Zamfara: ‘Yan Sa Kai Sun Kashe 'Yan Bindiga  15 Bayan Tare Hanyar Dansadau

Zamfara: ‘Yan Sa Kai Sun Kashe 'Yan Bindiga  15 Bayan Tare Hanyar Dansadau

 

Tsagerun ‘yan bindiga a ranar Asabar sun rufe babban titin Gusau zuwa Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, Daily Trust ta rahoto. 

‘Yan bindigan sun dinga kai farmaki kan masu ababen hawa da matafiya a kan titin mai tsawon kilomita 100. 
An tattaro cewa ’yan ta’addan sun dinga kaiwa dubban  matafiya kan hanyar.
Na tsawon lokaci, jami’an tsaro suka dinga raka matafiya har zuwa garin Dansadau don gujewa farmaki, Matafiyan sun dinga raka jama’a a tawaga. 
Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu Dansadau ya sanar da Daily Trust cewa ‘yan bindigan sun rufe titin da niyyar garkuwa da mutane tare da halaka matafiya amma tawagar sojoji suka fatattake su da gaggawa. 
Dansadau yace: “Sun tsara kansu a wurare masu hatsari da ake kira Mashayar Zaki, wurin ya kasance inda masu ababen hawa ke tsoro. 
“Yanzu an gyara titin kuma matafiya na tafiya lafiya kalau duk da suna kiyayewa. 
Tun farko ‘yan bindigan sun kai farmaki Maigoge, wani yanki mai nisan kilomita 8 yammacin Dansadau amma suka yi artabu da ‘yan sa kai. 
‘Yan sa kan sun halaka 15 daga cikinsu, “Da safen nan, ‘yan bindigan sun dawo domin daukar fansa a yankin, sun zo da yawansu kuma a babura, jirgin yaki ya isa babu dadewa. 
“Jirgin yakin ya zagaya Dansadau sannan ya karasa kauyen Maigoge, Sai dai bamu da tabbacin me ya faru bayan zuwan jirgin.” 
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, bai riga da yayi tsokaci kan lamarin ba.