INA HUJJAR TAKE: Labarin Mai Sosa Zuciya Fita Ta Farko

SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)

INA HUJJAR TAKE: Labarin Mai Sosa Zuciya Fita Ta Farko

SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)* 

 

 

           Na

 

 

Hauwa'u Salisu (Haupha)

 

  

 

 

 ~Da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai.

~

 ~Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad sallahu alaihi Wasallam.

~

 

 *Wannan littafin ƙirƙirarren labari ne idan wani ko wata yaga abin da ya zo daidai da shi to akasi ne.*

 

 *SADAUKARWA*

 _Na sadaukar da wannan littafin ga dukkan masoyan Hauwa'u Salisu (Haupha) a duk inda suke a faɗin duniyar nan._

 

Page 1

 

"Lantai don mai garinku ki maza ki fito daga cikin ɗakin nan ki wuce makaranta, kafin masifaffen Yayanki Hafizu ya zo ya kama min mitar na hanaki zuwa makaranta."

 

Wata dattijuwa ce ke maganar tana kallon ɗakin dake kallonta.

Sai da ga alama wadda ake kiran ko a jikinta, domin ko alamar fitowa bata yi ba daga ɗakin duk da cewar dattijuwar ta jima tana mata magana.

 

Sai da dattijuwar ta ce, "Yawwa Hafizu gara daka shigo ai yanzu ta fito ta wuce tunda ni ta rainani ai."

 

Kamar an jehota wata yarinya da bazata wuce shekaru takwas ba tai fitar burgu daga ɗakin tana cewa, "Inna Kande sai na dawo, kuma na iske ana zane ƴan makara na rantse dawowa zan ba malamin da zai dakeni."

 

Kallonta tayi dattijuwar tana cewa, "Ho ja'ira da ban ce haka ba, baki  fitowa daga ɗakin nan daman nasan ai."

 

Lantai tunda ta fito da gudu bata zame ko ina ba sai makarantarsu, ko da ta je ta hango ana taran latti, aikuwa ta juya da gudun tsiya da zummar komawa inda ta fito.

Karaf Malam Muntasir ya hango ta, yasa yara yace su tabbatar sun kamota.

 

Ai sai aka fara ƴar tsere tsakanin Lantai da masu kamata.

 

Sai da suka ci gudu iyakar gudu sannan suka iso gidansu Lantai domin kwana ta dinga shiga tana yawo da su har dai ta gaji ta kama hanyar gidansu duk suna biye da ita.

 

Tana zuwa ta tsallake Inna Kande ta afka ɗaki tana cewa, "Inna Kande ki takanki wallahi suka kamaki ba ruwana kinga nima da ƙyar na sha."

Ta faɗa ɗaki ta rufe garam !

 

Inna Kande da tsabar tashin hankali yasa ta kasa tashi tsaye da rarrafe ta samu ta isa bayan darnin makewayensu ta ɓoye tana nishin tsorata, ga duk ta gurje guyawunta gun rarrafe.

 

Su kuwa yaran da aka tura kama Lantai sun cirko-cirko a ƙofar gidan, don sun san indai Inna Kande ta kama mutum akan jikarta Lantai sai ya ji jiki, domin bata duka bata zagi illa mintsinin mutum kawai da ranƙwashi a kai har sai yayi kuka.

Sannan idan Yayan Hafiz na nan ba ƙaramin duka yake haɗa ku yayi maku ba harda Lantai ɗin.

Wannan yasa yaran su kai tsaye ƙofar gidan cirko-cirko an rasa wanda zai shiga ya kamo Lantai a cikin gidan.

 

Sun san kuma ko dawa suke yawo ba zasu koma makaranta babu Lantai ba, Malam Muntasir ba zai ƙyalesu ba, sai ya dake su.

 

Inna Kande ta lafe sai kiran sunan Allah take tana ƙarawa,domin ƙauyen nasu ya lalace ko da yaushe ƴan daban dake maƙwabtaka da su suna shigowa su yi masu ɓarna su fice babu mai iya tanka masu domin duk ƙauraye ne, addu'ar da take Allah Ya sa basu bane Lantai ta jawo faɗa ba, idan kuwa su ne tabbas yau kashin kowa ya bushe a ƙauyen ga shi Yayanta Hafizu na maraya (Birni).

 

Lantai kuwa tana afkawa ɗakin ta rufe ta kama leƙe ta taga, don ganin ko sun shigo har cikin gidan? Sai ta hango Inna Kande na rarrafe tana kiran Ya Allah Ya Allah.

Ai sai ta kwashe da dariya ta cigaba da tsorata Inna Kanden don ta fahimci ta ɗauka su Barbushe ne suka kawo masu farmaki har cikin gidan.

 

Sai da ta tabbatar da sun gama jira sun tafi sannan ta fito tana kallon Inna Kande tana dariya ta ce, "Yo wai ke Inna Kande miye na hangoki kina rarrafe kamar wata ta goye ?

Sai yanzu Inna Kande ta fahimci lalatar Lantai ce ta motsa ta aikata mata haka, aikuwa ta zaburo da kuzarinta da nufin kama Lantai ɗin.

 

Ko da ganin hakan sai Lantai ta ruga waje da guda tana cewa, "Ho Inna Kande anji tsoro."

 

Caraf yaran su kai da ita basu zame ko ina ba sai makaranta.

Malam Muntasir ya tambaye su dalilin jimawarsu suka ba shi labarin yadda Lantai taita yawo da su kafin su kamota.

 

Office ɗin malamai yace ta je ta jira shi, don yana cikin koyawa ƴan aji biyar lokacin.

Lantai na ƙunƙunai ta isa office ɗin daya ke lokacin darasi ne dukkan malamai suna azuzuwa gun koyawa sai ita kaɗai cikin office ɗin.

Ta jima tana waige-waige a office ɗin zuwa can ta hango wani littafi bisa teburin Malam Aminu mai koya masu Hausa, da hanzari ta isa gaban teburin sai ta ga ashe na turanci ne, ta ja tsaki ta ce, "Ni da ko Hausa ban iya ba me zan ci da turanci ? Ta buɗe tayi kallon-kallo ta maida ta aje.

Kamar an ce ta kalli inda teburin Malam Muntasir yake, sai ta hango wani littafin, ta isa ta ɗauka tana tunanin ko miye shi ? Ta ga zanen budurwa tana hawaye kome yasata hawayen ? Lallai ya kamata tasan abin da ya sata hawayen amma ta yaya zata sani bayan bata iya karatu da rubutu ba? Tai ta juya littafin tana kallon matar dake jikin bangon littafin tana hawaye, sai kawai ta ɗaga rigarta ta saka littafin ta cusa rigar cikin wandonta ta koma waje guda ta natsu hada su tara hawaye a ido irin ta gaji da tsigunni a wajen.

 

Sai da Malam Muntasir ya gama koyawa ya nufi office ɗin yana tunanin yadda zai hukunta yarinyar domin dai bata ji ko da yaushe sai ya kamata da laifin makara, wata ranar ma bata zuwa makarantar kuma sam bata maida hankali ga karatun.

 

Lantai na hangoshi ta fara kuka wi-wi kamar gaske, ya dubeta yaga duk ta ɓata fuska da hawaye hadasu majina yace.

"Nuratu Kabir me yasa baki jin magana ne ?

Ta sake fashewa da kuka ta ce, "Na rantse Malam Inna ce tasa na makara ita ce ta aikeni siyen goro."

 

Girgiza kanshi yayi ke kullum in kikai laifi sai kice Innarki ce shin ita Innar bata san lokacin zuwa makaranta ba ne ?

 

Sai da ta tura baki, sannan ta ce, " Ta sani man cin goronne dai sai ta yi ko da yaushe amma ba zan sake ba don Allah kai haƙuri malam na rantse idan na kuma makara ka zane ni sarai."

 

Murmushi yayi yace,  "Kin tabbata idan kika sake laifi a makarantar nan na zane ki ?

Da sauri ta ɗaga kanta tana shan majinar dake fitowa daga hancinta.

 

Kofar fita ya nuna mata kafin tasashi amai.

Sai da ta riƙe littafin  sarai ta tabbatar da ya riƙu bai fita sannan ta fice daga office ɗin kamar wadda akaima sabon shayi.

Mamakin yadda take tafiyar yake domin yasan dai lafiyarta lau amma ji wata sabuwar tafiya ta ƴan koyo da take lokaci guda.

Kamar ya kirata sai kuma ya fasa ya shareta.

 

Hatta fice ta leƙo da fuskarta ta ce, "Malam yo wai kai me yasa kake kirana da sunan yankana ne bayan Yayana kawai ke kirana da sunan?

Banza yayi da ita ya cigaba da gyaran jarabawar da yake.

 

Taɓe bakinta tayi ta wuce kai tsaye gida ta nuna da murnarta don so take ta je gun Musa maƙwabcinsu Dake karatu a bunni ya karanta mata littafin macen nan mai kuka.

 

Har zuwa lokacin Inna Kande bata huce akan abin da tai mata ba, don haka ta jefar da jakar makarantar da hijabinta ta fito da littafin ta kwasa da gudu ta nufi gidansu Musa tana addu'a Allah Ya sa ya dawo daga bunni.

Tun daga nesa ta hango shi zaune ƙasan darbejiya yana karatu da wani littafi dogo a hannunshi ya duƙafa kamar wani Malamin zaure.

 

Tana isa da gudun ta zauna dirshan kusa da shi kafin ya ankara ta ƙwace handout ɗin dake hannunsa tana dariya ta miƙa masa wanda ta ɗauko office ta ce, "Don Allah Musa daure ka karanta min inji yadda akai take kuka wannan matar ita kuma."

 

"Nuratu manya ke har yanzu kina aji uku primary school baki iya karatun Hausa ba?

 

Taɓe bakinta tayi ta ce, "Yo Musa banda abinka kaima ba sai da ka je maraya ka iya ba ? Ko da kana irin makarantarmu ka iya ne ? Ta tsare shi da idanuwanta.

 

Littafin yake kallo ya dubeta yace, "Nuratu ke kam me ya haɗa ki da littafin soyayya tun yanzu ?

Washe baki tayi kamar gonar auduga ta ce, "Yo an ce maka ni na san ta ma ne ? Kawai dai ka karanta min ni na rantse na ƙagu naji yadda akai matar nan ke kuka Allah."

 

"INA HUJJAR TAKE ?

 

    Na

Nura Sada ( Nasimat)

 

Dalalo idanuwa waje tayi ta ce, "ka ambaci sunan namiji bayan hoton mace ce ke kuka ?

 

Dariya yayi sosai yace, " Sunan littafin INA HUJJAR TAKE ? Sunan wanda ya rubuta ne Nura Sada Nasimat ai."

 

"Uhmmn to ni dai ka koyamin yadda zan iya karantawa da kaina tunda ban fahimta idan ka karanta min ma."

 

"To shike nan amma sai idan za ki dinga zuwa makaranta ki daina makara sannan ki daina tsokanar yara faɗa kina dukansu sai na koya maki karatu da rubutu."

 

"Yo wallahi na amince kuma Allah daga yau ba zan sake makara ba ko Inna Kande batai zafafen safe da wuri ba zan wuce abina."

 

Tun a lokacin Musa ya fara kowa mata baƙaƙen Hausa.managarciya.com

 

Wace ce Nuratu (Lantai)??

 

 

 

 _Yanzu wasan zai fara ku dai ku bibiyi alƙalamin Haupha don jin wannan labari mai cike da abubuwa._