MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 51--55

MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 51--55

Page 51----55

 

 

 

Zayyanul murrash ya dubeta fuska ba alamar wasa yace, "Idan kin aminta za ki ƙwato min yarinya ta sarauniya Raƙiyyatul Zayyanul murrash, sannan sharaɗi na biyu za ki kashe masoyiyar Abduljalal bin Uwais , to haƙiƙa ni nan zan taimaka maki da yadda za ki kashe yarinyar cikin ruwan sanyi."

 

Dariya ta bushe da ita, kamar an tarwatsa dutse, kana ta murtuke fuska ta dubesa ta ce, "Na sanka baka da amana baka san darajar alƙawari ba Sarki Zayyanul murrash, domin kuwa ku cin amana a cikin ibadarku take, ha'inci a cikin jininku yake, yaudara ita ce takenku.

 

Amma duk da haka bari ka ji wata magana, zan amince da wannan sharaɗi naka idan kaima ka amince da nawa sharaɗin.

 

Ka sani idan na kashe Bilkisu na kawo maka Raƙiyyatul Zayyanul murrash ka ce zaka ci amanata ta hanyar cutar da Jalal ɗina na rantse da Sarkin da ke busa ma matacce numfashi da kai da ita tare da duk magoya bayanka sai na halaka ku na ɓatar da ku daga doron duniyar baki ɗaya.

 

Kasan cewar nafi kowa baƙin hali, baƙar zuciya da taurin kai harma dana rai a cikin jinsinmu .

 

Dan haka ka tabbatar da cewa baka da burin ɗaukar fansa akan abin da Jalal yayi ma ƴarka Raƙiyyatul Zayyanul murrash .

 

Sannan ina son ka sani sai na shafe babin duk wasu masu bautar gunki da tsafi a wannan duniyar, kasan zai zan iya ko ?

 

Wata banzar dariya ya kwashe da ita mai ban takaici ga wanda akai mawa ya nuna wani madubin tsafi dake kafe a cikin ɗakin.

 

Sai ga hoton Bilkisu da Abduljalal bin Uwais, Bilkisu na kwance jikinsa yana shafa cikinta yana murmushi ya kai bakinsa ya sumbace ta a cikin yace, "Ya ke hasken idaniyata muradin zuciyata farin cikin raina, shin yaushe za ki sanyaya idaniyata da kyakkyawar ɗiya ko ɗa ne ?

 

Shafa fuskarsa tayi tana mai maida masa martanin sumbata a fuskarsa ta ce, "Ina roƙon Allah ya ban yaro kyakkyawan gaske kuma jarumi haziƙi kamarka masoyina."

 

Bakinta ya rufe yana murmushi yace, "A son raina na fi son ace kin haifi yarinya kamarki sak, da irin halayenki na tabbata da na fi kowane uba samun farin ciki a duniyar nan."

 

Wata uwar ƙara Suwaibatul Zabbar ta saka ta dinga marin fuskarta tana yakushin idanunta da suka gane mata wannan babban lamari .

 

Sarki Zayyanul murrash ya ɓarke da dariya yace, "Na rantse da abin bauta ta idan kika kashe yarinyar nan kin gama da duk wata damuwa taki, sannan idan kika maido min ɗiyata zan baki mamaki ta hanyar zama hadiminki .

Kin san dai na kasance ɗaya daga cikin masu cika alƙawari, sannan ban wasa da rayuwar ɗiyata ɗaya tal da na mallaka a rayuwata bayan shan gwagwarmayar rayuwa.

 

Saboda haka ki amince da buƙatata ni ma na amince da taki buƙatar."

 

Jin batunsa yasa Suwaibatul Zabbar ta amince da maganarsa amma sai ta dubeshi ta ce,  "Kasan dai babu wata yarda ko aminci a tsakaninmu wannan ma kawai haka Allah ya ƙaddara dan haka babu buƙatar ka zama hadimi a gareni, sai dai bayan cikar burin kowanne daga cikinmu kowa ya ɓace daga duniyar kowa."

 

"Ya ke Suwaibatul Zabbar ki yi sani cewa hakan ya fi komi sauƙi a gareni."

 

Ba tare da shakkar komi ba Suwaibatul Zabbar ta yadda da duk wani tsarin da Zayyanul murrash ya bata ta ɓace tana sheƙa dariyar samun nasara da mugunta.

 

 

 

 

 

Wasa-wasa Bilkisu ta zo tafi Abduljalal ɗin damuwa da rashin haihuwarsu, wanda har ta kai sai ta samu waje ta ɓoye kanta ta kama rusa kuka tana addu'ar Allah ya basu haihuwa da mijinta abin sonta Abduljalal bin Uwais. (Ta manta babu haihuwa a tsakanin mutum da aljani).

 

Shi kam Abduljalal bin Uwais tunda ya yi tambaya ga malamai da dama suka tabbatar masa da cewar babu haihuwa tsakanin jinsin aljanu da mutane ya shiga cikin tsananin damuwa domin kuwa yana matuƙar buƙatar haihuwa, ba da kowa ba sai da Bilkisu.

 

Amma ya zai yi dole ya danne abin a ransa ya ɗauki matakin daina yi mata maganar samun haihuwar ta su.

Aduk sanda ta keɓe kanta tana kuka yana ganinta sai dai bai san abin da zai mata ya sanyaya mata ranta ba, domin bai da abin da take buƙata a garesa haka bai san inda za shi ya samo mata shi ba.

 

Sai dai shima ya koma gefenta batare da ta ganshi ba yayita kuka yana ƙarawa yana kallonta cike da mugun tausayin kansu .

 

 

Kasancewar yanzu Suwaibatul Zabbar ta daina kawo ma Bilkisu hari yasa take samun damar zagaya ko ina a cikin ɗakin cikin natsuwa da kwanciyar hankali abin ta.

 

Sai baki ɗaya suka ɗauka ta haƙura ne da Abduljalal ɗin duk da shi yasan abu ne mai wuya ace Suwaibatul Zabbar ta fasa cikar burinta, ko ta fasa kashe Bilkisun, sai dai idan akwai abin da take shiryawa garesu.

 

Hakan yasa bai wani sakewa ya bar Bilkisun tai ta yawo ita kaɗai yana haɗata da manyan sadaukai jarumai suna take mata baya aduk sanda ta fita yawon rangaji ba tare da shi ba.

 

 

Kwata-kwata Bilkisu ta manta da wace ce ita, haka ta manta da iyaye ƴan'uwa ko ƙawayenta, abu guda kai take tunawa shi ne masoyinta Abduljalal bin Uwais.

 

Lokuta da dama ta sha tambayarsa me yasa ita bata kasance irin jinsin shi ba ta zo a wata halittar da ban ?

 

Sai dai yayi murmushi yace babu yadda Allah bai halittarsa bayan ke akwai wasu kalaluwan halittu ma da yawa a kewaye da duniyar nan." Da haka yake samu yana kashe mata baki daga yawan tambayoyinta a gare shi.

 

 

Suwaibatul Zabbar bata zame ko ina ba sai dajin da aka kafe Raƙiyyatul Zayyanul murrash, ta sha fama ta sha yaƙi da masu tsaron  dajin kafin ta samu damar shiga inda aka akulle Raƙiyyatul Zayyanul murrash ɗin.

 

Sai dai lokacin da ta yi arba da ita baki ɗaya sai komi ya kwance mata, domin ta ƙame ta koma tamkar gunki babu alamar motsi a tare ita balle a samu rai a jikinta .

 

Kamo wani aljani tayi ta ba shi umarnin maida Raƙiyyatul Zayyanul murrash yadda take amma sai ya sadda kanshi ƙasa yace, "Ki garceni yake wannan sarauniya, haƙiƙa babu wanda ya isa ya maidata a cikin suffar ta sai masoyinki ko abokiyar gabarki Bilkisu kaf faɗin duniyar nan sune kawai za su iya maidata yadda take."

 

Cike da fusata ta dube shi ta ce, "Akan me waccan jaririyar bil'adamar zata iya abin da ni ba zan iya ba?

 

Sake rusunar da kansa yayi yace, "Ki gafarceni saboda ita ce matar Sarki a halin yanzu ta jima da zama ɗaya daga cikin jinin sarautar nan domin ta samu damar kwanciya da Sarki a shimfiɗa guda."

 

Wani takaici ya taso ya duƙunƙune zuciyar Suwaibatul Zabbar baki ɗaya, wanda yasa ta kasa ko furta kalma guda.

 

Juyawa tayi da nufin barin wajen sai kuma ta tuna ba mamaki idan ta ɗauki gangar jikin Raƙiyyatul Zayyanul murrash ɗin mahaifinta tunda ƙwallo ne kuma shugaba a cikin matsafa ƙila ya maida ta yadda take, don haka ta sunkuya da nufin ɓambareta daga ƙasar ta tafi da ita.

 

Sai tayi-tayi amma ta kasa, daga ƙarshe sai wani baƙin jini mai muni daya dinga fitowa daga cikin ƙasar wajen.

 

Aljanin ya sake rusunawa yace, "Ya ke Gimbiya ki yi sani wannan jikinta ne kike yi ma lahani wanda hakan yasa take zubda jini."

 

 

"Lallai Jalal ya bani  mamaki, yaushe ya zama hakan ?

To da zan rasa duk abin da nake da shi ne sai na kashe Bilkisu na kuma fitar da Raƙiyyatul Zayyanul murrash daga wannan halin domin cika alƙawarin da nayi ma mahaifinta ."

 

 

Shi kuwa aljani Zayyanul murrash kai tsaye wasu baƙaƙen aljanu ya kira ya basu umarnin su je gidajen su Bilkisu da Nasir su tabbatar da sun yi bayanin yadda akai Abduljalal bin Uwais ya sace masu yara.

 

Haka kuwa akai nan take suka ɓace suna masu bin umarninsa.

 

Kasancewar yanzu iyayensu Bilkisu babu abin da suka saka gaba sai zuwa gun manyan malaman sunna don a taimaka a tayasu da addu'a yasa iyayen Nasir suka je inda aljanun Zayyanul murrash suka ƙafa dandali na manyan malaman sunna da shelar sun zo wa'azin ƙasa ne a garin wanda ake duk shekara.

 

Wannan yasa mutane suka dinga ba iyayen Nasir ɗin shawarar su je garesu ko sun dace .

 

Bayan sun je ne suka bayyana masu damuwarsu na ɓatan yaransu har biyu waɗanda masoya ne suna gab da aure, amma rana guda aka wayi gari babu su ba labarinsu.

 

Babban malamin yace su ba shi lokaci yayi istihara don ganin abin da ke faruwa.

 

Bayan wani lokaci ya fito cikin wani irin hali na alhini yace masu ba zai ce komi ba sai anzo da iyayen yarinyar musanman mahaifiyar yarinyar Huraira.

 

Haka kuwa aka yi su je suka gayama malam Ahmad yadda aka yi yace su je, Allah dai ya bayyana gaskiyar lamarin.

 

 

Bayan sun je ne malamin ya dubi Huraira yace, "Ba mu labarin abubuwan da suke faruwa dake na al'ajabi ban tsoro da mamaki a kwanakin baya Huraira."

 

 

Nan da nan Huraira ta fashe da kuka ta sadda kanta ƙasa tana addu'ar yau Allah ya bata damar bayyana abin da tayi shekara da shekaru tana son bayyanawa tana kasawa.

 

Malamin ya dubeta fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "Ke na ke saurare Huraira."

 

 

Cikin mamaki Huraira taji bakinta ya buɗe ta fara zayyano duk wani al'amari daya faru da ita a cikin gidan.

 

Mamaki da tausayi suka baibaye mutanen dake gun baki ɗaya. Kowa sai kallon Huraira yake yana goge hawayen tausayinta dake zubowa daga idanunsa.

 

Sauƙin guda ne, sanda suka ɗauke ta sun daina cutar da ita kawai wata makaranta ta ganta ciki wadda duk matane irinta a cikinsu ta dinga koyon karatu da sauran littattafan ilimi har zuwa lokacin data buɗe ido ta ganta cikin ɗakinta, amma kuma a ranar Bilkisu ta ɓace tare da Nasir saurayinta."

 

Malamin ya dubesu yace, "To abin da baku sani ba shi ne, yarinyarku Bilkisu ita ce ta jawo kowace matsala, ta hanyar jifar Sarkin fararen Aljanu da tayi wata rana da yaje makarantarsu domin yaƙi da mugayen baƙaƙen aljanu dake shiga jikin yaran makarantar suna zalunci.

 

Ita kuma ganin shi a suffar baƙin kare yasa ta jefe shi, wanda sai da ta fidda masa jini a jikinsa, wannan jifar yasa shi fusata yace sai ya ɗauki fansa a kanta ta hanyar yi mata mummunan kisa, sai hakan ya kasa samuwa kasancewar yarinyarku Bilkisu tana da riƙo da addini yadda ya kamata, sannan ita ɗin ma'abociyar karatun Alkur'ani ce .

 

Tun ranar da ya fara bayyana a gareta yake son kasheta amma ya kasa saboda tana da ilimin addini sannan kuma tana aiki da shi.

Ya nuna Huraira da yatsa yace, "ke kuma fadawansa ne ke wasa da ke kasancewarki jahila wadda babu abin da kika sani sai jahilci da bin ƴan bori da malaman tsubbu, sannan duk sanda suka bayyana gareki babu abin da bakinki ya iya daga ihu sai zagi sai kin bani kin lalace.

 

Kinyi matuƙar digiri agun masifa da rashin ragowa, amma a ɓangaren addininki babu abin da kika iya sai tarin jahilci.

 

Kinci sa'ar lokacin da suka ɗauke ki wani gagarumin al'amari ya faru da Sarkin nasu, wato kamuwa da soyayyar ɗiyarki Bilkisu, don haka ya kaiki makarantar aljanu ta mata ya ajeki yayi umarnin da a koya maki karatu da addini yadda ya kamata.

 

Daga ƙarshe idan baku manta ba akwai ranar da layinku ya ruɗe da ihu da koke-koke wanda aka rasa wane iri ne ko ?

Iyayen Nasir suka jinjina kai, tare da wasu mutane dake layin suna gun kuma ƴan jin ƙwab irinsu Huraira.

 

Yace, "To aranar ne ya turo aljanunsa suka ɗauke maku yara, koke-koken da kuka dinga ji kuwa Bilkisu ce take addu'a don haka suke azabtuwa suke wannan koke-koken, amma daga ƙarshe sai da suka yi nasarar ɗauke ta, suka je su ka ɗauke Nasir.

 

Sai yanzu haka ita Bilkisu ta jima da mance wace ce ita saboda wani mantau da shi aljanin yasa mata, yanzu haka ya jima da aurenta suna can cikin farin ciki.

 

Shi kuwa Nasir ya kaisa wani daji inda wata makaranta take ta matasan Aljanu mai suna Darul Islam wanda duk wanda ya shiga cikinta sai yayi shekaru sittin da biyar kafin ya fice daga cikinta.

Wannan shi ne gaskiyar abin da na gani game da yaranku."

 

 

Tashin hankali ya bayyana sosai a fuskar mutanen wajen.

 

Yanzu kenan ya za su yi ?

 

Haka suka ɗunguma suka koma gidajensu kowa yana cikin tashin hankali da neman mafitar lamarin.

 

Sai kuma labari ya sauya a gari, Bilkisu ce ta jawo yaƙi da Sarkin Aljanu yanzu haka tana gunsa har saurayin nata, ƙilama ya kashe saurayin ita kuma ya aureta.

 

Malam Aminu ba'a barshi a baya ba, gun jinjina lamarin da neman mafita lokacin da labarin ya sameshi kasa haƙura yayi sai da yaje gidansu Shema'u Yahaiya ta rakashi gidansu Bilkisun ya ji maganar daga bakin Huraira sannan ya yarda.

 

Ya amsa cewar idan har za a amince to a koma gun malaman suyi masa kwatancen dajin da aka kai Bilkisun yaje ya ƙwato ta hakama yaje ya ƙwato Nasir ɗin .

 

Sai iyayensa sun shafama idanunsu toka sunce idan ya sake maganar wata Bilkisu sai sun tsine masa, ya manta yadda akanta aka azabtar da shi ne ? Ko ya manta yadda aljanun suka so halaka shi akanta ne ? To kada ya sake wannan maganar.

 

 

Bawan Allah Malam Ahmad sai ya kame kansa ya kama azumi yana sallar dare yana karatun Alƙur'ani akan buƙatar Allah ya fito da yaran lafiya .

 

Itama Huraira sai ta buɗe makarantar dare a cikin gidan tana koyama matan aure karatu wanda duk sanda za a fara karatu da sanda aka gama addu'ar kuɓutar yaran ita ce abu na farko da ake yi a makarantar.

 

Wasa-wasa Malam Ahmad ya sauke Alƙur'ani ya sake saukewa ko da yaushe yana sadaka yana ƙara kaskantar da kansa ga Ubangiji akan lamarin.

 

Yau yana cikin barci yayi mafarkin Bilkisun tana kallonsa tana murmushi, tana tafiya cikin wani kyakkyawan gida mai kayan alatu kamar wata masarauta yana ta kallonta yana son yi mata magana amma ga alama ita bata son yayi mata magana don sai sauri take ta ɓace masa.

 

Bayan ta ɓace masa ne ya ga wani ɗaki ya shiga, yana shiga wasu kyawawan samari zaune sunata karatun Alƙur'ani cikin murya mai daɗin saurare, kamar an ce ya dubi na kusa da shi sai ya ga Nasir yayi kyau ya ƙara haske fuskarsa tayi wasai sai karatu yake .

 

Kiran sallar asuba ya tada shi daga mafarkin da yake yi .

 

Godiya yayi ma Allah domin ya fahimci yaran na cikin natsuwa, basu tare da damuwa ko kaɗan.

 

Bayan ya dawo masallaci yayi sadaka yake ba Huraira labarin mafarkinsa.

 

 

    Darul Islam

 

Nasir ya saje da su ya sauya yayi fari yayi ƙiba kamar ba shi ba, halshensa ya karye kamar balaraben asali, yana rayuwa irinta Aljanu sai dai duk sanda ya tuna da Ibnah tare da iyayensu sai yayi kuka ya godema Allah.

 

Yuzarsef  ne abokinsa dan haka shi ne mai ba shi haƙuri a duk lokacin da ya shiga halin kewar gida da masoyiyarsa.

 

 

Baki ɗaya Bilkisu ta ɗauki muguwar damuwa ta ɗora ma kanta akan rashin haihuwa abin da ke matuƙar damun Abduljalal ɗin kenan.

 

Ya sashi cikin damuwa fiye da tata damuwar domin yayi ma kansa alƙawarin duk abin da take so sai ya samar mata shi indai akwai shi a duniyar nan.

 

To yanzu ya zai yi da wannan lamarin ?

 

Malaminsa ya shaida masa indai yana son farin cikin ta to ya maidata cikin jinsinta ta auri irin jinsinta shi ne kawai zata samu haihuwar da take nema.

 

Shi kam ya zai yi da tarin soyayar da yake mata ?

 

Yaushe zai iya haƙura da ƙaunarta ya maida ta duniyarsu ta auri wani ba shi ba ?

 

Lallai akwai babban ƙalubalen rayuwa tafe a garesa daga shi har itan?

Yasan yadda yake sonta haka take sonshi dan haka ba ƙaramin lamari bane rabuwarsu .

 

To wai shin yaya zai yi ne da wannan matsalar ?

 

Zai sadaukar da farin cikinsa ne domin samuwar buƙatar masoyiyarsa ko me ?

 

 

 *Ku cigaba da bibiyar alƙalamin Haupha