HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 32
Ta jima ba numfashi har Allah Ya kawo ƙawarta ta iske ta a halin, da farko ta ɗauka aljanunta ne suka tashi sai kuma ta fahimci suma tai, cikin sauri ta yayyafa mata ruwa sai ga shi kuwa ta farfaɗo tana ajiyar zuciya, sai kuma ta fashe da kuka mai ciwon gaske.
A'isha Yusuf ta ruɗe ta dinga tambayarta abin da akai mata take kuka amma ba amsa kukanta kawai take don haka A'isha ta ɗauki wayar Jiddah da zummar kiran Abubakar tasan shi ne kawai zai iya jin damuwar Jiddah ya bata haƙuri ko shawarar da zata natsu. Sai dai me? A'isha na ɗaukar wayar ta fasa ƙara tace, "Na shiga uku na lalace Ni A'isha me zan gani haka? E gaskiya ne kuka ya ganki Jiddah buɗe bakinki ki yi kuka kar da ki bar komai a ranki maida kuka ya zama hanyar wanke takaicinki tabbas ba zan hanaki yin wannan kukan ba... Ita ma kuma ya ci ƙarfinta ta rungume Jiddah su kai ta kuka, har gwara Jiddah bata iya ko furta kalma guda amma ita A'isha kukan take tana tsinewa Abubakar har da iyayensa.
A haka sauran ƙawayenta suka zo kowacce taga hotunan sai ta dafe ƙirji ta ambaci ta shiga uku me zata gani haka?
Cikin lokaci kaɗan wajen ya kacame da koke-koke tamkar gidan mutuwa, baki ɗaya sun tausayawa Jiddah yadda ta ɗauki so da ƙauna ta damƙa ma Abubakar amma shi ne ya saka mata da wannan muguwar sakayyar, tabbas ba ƙarya ake ba da akace wasu mazan babu tsoron Allah a tare da su kuma sun cika munafukai na gaske a shafin soyayya.
Har suka taso daga makarantar Jiddah bata furta ko da kalma guda ba, sai dai kukan da take rerawa kawai kamar wadda akai ma mutuwa.
Ko da ta isa gida kasa biyawa tai ta ɗauki yaranta kawai wuce wa tai ta shige ɗakinta ta dasa wani kukan, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama akan Abubakar, shin me yasa yai mata haka? Dama akwai yaudara a tsakaninsu? Me tai mai wanda zai sa ya yi mata wannan hukuncin? Ashe dama ba zata daina ganin baƙin cikin ɗa namiji ba? Me yasa maza su ke mata haka ne? Akan me take wahala a rayuwarta da maza? A fili tace, "Ya Allah kaga halin da nake ciki ka bi min haƙƙina ka saka mun Ni da Abubakar duk wanda ya cuci wani Allah ka sakama wanda aka cuta. Tabbas ban yafe maka ba Abubakar!
Haka ta kwana bata aikin komai sai kuka da tunanin abin da yasa Abubakar ya yaudareta.
Wasa-wasa ta shafe sati bata je makaranta ba, domin ciwon hawan jininta ya tashi sosai, kamar zata mutu, har sai da aka kwantar da ita asibiti tai kwana biyar jininta ya ƙi sauka.
Babu yadda Yayar Mamanta dake jinyar ta ba tai da ita ba, kan ta gaya mata damuwarta ba amma bata magana sai hawaye kawai lokaci zuwa lokaci da take zubarwa.
Ga shi duk lokacin da aka aunata jinin bai sauka sai ƙara sama yake, abin da ya ba likitocin mamaki kenan suka dinga mata faɗa kan ta cire damuwar dake ranta idan ba haka ba tabbas hawan jini zai mata muguwar illa.
Kaf ƙawayenta na makaranta sai da suka zo dubata, tabbas ta basu mamaki sun ci alwashin duk ranar da Abubakar ya dawo makarantar sai sun yi ma shi mafiyin abin da ya yi ma Jiddah.
Sai da shafe kwanaki goma cur a asibitin sannan jininta ya daidaita aka sallameta, ta koma gida tai wata irin rama tai fayau duk wanda ya ganta yasan ta sha jinyar ciwo mai zafin gaske.
Tun daga lokacin sai Jiddah ta koma shiru-shiru bata magana haka bata tankawa duk wani namiji balle a samu wanda zai ce yana sonta. Ta saka a ranta cewar babu ita ba sauran soyayya ta gama ta, domin ta amince da cewar duk maza halinsu guda basu da amana haka sun ƙware da cutar da zuciyar mace.
Abubakar kuwa, ya kira tura mata message ya ce, "Sweetheart don Allah ki yi haƙuri za ki ji Ni kwana biyu shiru, kin san ban da waya kuma ga tafiya bikin ƙanwata da aka riƙe Niger ya zo don haka za mu tafi can sai na dawo zan yi matuƙar kewarki koma ince ina cikin kewarki sosai abar ƙaunata."
Kuka ya ƙwace mata sosai, tabbas akwai abin da Abubakar ya ɗauke ta da yake wasa da hankalinta yake mata yawo da zuciya, shin wane fage ko fanni take a zuciyarsa? Tabbas ta jima tana jin labarin mayaudara amma bata taɓa haɗuwa da mayaudari irin Abubakar ba, tsabar yaudara ka yi auren ma sai ka ci-gaba da yaudara?
Sai da tai da gaske ta tura mai reply da "Na gode Allah Ya tsare hanya."
Tun daga lokacin bai sake kiranta ba, haka bai sake yi mata message ba, sai da aka fi sati biyu sannan ya turo mata message ɗin ya dawo Nigeria.
Zuwa yanzu ta dake ma zuciyarta so take taga iyakar gudun ruwansa don haka duk lokacin daya turo mata saƙon soyayya tana danne zuciyarta ta maida mai ko ba yawa.
So take su haɗu ido da ido ta nuna mai hotunan aurensa don taga me zai yi kuma me zai ce mata, don haka take biye mai duk da akwai sauyi sosai a tsakaninsu yanzu waya ba sosai ba text ma ba sosai ba, amma duk ta share shi hatta ƙorafin ya daina kulawa da ita ta daina mai.
A da kuwa komin dare idan ɗaya daga cikinsu ya farka daga barci sai ya tada ɗayan haka wayarsu ce ƙarshen barcin kowane haka suna tashi asuba kafin su yi alwala sai sun waya haka idan suka gama sai sun waya, amma ban da yanzu waya zuwa karfe takwas sun gama na dare bai kiranta da asuba ko da sassafe duk wayarsa a rufe take ma.
Ranar Litinin ya ce mata zai dawo makaranta don haka ta gayama ƙawarta A'isha Yusuf cikin baƙin ciki A'ishar tace, "To ina ruwana da zuwan shi? Matsiyaci wallahi ya yi asarar da ba zai taɓa maida irinta ba."
Bayan sun fito class sai ga kiran Abubakar suna zaune bayan class suna hutawa , ta gaya mai inda take sai ga shi kuwa ya sha sabuwar shadda sai washe baki yake ya yi gwanin kyau abin sa alamar angonci na kai mai karo yadda ya kamata.
A'isha kamar ta tashi sai kuma taga rashin dacewar tashinta don haka ta gyara zamanta sosai ta tsira mai ido yana nufo su ji take tamkar ta rufe shi da duka yana kawowa inda suke.
Da sallamarsa ya iso gun ya leƙa fuskar Jiddah ya ce, "Wow ! Na ji daɗin ganinki wallahi na shiga tashin hankali da muguwar kewarki sosai Jiddata."
Jiddah dai ta sadda kanta ƙasa kawai tana murmushi mai cike da takaici bata ce mai komai ba.
Ya amshi wayarta dake hannunta yana dubawa ya ce, "Mu ga sabbin hotunan da akai min da ban nan naga kin ƙara haske da kyau kamar ba ki yi kewa ta ba."
Karaf A'isha Yusuf tace, "Ciki gare ai kaga dole tai haske da kyau ai."
Cikin murmushin wasa ya ce, "Haba Aisha kar da ki shiga tsakanina da matata man daga zuwa na ki bari na bata haƙurin rashin gani na da bata yi na barkatai man."
A'isha tai dariya tace, "Daman ina fa zata ganka tunda ka yi naka wajen?"
Yana buɗe wajen hotuna ya ci karo da hotunan bikinsa kawai gani mu kai ya yi tsuru-tsuru ya kasa haɗa ido da Aisha ma balle Jiddah.
Amma da yake ɗan duniya ne sai ya wayance ya ce, "Jiddah naga sai wani haɗe rai kike yi kamar baki amshi tuban da nayi maki ba? Kin san dai ina sonki ba zan iya barinki ba duk rintsi...
"Kai dakata Malam! Kada ka rainawa mutane hankali a karo na barkatai mana, kana nufin yanzu ma duk da kaga hotunan aurenka a wayarta ba zaka sararama yaudararta ba? Tabbas ka ci uwar rainin wayau rai Ni kai kam."
Tsugunnawa ya yi ƙasa ya ce, "Don Allah ku fahimce ni wallahi ina son Jiddah amma lokacin dana haɗu da ita akwai maganar wata a kaina sai dai sonta ya rufe min ido na kasa gaya mata gaskiya kawai nasa a raina idan nayi aurena zan dawo na aure ta ita ma a ta biyu."
"To ai hakan ba zai yiyu ba Abubakar Yau ta zama ranar ƙarshe a tsakanina da kai ka manta da Ni kamar yadda na manta da kai." Cewar Jiddah kenan ta bar gun bayan ta fisge wayarta a gun shi.
Ya dinga kwaɗa mata kira amma ko waigen inda yake ba tai ba tai tafiyarsa.
A'isha ta dube shi tace, "Ka dai ji kunya wallahi kuma ka aje a ranka sai ka yi nadamar abin da kai ma Jiddah insha Allah ba zaka taɓa jin daɗin rayuwar aurenka ba tunda ka yaudari ƙawata."
Ita ma ta wuce ta bar shi gun a tsugunne.
Tun daga lokacin ko da yaushe sai Abubakar ya kira wayar Jiddah amma bata ɗagawa haka idan ya turo mata saƙo bata maida mai reply.
Ya takura mata a makaranta duk inda tai yana biye da ita yana bata haƙuri amma ita bata yi mai magana, takan kalle shi sau guda ta kauda kanta.
Hakan yasa ya tsare ta yana kuka ya ce idan ta amince zai saki matarsa ya aureta indai zata yafe mai ta amince da shi da soyayyarsa.
Ita kuma sai ta ji ya ƙara bata haushi domin duk namijin da zai iya sakin matarsa ta gida don ta waje tabbas ita ma wata rana haka zai sake ta don ya auro wata.
Sai kawai tai blocking na number shi da duk wani account na chat ɗinta da shi.
Ta dinga saka liƙab a makarantar don haka sai ta samu sauƙin shi sosai.
Wata rana da ya gane ita ce ke saka nikab ya tare ta zai fara magiyar da ya saba yi mata ta tsaida shi tace, "Abubakar anya akwai zuciyar imani da tausayi a jikinka kuwa? Anya kuwa kana da adalci ka san shi ma kuwa? Yanzu idan akai ɗiyar cikinka abin da kai min zaka ji haushin hakan kuwa? Abubakar me yasa wasu mazan ba ku da adalci ne? Me yasa kuke murna da karyawa mace zuciya ne? Tabbas zuciyarku kan mata bata da tausayi ko da yaushe cikin muradin sauraren kukan ɗiya mace take.
To a Yau a yanzun nake son mu kawo ƙarshen alaƙar tsakaninmu, domin na tsane ka na tsani soyayya ba zan taɓa manta cin amanar da kai min ba Abubakar ka manta da Ni ka riƙe matarka."
Ta tafiyarta ta bar shi gun yana goge zufa.
Wannan shi ne ƙarshen soyayyar Jiddah da Abubakar.
Tafiya kwana nesa sai ga Jiddah ta gama karatun ta, da kanta ta ga dacewar zuwa Kano gun Hajjo tai kwana biyu don kawai ta huta don haka ta shiryawa yaranta kayansu duka ta kaiwa Mama ta aje masu kayan abinci masu yawa tai bankwana da su ta wuce Kano tana jin ta wasai ba ta da wata damuwa ko takaici domin ta riga ta fahimci cewar soyayya da aure su neasu saka mace a damuwa to insha Allah ta yi nesa da su ba zata sake yin su ba har abada, zata kalli kowane namiji da kallon matsala a gareta zata kalli kowane namiji da kallon marar tausayi a gareta don haka zata zama cikin shirin korar soyayya ko ta halin ƙaƙa daga rayuwarta.
Idan akwai abin da Jiddah ta tsana to kalmar ina sonki ce Jiddah.
Ko taga namiji na mata kallon nan nasu na yaudara sai taji nan take ta tsane shi.
KANO TA DABO TUMBIN GIWA...
Tun da Jiddah ta iso Kano take jin ta cike da farin ciki da annashuwa, bata da wata damuwa ko tashin hankali ko da yaushe tana waya da Mama da yaranta don haka sai gogewa take tana ƙara waye wa, ganin zamanta haka nan ya yi yawa yasa ta shiga wata makarantar koyar da sana'a kala-kala don rage lokaci.
Tun zuwan Jiddah Kano Mustapha ke cikin farin ciki ba kamar da ya fahimci cewar Jiddah zata jima a garin sai ya ji tamkar an yi mai bushara da gidan aljanna.
Ita kuma ɓangaren Jiddah a kwanakin nan tana yawan mafarkin Uncle Salim da wannan dogon mutumin da tun tana yarinya take mafarkinsa. Kamar Yau da take kwance tana barci tai mafarkin gata zaune ta yi tagumi, gefenta Uncle Salim na zaune ya tsira mata ido kamar mai nazarinta, ya ja ajiyar zuciya ya ce, "Jiddah kin san cewa hanyar da kike ba mai ɓullewa bace ba? Ki sani saka tsanar soyayya a ranki ba abun tutiya bane ba, shin ba ki son ace Yau gaki kin yi aure ba Deeni na kallonki yana ganin yadda kika cigaba ba kika cika burinki na auren soyayya ba ya ji nadama da takaicin abin da ya yi maki a baya ba? Ko kin ɗauka har zuwa yanzu Deeni bai jin takaicin rabuwa da ke ne? To ki sani Ni dai idan zan baki shawara ki ji to ga wanda naga zai maye maki duk wani gurbin baƙin cikinki da farin ciki Jiddah." Ya kama mutumin zai jiyo da fuskarsa kenan ta farka daga barcin ba tare da ta ga fuskar ko waye ba Uncle Salim ke ta mata maganarsa.
Wanka tai ta shirya zata shiga gidan Bilkisu kenan sai ta kalli gidan Mustapha kawai sai ta ja ta tsaya ta fiddo wayarta daga aljihun rigarta ta nemo lambar ta kira shi, har ta katse bai ɗauka ba, sai kawai ta sa a ranta idan ta sake kira bai ɗauka ba zata goge lambar daga wayarta baki ɗaya ta share shi tunda daman ba wani abu ke tsakaninsu ba ko da sai gaisuwa idan sun ƙure ma juna. Sai dai tana fara ringing ya ɗauka ya ce, "Salamu alaikum."
Ita ma ta amsa mai tai shiru, kamar daga sama taji ya ce, "Jiddah mutanen ƙauye an shigo birni ne?"
Dariya maganar ta bata wai mutanen ƙauye watau ya koya daga Uncle Salim kenan shi ne ke ce mata hakan.
Cikin sautin dariyarta tace, "Birni ko ƙauye dai? Ai bai kamata ba kace na zo birni ba tunda kowa yasan daga birni nake don yadda Kano take State haka ma Barno take state don haka ka kashe wuta kawai duk kanwar ja ce."
Shima cikin dariya mai cike da farin ciki ya ce, "Ba don na yarda ba fa, amma ki shirya na kai ki shan ice cream ki ga gari kuma nasan kin yarda da maganata."
Kamar tace ya barshi sai kuma ta samu bakinta da amsa mai cewa sai ya fito ɗin.
Ta kashe wayar tana murmushi ta shige gidan Bilkisu, sun taɓa fira kaɗan wayarta tai ƙara tana dubawa ta ga Mustapha ne don haka ta ɗauka, cikin fara'a ya ce, "Ki fito mu je ina ƙofar gidan."
Cikin sauri ta miƙe ta nufi waje tana ma Bilkisu sai ta dawo.
Tun daga zauren gidan Bilkisu take jin ƙamshin turarensa wanda tunin duniya ƙamshin ke matuƙar birge ta sosai take son ƙamshi musamman na turare sai kawai ta samu kanta da murmushi.
Yana zaune kan mashin ya sha sabuwar shadda sai ƙyalli take duk da cikin duhu ne, shi kan shi tun da ta fito yake kallonta yana jin nishaɗi a ranshi kamar har sun fara soyayya da ita ne irin za su fita yawon nan na shaƙatawa, har ta iso gun bai san ta isa ba, sai da ta maimaita sallamar sannan ya dawo daga duniyar tunani.
Nan take ƙamshin turarensu ya haɗe da na juna sai wani sansanyan ƙamshi ya bayyana gun mai daɗin shaƙa.
Kamar su zauna ya tasa ta gaba yai ta kallo haka yake ji sai kuma ya goya ta suka nufi cikin garin domin ya gwada mata gari kamar yadda ya ce.
Wajajen shan iska ya kaita sosai, duk inda suka je ban da tsokanarta babu abin da yake, ita kanta ta yi mamakin yadda bakinta ya buɗe take maida mai martanin tsokanar da yake mata.
Sai wajen tara da rabi suka dawo da leda cike da ice cream da kaza da sauran tarkace, ko da suka iso ƙofar gidan sun jima tana tsaye yana zaune kan mashin suna ƙara tsokanar juna kamar sun saba da juna sai da goma ta buga sannan su kai bankwana ya buga mashin ɗinsa ya kama hanyar fita unguwar ta kira shi a waya cikin mamaki tace, "Malam ya da koma wa yawo bayan dare ya yi?"
Yana dariya ya ce, "Wa ? Ai sha biyun dare marecen Kura, ba yanzu muke dawowa ba mu."
"To Allah Ya tsare Ya dawo da kai lafiya."
Cike da jin daɗi ya amsa da "Amin Ya Allah na gode, idan na dawo zan kira ki."
Ta amsa da to kawai ta shige gidan, har Hajjo tai barci ma lokacin don haka ita ta rufe gidan ta ware abubuwan da ta dawo da su ta aje don ta ƙoshi tai wanka ta saka kayan barci ta kwanta.
Yana shan kwanar gidan ya samu wani kwalbati ya kashe mashin ɗin ya sauka ya zauna ya cigaba da tunano abin da ya faru da shi da Jiddah a yanzu.
Muryarta kawai yake ji a kunnensa yana farin ciki ji yake nishadi nata ƙara ƙarfi a zuciyarsa.
Komai nata ya yi mai, yadda yake buƙata, gata kyakkyawar gaske ajin farko, ina ma Allah zai wanke mai baƙin cikinsa ta hanyar mallaka mai ita matsayin sakayyar rayuwar aurensa? Tabbas da ya yi matuƙar farin ciki kuma ya amince cewar bai yi haƙurin banza ba.
Sai wajen sha ɗaya ya tashi ya je shagon da yake siyen fura ya siya ya koma gida, tuki yake amma ji yake kamar cikin sararin samaniya yake take don nishaɗi.
Sai da ya gama komai kamar yadda ya saba bai iya kwanciya bai wanka ba ya saka doguwar rigar barcinsa ya jawo waya, sai kuma ya samu kansa da tunanin me ya kamata ya yi ne? Kiranta zai yi ko text zai tura mata? Sai kawai ya samu kanshi da tura mata text kamar haka.
"Ban san haka ake farin ciki ba idan akai irin wannan fitar ba sai a Yau don haka gobe ma ina nemanki don mu sake fita ba mamaki farin cikin zai fi na Yau, ina maki ban gajiya sosai."
Jiddah na kwance tana game a wayarta ta ji alamar shigowar saƙo don haka ta duba sai ta ga na Mustapha ne, ita ma murmushi tai ta samu kanta da maida mai amsa kamar haka.
"Tabbas akwai farin ciki kam, don ji nayi tamkar mu cigaba da tafiya a haka har abada. Gajiya kai za a tambaya kai da ka sake fita bayan mun dawo."
Yana ta kallon saƙon daya tura mata nata ya shigo ya buɗe cike da nishaɗi ya karanta.
Sai da ya yi tsalle ya fasa ihu don murna kana ya koma ya kwanta ya tura mata.
"Kin ji ta kamar gaske, bayan na lura da yadda kika ƙagara mu dawo gida kamar na sace ki shi ne za ki ce hakan."
Ba ƙaramar dariya tai ba ganin abin da ya ce, don haka ita ma sai tace mai.
"Ba dole ba na ƙagara ka maido Ni gida ba kada ka saida Ni ka samu kuɗi ka ga kyakkyawar da babu irinta a ƙauyenku."
Sosai ya yi dariya da abin da tace , sai ya samu kanshi da ce mata.
"Haba dai ai duk kyawun naki naga baki kai Jiddah ta ba ko? Nasan kina ganinta za ki ce dama na gaya maki hakan."
Girgiza kanta tai tana murmushi tace mai.
"Ikon Allah! Ai tunda ta ci sunana dole daman nasan za tai kyau don haka albarkar nawa ne ya shafe ta.
Sai da safe ka kula da kanka barci zan."
Tana tura mai ta kashe wayarta ta gyara kwanciyarta ta kwanta tana jin nishaɗi sosai a ranta.
Mustapha kam kasa barci ya yi bayan ya tura mata saƙon sai da safen shima.
Ganin ya kasa runtsawa yasa ya tashi ya ɗauro alwala ya kama sallah yana neman zaɓin Ubangiji tsakaninsa da Jiddah.
Sai wajen ƙarfe biyu da rabi ya sallame ya kwanta yana mai jin sabuwar soyayyarta na ratsa dukkan hanyoyin jijiyoyin jikinsa, a hankali ya furta, "Princess sai da safe zan kula kamar yadda ki ka ce ɗin." Ya shafa addu'a ya kwanta barci mai natsuwa ya ɗauke shi.
Washegari tunda safe Bilkisu ta zagayo gun Jiddah da wayarta sabuwa tace, "Don Allah ki turamin WhatsApp idan kina da shi wani littafi aka ce min ana saki a wani group don haka na nace sai da maigidan ya sai min wayar nan Yau."
Jiddah ta ɗauki wayarta ta tura mata ta buɗe tace, "Ni kam ban yi sam bai dame ni ba wallahi kwata-kwata."
Bilkisu cike da mamaki tace "Ai kuwa an barki baya wallahi don a chat babu abin da babu wallahi dama kin buɗe kin ga me duniya ke ciki, har wanda baki tunani sai ki ga kun haɗu da shi a can."
"Tabbas ina son na haɗu da Alawiyya kam Bilkisu da nasan zan ganta da zan buɗe."
Bilkisu tace "Tabbas za ki iya ganinta indai tana yi ita ma balle yanzu chat ya ga me duniyar kowa yi yake ."
Cikin sauri Jiddah ta buɗe facebook, WhatsApp, Instagram duk ta saka sunanta wanda Alawiyya zata iya gane ta watau Jiddah Iyami Lagos.
Nan dai su kai ta fira da Bilkisu har tace mata zata ba da Number ta a saka ta groups ɗin da ake posting littafai da abubuwan ƙaruwa Jiddah tace ta gode.
Da rana tana kwance tana duba mutanen dake cikin WhatsApp ɗinta sai taga lambar Mustapha shi ma ashe yana chat don haka tai mai sallama ba a jima ba ya maido mata da sallama yana tambayar ina ta ɓoye duk Yau bai ga wulginta ba.
Sun jima suna fira da shi ta gaji ta sauka ya ce anjima ta shirya za su fita tace to.
Facebook ta koma taga wani posting da mutane ke ta ka-ce-na-ce akan shi don haka sai ta karanta abin da akai posting ɗin sosai.
Wata uwar ƙara ta saka ta ruga gun Hajjo tana kuka tana cewa, "Wallahi ƙarya su ke mata ina bayanki sosai kuwa nasan Mama ba zata kashe mijinta ba Alawiyya."
Hajjo ta dube ta sosai jin ta ambaci Alawiyya tace, "Ina kika ga Alawiyyar ke kuma? Shekara da shekaru har Yau kin kasa manta ta ba mamaki ita ta jima da manta ki ma."
Jiddah ta fashe da kuka ta tashi ta shiga ɗaki sai gata ɗauke da jakar goyo bayanta ta dubi Hajjo tace, "Hajjo ki yi haƙuri zan tafi Kaduna a yanzu ba sai gobe ba, domin in gana da Alawiyya."
Hajjo ta taɓe bakinta tace "Sai kin dawo, amma wallahi ko sisi ban baki Allah Ya kai ki lafiya."
Ita dai Jiddah kuka kawai take, don haka ta fice hankali tashe, sai dai dole ta tsaya don ganin Mustapha gabanta hankalinsa a tashe ganin tana kuka.
"Jiddah ina za ki kina kuka?"
Cikin kuka tace, "Kaduna zan je gun Alawiyya Yau Allah Ya nuna min Alawiyya."
Wayarta ta fiddo ta nuna mai hoton Alawiyya da Mamarta a lissafi kuma Yau ne za a shiga kotu.
Kowa yasan Jiddah yasan Alawiyya kowa yasan Salim yasan labarin Jiddah don haka ya tuna lokacin da Salim ya sa shi su kai ta neman Alawiyya basu ganta ba, don haka ya ce "Tabbas dole ki yi kuka ba zan barki ki je ke kaɗai ba don haka bari na fito mu tafi tare."
Kafin tace komai ya faɗa gidansa.
Bata jima ba sai gashi ya fito suka tsaida keke napep ya kaisu tasha suka shiga motar Kaduna har zuwa lokacin Jiddah kuka take.
To masu karatu mu haɗe a kashi na gaba don jin yadda zata kaya.
Taku a kullum Haupha 