‘Yan Bindiga Sun Halaka Tsohuwa Mai Shekaru 120 A Sakkwato

‘Yan Bindiga Sun Halaka Tsohuwa Mai Shekaru 120 A Sakkwato

 

A ranar Talata 'yan bindiga sun halaka wata tsohuwa mai shekaru 120 da wasu biyar tare da kone gidajensu tare da sace musu dabbobi a Sokoto, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto. 

Majiyoyi sun labartawa manema labarai yadda 'yan bindiga suka yi dirar mikiya anguwar Raka cikin karamar hukumar Tangaza, in suka jefa firgici da rudani a zukatan mutane bayan sun tafi. 
"Duk da babu wanda aka yi garkuwa da shi, 'yan bindiga sun halaka mutane shida  da wata tsohuwa, sannan suka kone kashi biyu cikin kashi uku na gidajen anguwar, yayin da suka sace kayayyakin abinci da shanun jama’a.” 
Hakimin Raka Sa'idu Wakili ya bukaci mazauna yankin da su roki Allah ya kawo musu daukin gaggawa don zaman lafiya ya tabbata, sannan yayi kira ga jihar da gwamnatin tarayya da su yi kokari wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin. 
Shugaban karamar hukumar Tangaza na rikon kwarya, Ibrahim Lawal Junju, tare da mai ba gwamna  sharawa ta musamman a bangaren kula da tituna, Injiniya Mai Damma Tangaza, ya jajantawa  mutanen anguwar Allah ya tsare gaba. Sun siffanta harin a matsayin ba-zata tare da alkawarin sanar da  ga gwamnati don ba da taimakon da ya dace ga wadanda lamarin ya shafa.