WATA UNGUWA, Fita Ta Biyar

WATA UNGUWA, Fita Ta Biyar

 

BABI NA BIYAR

 

wata makekiyar tabarma ce Shimfiɗe a tsakiyar mayalwacin gidan, inda wata rusheshiyar mata mai ƙiba sosai take zaune akai ta yi tamatela, wasu matan guda uku ne zaune a gefenta, da alama dai hira suke yi. Domin kuwa hankalinsu ya raja'a sosai gurin saurarenta.

 

Matar da za ta kai kimanin shekaru sittin zuwa da biyar a duniya ta ce "Kai jama'a lallai unguwar nan tamu ta Garwa kowa na abunda ya ga dama."

 

"Me ya faru kuma Iya?" Ɗaya daga cikin matan da ke zaune kan tabarma ta tambaya.

 

Iya ta kaɗa kai kamar kirki ta ce "Uhm! Uhmm!! Bari kawai Halima ashe ƴaƴan nan na Baba Mudi lalacinsu da fanɗarewar su har ta kai sun fara neman rayukan junansu?"

 

"Waɗanne yaran kenan ba dai Sofi da Maryam ba?" Matar da bata yi magana ɗazu ba ta jefo tambayar cikin mamaki.

 

Iya ta gutsiri goronta ta tauna sannan ta ce "Allah ya sa ga ki Mariya, ita Maryam ɗin yaushe ta taso ma da har zata riƙa haka? Waɗannan riƙaƙƙun 'yanmatan dai Hanifa da Safiya, baki san shekaranjiyan nan suka yi faɗa kan ruwa ba har suna neman kashe junansu?"

 

"Ki bari don Allah iya! Ai bamu sani ba." Suka faɗa gaba ɗaya.

 

Da kyar Iya ta miƙe tana faɗar "Wash! wash!! Jikin tsufa kenan dubi yanda na kasa tashi.

 

Can ta wuce taɓur, taɓur cikin tafiyarta mai kama data agwagwa, bata ma iya miƙewa duka a dudduƙe take tafiya tsabar ƙiba da kuma ciwon ƙafa dake damunta.

 

Gun murhunta ta je tana iya wuta daga can ta juyo ta kalli su Mariya dake cikin jimami ta ce "Ai baku sani ba, Biba tana dab da suƙa Habibu ya tsinke sauran igiyoyi biyun da suka rage tsakaninsu, don ma yana ta haƙuri da ita."

 

"To ita kuma Bibar me ta yi Iya?" Suka haɗa baki gun tambaya.

 

"Ai ya fara gajiya da halinta ne na tara masa 'yanmata da samari da take, suna cika masa gida kamar ƴaƴan ɓeraye, kuma suna cinye masa abinci. Ita kuma ga baƙar ƙazanta ɗakinta kamar na jaka."

 

kwashewa suka yi da dariya duka, Mariya ta ce "Ai gwanda ya taka masu birki kafin ta ja masa salalan tsiya, kin ga wannan yarinyar Sagira dake zama a gidan? Al'amarinta sai dai ayi kurum."

 

"Allah ko Mariya?  ina ganinta kamar Saliha ashe tana ƙasa tana dabo, to ba mu mu sha." Iya ta faɗa yayin da take juyowa zuwa gunsu.

 

Mariya ta miƙe tsaye "ke dai a yi ta sha'ani kawai amma yaran zamani da kike ganinsu idonsu tsakar ka yake. Sagira 'yar bariki ce ta ƙarshe da kike ganinta nan simi-simi macijiyar sari ka noƙe ce."

 

Nan suka riƙe haɓa suna ta mamaki da zaginta.

Mariya ta ce "Ni dai zan wuce gida kafin waccan munafukar ta dawo kunsan halinta dai."

 

Daga haka ta fice gidan cikin hanzari,ta bar su nan suna ci gaba da gulma da cin naman mutane unguwa har ma da na ƙetare.

 

Abba ne tafe a hanya ya haɗu da Sagira tana tafe a hankali yanda kasan wata Saliha, in ka ganta sai ka rantse da Allah idan ka saka mata yatsa ba zata ciza ba.

 

Abba ne ya ce "Hajiya Sagira ina za'a haka?"

 

"Uhmm! Ya Abba ina wuni, wallahi gidan Iya mai bakin Aku za ni, Inno ce ta aike ni gurinta."

 

Ɗan murmushi ya yi tare da yamutsa hargitsattsiyar sumarsa irin ta kangararrun yara, ya ce "Ok  gidan wannan munafukar tsohuwar za ki kenan, To a dawo lafiya Allah ya sa kada ki tarar Ana gulmarki."

 

Yana gama faɗa ya wuce abinsa, girgiza kai Sagira ta yi tare da wucewa a ranta tana cewa in dai Iya mai bakin Aku ce zata aikata, domin kaf Unguwar nan ba wanda ya ƙware a gulma kaman ita, ko Mamuda s/m Sarkin munafukan Afrika ya shafa mata lafiya a fagen gulma."

 

Haka ta wuce zuwa gidan. Tun daga soron gidan ta ja ta yi turus, domin abinda kunnenta ya jiyo mata, "Sagira kuwa ta lalata rayuwarta, ko da yake bata yas ba kan gado ta ɗauko, lokacin ƙuruciyar mahaifiyarta ba abinda bata yi ba daga baya ne....."

 

Kafin Iya ta gama rufe baki Sagira ta faɗa gidan da gayya don ta ga ya za su yi idan suka fahimci ta ji.

 

"Assalamu alaikum." Ta faɗa.

 

Da sauri suka ɗago suna kallonta, ko waccen su ta yi wuri-wuri da ido tamkar wanda aka kama yana sata. Ko da yake meye marabar dambe da faɗa?

 

Iya ce ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Wa'alaikumus salam, A'ah! Sagira ke ce? Ya gida ya Maman taku da Kakarku?"

 

"Suna nan ƙalau." Ta bada amsa a takaice domin mamaki da takaicin halin dattijuwar ya mamaye ta.

 

"Madallah! Ya aka yi ne?" Iya ta tambaya.

 

"Inno ce ta aiko ni gunki, wai ki Sammata goro da 'yar taba, ta aika siye ba ta samo ba, shi ne tace tasan ba'a rasa nono ruga don haka za'a samu wurinki." Sagira ta faɗa fuskarta ba yabo ba fallasa.

 

"Inno tamu, to bari na ɗauko mata." Tashi ta yi ta nufi ɗaki, dai dai lokacin wani yaro ya shigo gidan a guje sai shessheƙa ya ke. "Mama Halima wai... Ki.. zo ga shi can Anas ya jefa Sabi'u cikin rijiya." Ya faɗa muryarsa na sarƙewa tsananin tashin hankali.

 Dafe ƙirji ta yi tana faɗar "Innalillahi wa innailaihir raji'un! Na shiga tara ni Halimatu, mai wannan yaron yake so ya mayar mun da kansa tun yana ƙanƙani? Yaro baƙar zuciya sai kace kumurci?" Tana gama faɗa ta fice daga dandalin gulmar ta su cikin hanzari ta nufi gida don ganewa idonta abunda ke faruwa.

 

Tafiya take cike da tashin hankali, tun kafin ta isa kusa da ƙofar gidanta ta hango cincirindon mutane gurin sai hatsaniya ake. Isowarta gurin ya yi dai-dai da lokacin da Shu'aibu yayan Sabi'u ke faɗar "Tab! yau akwai ƙaramin yaƙi a unguwar nan kenan, bari a fiddo shi in har ƙanina bai rayu ba yasin kai ma sai na jefa ka rijiyar nan in ya so in kun haɗu can lahirar ku ƙarasa rigimarku."ya faɗa ya na kallon Anas ɗan shekaru goma.

 

Dai-dai lokacin aka janyo wanda ya shiga rijiyar da igiya, yana goye da Sabi'u a bayansa. Jikinsa tsamo-tsamo da ruwa. A nan ya sauke shi bakin rijiyar dattijan gurin suka shiga duba ko yana raye. Bayan an matse ruwan cikinsa an ji shiru ba alamar ya na ko motsi, wani daga cikin mutanen ya ɗago yana faɗar "Ina jin kamar wannan ruhin ta jima da barin gangar jikin da take maƙale a ciki."

 

Rufe bakinsa ke da wuya Shu'aibu ya yi ihu irin na 'yan daba ya rarumo Anas ba ɓata lokaci ya ɗaga shi ya saita bakin rijiyar yana shirin wulla shi....

 

Ganin haka ya tsinkewa Halima duk wani jini dake gudana a jikinta, ta razana matuƙa, tsaye take guri ɗaya ta zama tamkar mutum-mutumi?