji daɗin maganarsa. Aka kira wani aka ce ya shigar da Ni gidan ya kaini gun Hassu ya ce taban waje ɗakinta zan zauna.

Matar mai kirkin gaske, ganin farko da ita na ji ta zauna daram a raina kuma naji ina matuƙar ƙaunarta a raina kamar naga mahaifiyata haka naji.

Ita ma haka ta saki fuska cike da fara'a ta tarbeni ta kawo min fura ta kawo min abinci, tana ta cewa na ci.

Saida na ci na ƙoshi sannan na bata labarina kaf. Kuka take sosai tana ƙarawa, ƙarshe ta bini da addu'ar Allah Ya bayyana iyayena a duk inda suke.

Zamana gidan Hakimi ya yi min daɗi sosai, domin ba tsangwama ba kyara komi nake so shi Baba Hassu ke yi min. Duk da akwai sauran mata har uku a gidan na lura ba ruwan Baba Hassu da su, sune ma suke yawan haye mata amma bata tanka masu, suna yawan tsokanarta amma bata nuna masu ta gane ma.

Gani na ma sun so su ji inda ta samo Ni amma ba damar hakan dole suka koma yi mata habaicin  haihuwa.
Sai dai kuma sam ban bari sun ga wajen kwana na ba balle su raina Ni, duk sadda su ka nemi taka Ni rufe ido nake na yi masu rashin mutunci domin nayi alƙawarin ba zan sake bari wani ya cutar da Ni ko ya wulaƙanta ni ba.

Da farko sun kai ƙarata gun Hakimi amma sai ya rufe ido ya ci masu mutunci ya ce masu a kaina zai iya ɓata masu rai don haka su kiyaye ni.

Dole suka shafa min lafiya suka koma kan Baba Hassu da rashin mutuncinsu don haka sai na sake nuna masu nan ma ban yadda ba, domin Baba Hassu tamkar uwata ce duk wadda ta ci mata mutunci sai na yaga mata rigar daraja a gidan.

Sai dai inda Gizo ke sakar guda ne, Hakimi ya matsa min duk dare sai ya shigar min ɗaki idan ina barci, yai ta kallona yana lashe baki, bai taɓa tada Ni ba ko taɓa Ni ba amma tabbas ina ganinsa tsaye kaina yana kallona.

Hakan yasa na shida tashin hankali sosai domin zuciyata ta fara rawa kan Hakimi, me yasa yake zuwa ɗakina cikin dare? Kallon me yake min yana lashe baki? Sune tambayar da nake yawan yi wa kaina ban san amsar su ba.

Hikimi kuwa tun da yaga Alawiyya yake jin matuƙar sha'awarta azuciyarsa domin yasan dai ba aurenta zai ba, saboda matansa huɗu cif don haka ba maganar ƙara aure, koma ba hakan ba yasan yarinyar ba zata taɓa amincewa ba ya aure ta ba, da yasan zata amince da babu abin da zai hana ya saki matarsa guda ba ya maye gurbin ta da Alawiyyar ba.

Duk lokacin da ya shiga ɗakinta cikin dare sai ya samu kan shi da kasa iya aiwatar mata da komai sai kallo yana jin nishaɗi sosai a zuciyarsa.

Duk lokacin da ya shiga ɗakin yana shiga ne da zummar ya aiwatar da ƙudurinsa kan yarinyar amma sai ya kasa koda ɗora yatsansa a kanta. Ya rasa yanda akai hakan ke faruwa sam. Ga wani irin kyau da yarinyar ke ƙara yi mai amma ya rasa me yasa yake kasa cimma burinsa kan ta.

Ni kuma a ɓangare na sai na samu kaina da jin me zai hana na gaya ma Baba Hassu abin da ke faruwa na zuwan Hakimi ɗakina cikin dare? 

Don haka na same ta ɗakinta na gaya mata abin da ke faruwa. Sosai ta razana na lura maganar ta girgiza ta sosai amma sai ta dake don ina wajen ta ce min, "Ki yi haƙuri Alawiyya zan dakatar da faruwar lamarin insha Allah."


Daren ranar kamar yadda ya saba, ya shigo min ɗaki sai dai Yau ga dukkan alama da ƙarfinsa ya shigo don yana shigowa ya maida ɗakin ya rufe har da sakata.  Ya tasanma gadona haiƙan da wata kwalba a hannunsa yana niyyar watsa min abin da ke cikin kwalbar.

Baba Hassu dake ɓoye cikin toilet ɗin ɗakin Alawiyya ta fito ta kaɓe kwalbar ta dube shi cike da ɓacin rai tace.
"Na gode wa Allah da bai azurtani da samun zuri'a da kai ba, ashe daman baka da imani har irin haka? Tabbas a Yau zama na da kai ya ƙare tunda ba mutumin kirki bane ba kai, daman ina zaune ne a cikin gidan nan saboda kai tunda kai ma baka da halin kirki to mun raba hanya.
Ya dube ta cike da ruɗani kan fuskarsa, sai kuma ya ce, "Kin yi wauta mai girman gaske Hassu da kika jefa kan ki a cikin abin da babu ruwanki, ya kike da ita ne? Kar ki manta ni ne na kawo maki ita da baki san ta ba sai da na kawo maki ita.

Don haka duk abin da naga dama zan yi da ita ke baki isa ki hanani ba. 
Ya sake ɗauko kwalbar zai watsa min duk da ina zaune ina kallonsu ina jin duk abin da suke cewa kuma.

Baba Hassu ta sake buge kwalbar ai sai kawai Hakimi ya shaƙe ta ya buga mata kai da bango, nan take jini ya fito ya sake ta ƙasa tana kakarin mutuwa, sauri ya fice daga ɗakin, cikin kuka na rumgume Baba Hassu amma sai ta ce min da ƙyar, "Ki yi hanzarin guduwa domin dawowa zai kuma idan ya dawo sai ya cimma burinsa Ni kam nasan mutuwa zan, amma idan kika cika burinki na zama Lauya ki bi min haƙƙina domin ban da kowa duk duniyar nan, dangina sun mutu a wani hatsarin da akai. Na takaice maki labari dai irin labarin da tsohuwa ta bamu Ni da ke ta gaya min ya faru da su, ashe ɗiyar Yayan Mamata ce ita. Nan Ni ma na bata labarin mahaifiyata Fatima tai murmushi duk da halin da take ciki tace "Allah na gode maka, da zan mutu bayan naji labarin ahalina, tabbas to za ki ga mahaifina da sauran danginmu don Allah ki ce su yafe min... Cak ta tsaya da maganarta na taɓa ta naji shiru na kira sunanta naji shiru alamar rai ya yi halinsa.

Da hanzari na tashi na ɗauki kaɗan daga kayana na ɗibi kuɗi na tsallake gawar ƴar'uwata kwance na bar gidan.

Ina kallon lokacin da Hakimi ya koma ɗakin ban san abin da ke hannunsa ba.

Gidan ƙaninsa na nufa wanda na fara sauka gidansa, ban ɓoye masa komai ba na gaya mai, ya jajanta shi ma ya ƙara min wasu kuɗin ya ce maza na bar garin kuma insha Allah zan ga iyayena da yardar Allah. Ya ƙara da cewa nasan waye Yayana zai iya maida kisan da ya yi kanki bayan ya wulaƙanta maki rayuwa don haka ki bar jahar nan baki ɗaya Alawiyya Allah Ya shige maki gaba kan dukkan lamurranki."

Haka na bi dare na tafi na kwana tasha motar asuba na bar Sokoto na shiga motar Katsina ina jin tashin hankali sosai a raina.
Bayan na isa Katsina ne na sauka a hanyar shiga wani ƙauye gab da Katsina, ban san kowa ba ƙauyen kuma naji a raina nafi son zama ƙauye fiye da cikin gari, domin na lura zama cikin garin yafi ko'ina tashin hankali, na karanci mutanen gari ba su da amana basu da taimako basu iya tausaya ma mutum haka ba su yin abu don Allah.

Na jima zaune a wani ƙaramin waje dana lura kamar kasuwar su gun. Na ji yunwa na je na siyi abinci na ci na koma inda nake zaune na sake zama, har dare ya yi ban gusa daga gun ba idan ba sallah da cin abinci na tashi yi ba.

Wani matashin saurayi dake kula da Ni tunda na sauka mota ya iso inda nake zaune ya yi min sallama na amsa ya tambaye ni gidan wa nake nema ne. Na ce mai ba gidan kowa, ban san kowa ba na zo neman iyayena ne kawai ko zan dace cikinsu wani na garin.

Ya dubeni sosai ya ce, "Kina nufin b tare suke da juna ba iyayen naki ba? To taya suka rabu da juna idan haka ne?"

Haka kawai naji na yarda da shi don haka na ba shi labarina kaf tun daga farko har ƙarshe.

Jinjina kai ya yi, ya ce min, "Ki zo mu je na kai ki gidanmu wajen Mamana, ita kaɗai ce sai Ni a gidan mahaifina ya rasu shekara biyu kenan da rasuwarsa."

Na bi shi har gidansu ya yi ma Mamarsa bayani kamar yadda nayi mai, ta amince za ta zauna da Ni gidanta amma ta gayamin tana zuwa cikin garin Katsina gun aikatau a wani gida idan ba damuwa na dinga bin ta muna zuwa tare muna dawowa tare. Ban ja ba nace ma amince.

Sunanta Zainab sunan yaronta Awwal sosai naji daɗin zama da su saboda ba tsangwama sun gaya ma jama'ar ƙauyen daga garin ƴan'uwanta na zo zan kwana biyu nan.

Ranar da muka fara zuwa aikatau gidan sai da na razana ganin gidan mai kyan gaske ga shi babban gida, amma kuma Baba Zainab ta gayamin maigidan bai da iyali shi kaɗai ne gidan, kuma abincin da ake a gidan sadaka yake ba da shi.
Wata na guda ina zuwa aiki gidan rannan dai Baba Zainab ta kwanta bata lafiya sosai, muka kaita asibiti Ni da Nura aka ce mana musayar ƙoda za ai mata, ga shi ba mu da kuɗin da aka nema na aikin.

Hakan yasa na nufi gidan aikinmu da takardar asibitin aikin da za ai ma Baba Zainab da nufin neman taimako gun maigidan tunda halinsa ne bada taimakon.

Ina zuwa cikin sa'ar gaske na iske motar gidan ban sha wahalar samun iso gunsa ba, da yake mun saba da sauran ma'aikatan gidan.

Ina shiga da sallamata falon maigidan inda ban taɓa shiga ba tunda nake zuwa gidan aiki sai Yau, yana zaune ya sadda kansa ƙasa tamkar mai tunani na sake yin sallama a karo na biyu.

Ya ɗago kanshi ya kalle Ni da nufin amsa sallamar sai kuma ya tashi zumbur ya nufoni ya kama Ni ya dinga girgiza Ni yana cewa, "Da gaske ke ce a gabana Alawiyya! Alawiyya dama kina raye? Alawiyya ke ce gabana! Ya fashe da kuka ya rungume Ni sosai a jikinsa, maganarsa ta ƙarshe tasa na gane mahaifina ne shi da naji ya ce, "Ina Fatima ina tsohuwa Alawiyya?"

Kuka mai ƙarfi ya ƙwace min nima na rungume mahaifina sosai ina kukan farin cikin ganin mahaifina.

Sai da mutane suka shigo jin kukana ya yi yawa duk suka ja birki ganina rungume jikin Alhaji muna kuka sosai.

Da ƙyar ya sake Ni ya zaunar da Ni ya dube su yana matuƙar murna ya ce masu, "Yau Allah Ya amsa addu'a ta Ya bayyana min jinina ɗiyata wadda na fito nema shekaru masu dama da suka wuce. Wannan ita ce Alawiyya ɗiyar Fatima da nake baku labarin ta ɓace a garin Lagos."

Nan da nan wajen aka ɗauki murna ana hamdala ga Allah.

Sai daga baya na dawo hayyacina na tuna da marar lafiya ta dake kwance asibiti, na ba Daddy takardar na ƙara da yi mai bayanin halin da take ciki. Ina zaune nayi ya yi waya nan take aka tura komai na aikin. Ni kuma na ba shi labarin abin da ya faru dani bayan rabuwarmu da tsohuwa.

Tun daga nan ne ya saka Ni makaranta na cigaba da karatuna cikin kwanciyar hankali sai da na gama karatuna kaf sannan ya ce na shirya mu je garinsu wajen danginsa dama alƙawari ya yi ba zai koma ba sai ya gano ɗiyarsa.

Haka kuwa akai ya basu Awwal gida mai kyau ya ba shi jari mai kyau muka nufi garinsu Daddy na yi matuƙar mamaki dana ga Kano muka nufa ban sake tsinkewa da lamarin ba sai da naga mun shiga cikin gidansu Inna Saude na kalli Daddy na zaro ido waje nace "Me za mu yi nan kuma Daddy? Nan ne gidan dana baka labarin an riƙe Ni an azabtar dani sosai fa."

Baice komai ba muka shiga cikin gidan duk ya sake lalacewa gidan ya koma kamar kango. Jikina a sanyaye muka shiga gidan kamar yadda na lura da jikin Babana ma a sanyaye yake.

Tana zaune tsakar gida ƙafarta tayi wani uban kumburi ba kyan gani duk ta rame ta fice hayyacinta kamar ba Inna Saude ba, Daddy ya yi sallama nikam biye nake da shi kawai na kasa ko buɗe bakina.
Ta zabura tai kamar ta miƙe tsaye amma ba dama, saboda ƙafarta da ba lafiya.

Kuka ta saki da ƙarfin gaske tana ambatar "Bello kai ne a gabana ashe kana raye dama?"

Nan da nan sai ga jama'ar gidan sun cika gidan, kowa na ambatar Auta ya dawo ga Autan Inna Saude!

Mamar Faisal kawai ta kula da Ni ta kuwa jawo ni tana cewa, "Kar dai ince Alawiyya ce ta dawo? Allah na gode maka da ka dawo wa yaron can da farin  cikinsa." 

Sannan kallo ya dawo waje na kuma, Inna Saude ta dube ni tana kuka tace, "Da gaske Alawiyya ce ko wasa? Idan ita ce ina ta gano Auta na? Kai wannan yarinya ba dai zata rabu da jinina ba ashe? Na tsaneki na tsane ki amma kin liƙe min, kamar kaska.

Sai a lokacin Daddy ya kama hannuna ya riƙe ya dube su duka ya ce, "Ina Baba yake?"

Aka ɗauki kuka ana cewa Allah Ya yi mai rasuwa ai.

Ya girgiza kan shi yana jin ciwon rashin mahaifinsa sosai har sai da ya kai da goge hawaye.

Da ƙyar ya ce, "Wannan ita ce ɗiyata da na fita nema ta wajen Fatima dana haifa a Lagos."

Sai kallo ya koma sama, nan da nan fuskar Maman Faisal ta sake washe wa ta ce, "Allah abin godiya, tabbas Alawiyya tai kama da kai amma ba damar faɗa saboda Inna bata son ta."

Na dube ta nace, "Mama ina Yaya Faisal ?" Tai murmushi tace, "Yana asibitin da yake aiki, kullum sai ya yi maganarki ko da yaushe bakinsa na kanki ba don na ƙi amince mai ba da tuni ya bi duniya nemanki .

Naji sanyi a raina domin duk tsawon rayuwar da nake da gabaɓiɓin da nake ina maƙale da son Faisal a raina , kawai na ɓoye abin ne saboda ban da ƴancin hakan, ban da gata da galihun da zan ce ina son shi balle har na saka a raina zan aure shi. Ko ba komai nasan cewa Kakarsa ta tsane Ni fiye da yadda ta tsani kowa a rayuwarta.

Muna a haka ne ya dawo da gudu ya shigo yana ambatar sunana, cikin farin ciki muka dubi juna murna fal a zukatan mu.

Da dare sai ga Yaya Mansur ya zo, ya yi murna sosai daya ganni, lokacin da ya ji labarin nice ɗiyar Oga Bello ba ƙaramin farin ciki ya sake shiga ba.

Nan ne yake ban haƙuri kan abin da ya dinga min, ya ce, ashe Inna Saude ce ta zuga matarsa har ta kai ta gun Malami akai min asiri aka saka min tsanarki a raina don haka ne duk sanda na ganki nake jin kamar na kashe kaina ko na kashe ki."
Matar ma ta zo cike da kunya tai ta ban haƙuri nace ba komai ya wuce ai.

A lokacin ne Yaya Mansur ya dubi Daddy na ya ce, "Oga kaga kuɗaɗen da nake turo ma kuwa na gareji ko? Ai Masha Allah ana samun alheri sosai bayan tafiyarka."

Sai a lokacin ne ma Daddy ya tuna da wani account na shi na da ya manta da shi ma shi sam. Ya ce "Ai kuwa ban san kana turawa ba, domin hatta layina karya shi nayi ban sake bi takan wani account ɗin banki ba balle na cire kuɗi kona saka wasu ba."

Washegari kuwa aka sake bincikar account ɗin sai ga maƙudan kuɗaɗe a ciki masu yawan gaske. 

Daddy ya fitar da su kaf ya ban ya ce, na nemi sana'a mai kyau, don haka na yanke shawarar zan gina asibiti mai kyau inda za a dinga taimakon marassa ƙarfi tunda Yaya Faisal likita ne.
Kwana biyu da zuwanmu Daddy ya zuba kuɗi ta hanyar abokin aikinsa aka fitar da Inna Saude ƙasar waje akai mata aikin ƙafarta sai dai dole sai da kujera take amfani bata iya tashi tsaye ta taka ƙafarta kamar kowa.

Bayan mun dawo ne daga yi mata aikin akai aurena da Faisal lokacin na kama aikina na lauya sosai babu garin da ban zuwa kan aikina, a haka Allah Ya azurta Ni da yara uku maza biyu mace guda ƴan biyu duk maza na fara haifa aka saka masu sunan Daddy da Kakana amma ana kiransu da Affan da Aiman sai macen da na saka wa sunanki Hawwa'u nake kiranta da Jiddah.

Wannan shi ne labarina bayan rabuwarmu dake Jiddah."

Cewar Alawiyya tana kallon Jiddah dake ta kuka.

Wayar Alawiyya ce tai ƙara tana ɗagawa aka gaya mata cewa tai baƙuwa daga nesa tana son ganinta.

Bata ji komai ba ta bada umarnin a kawo ta gidan da take yanzu tana jiranta.

Ba da jimawa ba sai ga tsohuwa an kawo ta kamar ba ita ba,madadin tai rame ko ta yamutse sai ma kyau da tayi.
Su duka suka fasa ihu suka rungume ta suna ihun tsohuwa ta dawo ga tsohuwa.

Kasancewar mutanen gun kowa yasan labarin tsohuwa shi Daddy shi ne ma yafi kowa sanin ta domin ita ce ya auri Fatima gunta kamar ya fi su murna ma.

Bayan an gama murna ne tsohuwa ta fashe da kuka tace, "Na samu labarin abin da ya faru ne ta hanyar sauraren rediyo da jikana ya zo kuma ya sake bayyana min abin da ya gani a jarida, tabbas a nan na amince da cewar Alawiyya ce da Fatima, hakan yasa na matsa ma jikana sai ya kawo Ni Kaduna domin Ni ina zaune ne a ƙauyen Sokoto wani ƙauye da ake kira FANGWA to da can muke zaune sai kuma jikan nawa ya samu ɗaukaka ta hanyar samun aiki mai kyau a cikin garin Abuja a wata ma'aikata har suka ba shi gida da mota, hakan yasa ya ɗauke Ni kuma koma can da zama cikin kwanciyar hankali."

Jiddah ta dubi tsohuwa tace, "Amma me ya hanaki komawa Lagos bayan kin bar Alawiyya gidanmu tsohuwa?"

Hawaye suka zubo ma tsohuwa tace, "Bayan na koma garinmu ne da nufin nayi wata guda na dawo sai hakan bai samu ba, domin daren ranar da zan dawo ne aka fara faɗan siyasa, wanda aka kashe mutane da dama na garinmu wasu aka raunata su sosai. Ni da Yarona muna zaune yana fama da Ni kan na haƙura na zauna nan yanzu yana samu ba kamar da ba tunda har ya yi aure matarsa ta haihu ma yaron ya girma sosai, ya ce zai iya riƙe Ni nace mai sai idan ya amince zan je na dawo da Alawiyya nan wajena na ba shi labarin kaf rayuwata da Fatima har zuwa kan Alawiyya, ya yi jim sai kuma ya ce, amma Inna ai da kin sani da ita kika dawo, da baki baro ta gun arniya ba, tunda ke iyayenta suka ba amanarta don haka ki bari a gama wannan guguwar siyasar sai na raka ki mu je tare ki amso ta, idan ya so sai mu bar saƙon idan iyayenta sun zo neman ta su zo nan su amshe ta."

Har dare ya yi muna ta fira da shi ya tafi, washegari sai dai na ji kururuwa daga cikin gidansa wai wasu sun shigo sun kashe shi har da matarsa ɗan sa kuwa sun ji mai rauni sosai.
Wannan tashin hankalin yasa na manta labarin komawa Lagos har sai da jikana ya samu lafiya lokacin komai namu ya ƙare ban da komai hatta gidanshi na saida sai gidana kawai inda muke rayuwa nida jikana.

A haka mu kaita rayuwa cikin baƙin talauci na tsawon lokaci har Allah ya kawo wani bawan Allah ya taimaka ya ɗauki jikana yana mai aikin lissafin kuɗaɗe daga nan ne ya zama silar samar mai aiki a wani banki dake Abuja muka koma can rayuwa tai mana daɗi, bayan mun koma ne na matsa mai muka shirya muka je Lagos nemanki amma aka ce mai ai ba a san inda kuke ba ke da Jiddah an neme ku an rasa haka ma an nemi Iyami an sara kuma Babanki ya je nemanki bayan guduwar Iyami. 
Tun daga lokacin nake neman ki ta hanyar addu'ar Allah Ya bayyana min inda kuke shiru.

Sai jiya ne naji a labarai an kira sunanki dana Jiddah sai na amince da cewa ke ce, da jikana ya dawo nai mai magana sai ya ce ai kowa yasan ki yana ma da hotonku shi ne ya nuna min nace tabbas kuwa ke ce, hakan yasa na shirya nace Yau ban kwana sai na zo Kaduna tun da akwai kotun da kuke shari'ar nasan zan ganku."

Su duka sukai mata jajen ɗanta da ta'aziyya,sannan ta dubi Baban Alawiyya tace, "Bello me ya faru bayan danginka sun tafi da kai baka dawo ba, bayan kai min alƙawari zaka dawo?",

Daddy ya nisa ya ce.


Mu haɗu a page na gaba don jin labarin Daddy bayan ya shiga duniya naman ɗiyarsa Alawiyya.

Taku a kullum Haupha ✍️