DUHU DA HASKE: Fita Ta 16

DUHU DA HASKE: Fita Ta 16


  *DUHU DA HASKE: 


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 16*


                 ~Yau tunda safe manal ta tashi ta bar man kwance akan gado yana bacci fitowa tayi ta share gidan duk tayi mopping tasa turaren wuta, kitchen ta shiga ta fara girkin breakfast saida ta gama ta kwashe ta kai falon babu wanda ya fito har yanzu, komawa ɗaki tayi ta zauna a gefen man dake bacci, kallonshi take yi tana murmushi, soyayyan Abdool daban yake a ranta ji take zata iya rabuwa da kowa akanshi, zata iya yin komai akanshi, tashi tayi zata tafi ya rike mata hanu, murmushi tayi bata juyo ba yace "kin gama kallona ne?"
fizge hanunta tayi "nidai bana kallonka"
yace "karya kina kallona"
tana yaye mayafin kanta tace "noo"
fizgota yayi ta faɗo kanshi zata tashi ya danneta yace "ba inda zakije kema saina kalleki"
kwacewa ta fara yaki sakinta, bakinshi ya kai gefen wuyanta ya fara kissing nata, kwacewa takeyi tace "muje kayi breakfast"
da gudu ameesha ta shigo tace "man?"
saurin juyawa tayi tace "so..so..sorry na manta ne"
zata tafi yace "my meesha"
tsayawa tayi bata juyo ba, yace "kizo"
kin zuwa tayi tace "umma ce ta kirani tana jin jikin kamar zai tashi na manta ne na shigo kuyi hakuri"
fita tayi, manal da takejin kamar wuta a kirjinta ta tashi da sauri tace "umma babu lafiya? muje mu dubata"
tashi yayi suka fita tare, ɗakin umman sukaje ameesha ta hau gadon tana cewa "sannu umma"
kallon ameesha tayi tace "yawwa ameesha ba wani ciwo bane fa, daga faɗa miki har kin fito da damuwa shiyasa banason faɗa miki abu ai"
dariya tayi tace "to umma.."
manal ce tayi sallama, shiru sukayi ta zauna kusa da umma tace "umma sannu wai bakida lafiya"
a takaice tace "yawwa"
man ya zauna kusa da ameesha yace "umma sannu"
tace "yawwa abdool ya ka tashi?"
yace "lafiya ƙalau ya jikin?"
tace "Alhmdllh"
yace "umma muje kici abinci sai kisha magani"
Imran dake bacci ya tashi yana murza ido, da sauri yace "ameesha yaushe kikazo?"
tace "ɗazu nazo"
zuwa yayi ya zauna kusa da ita yace "bakya zuwa yanzu nayi kewarki sai naje gidanku kuma bakya gida kin tafi wajen aiki kafin na tashi daga bacci"
tace "sorry dear zan rinƙa zuwa ka ganni"
umma tace "ameesha jeki mana girki"
man yayi saurin cewa "manal tayi girki"

"Ameesha nace tayi girki ko baka jini bane?"
shiru yayi, manal ta kasa ƙasa take aikawa umma wani kallo me wuyan fassara, danne ɓacin rai tayi tace "umma kiyi hakuri kici abincin kisha magani kiyi hakuri"
ɗauke kai tayi, ameesha ta rike hanun umma tace "umma muje kici tunda anyi abinci babu amfanin dafa wani"
zata yi magana tace "mujeeee"
tashi tayi ba dan taso ba suka fita, Imran ya bisu sai manal da man ne a ɗakin, ta sunkuyar da kai tayi shiru, a hankali ya matso kusa da ita ya rike hanunta yace "baby"
dago idanunta tayi ta kalleshi yayi mata dariyanshi me kyau yace "kar kiyi fushi komai zaiyi daidai"
tace "zuwa yaushe man? basa sona kullum ina kokari naga sun soni amma duk sun tsaneni"
yace "no basu tsaneki ba, koda sun tsaneki ni ba ina sanki ba?"
gyaɗa kai tayi, yace "yimin kiss"
murmushi tayi ta mishi kiss a gefen kumatu yace "good girl muje muyi breakfast"
tashi sukayi suka nufi falon, ameesha tana zaune kusa da umma tana bata abincin, Imran ma yana ci badan abincin yayi daɗi ba sai dan ameesha data sasu dole, zama sukayi man ya zuba mata a plate, ɗauka tayi ta fara ci, shima ci ya fara, umma ta fara tari da sauri manal ta mika mata ruwa, a fusace tace "nace ki bani ruwa ne? ko dama kece kike..."
ameesha ce ta hanata magana ganin manal ɗin ta fara dunƙule hanu tana huci ƙasa ƙasa idanunta suka canja kala, man baiyi magana ba yana cin abinci kanshi kasa, tashi umma tayi a fusace zata tafi, manal ta faki idonsu tasa mata kafa "Ahhhhh"
kara umma tayi jin wani azaban zafi daya ziyarci jikinta, Imran a firgice ya kalleta sannan ya kalli manal, ameesha ma kallonta tayi, da gudu suka tashi suna ɗaga umma kasa tashi tayi, saida man yasa hanu kafin ta iya tashi, kafanta kamar ya fita a jikinta ga hanunta da taji yayi kara, cikin azaba ta kalli manal wacce take cewa "sannu umma"
tace "kafa kika samin na faɗi? anya zakiyi albarka kuwa?"
man rufe ido yayi cikin ɓacin rai yace "wai umma me haka ne? kin tashi cikin fushi zaki tafi kin faɗi kuma kice tasa miki kafa?"
umma cike da mamaki da ciwo tace "man kenan karya nayi?"
yace "bance kinyi karya ba amma gaskiya tsanan yayi yawa duk kokarin da take na ganin ta saku farin ciki bakwa gani"
da ido kawai umma take binshi, Imran wani kallo yake aikawa manal, cikin zafin nama ya tashi ya wanketa da mari, a bayan man ta ɓuya tana ɓoye fuskanta, man ma cikin ɓacin rai ya ɗaukeshi da mari, dafa kunci yayi yana kallonshi, ameesha cak ta tsaya tana kallonsu ta kasa cewa komai, Imran yace "ka mareni akan wacce tasa kafa umma ta faɗi?"
yace "na mareka ko zaka rama ne?"
dunƙule hanu yayi da sauri ameesha ta rikeshi, girgiza mishi kai tayi man yaja hanun manal suka tafi, a hankali ta juyo ta yadda ba zai ganta ba, suka haɗa ido da ameesha, kashe mata ido tayi sannan tayi kyakkyawan murmushi, ameesha ji tayi kamar zata faɗi har suka shiga ɗaki tana kallonsu, a hankali ta durkusa wajen umma tana duba hanunta, da taimakon Imran suka shigar mata da hanun daya gurɗe, zama tayi a wajen tana kuka, da kyar suka ameesha suka lallasheta, saida tayi bacci ameesha ta tashi cikin mutuwan jiki ta tafi gida, koda taje gida kasa magana tayi ta shiga ɗaki ta kwanta tayi shiru tana tuna abinda ya faru.

man yana tare da ita har dare basu fito ba, duk hanyan da zaibi ya kwantar mata da hankali saida yabi, cikin hawaye ta kalli man da shima yake hawaye yana rabata da kayan jikinta, a hankali tace "man ba zakamin komai da zafi ba?"
gyaɗa kai yayi baiyi magana ba, runtse ido tayi ta kankameshi tana jin zafi lokacin daya shiga jikinta, numfashi me nauyi ya sauke hawaye suna wanke mishi fuska, cikin nannauyan murya yace "sannu"
manal bata taɓa jin haka ba tunda take a rayuwarta sai yau, tana kallon films kam amma bata taɓa aikatawa ba sai yanzu da man yake kokarin maidata cikakkiyar mace, a hankali ya fara loosing control ɗinshi, saide bayaso yayi mata illa kamar yadda zuciyanta yake cike da illa, ganin ta fara kuka ya haɗa bakinshi da nata, kissing nata yake cikin natsuwa yana control ɗin kanshi, da kyar ya samu hanya me kyau sabida shima ba sani yayi ba, sunyi good 2hours a hankali ya zame jikinshi daga nata ya koma gefe yana sauke numfashi me nauyi, saida ya ɗan nutsu kafin yace "sorry"
shiru tayi, ya rike hanunta shima yayi shiru, tace "kaini toilet nayi wanka zanyi sallan Isha"
yace "to"
ɗagata yayi ya kaita cikin toilet ɗin yasa mata ruwan zafi sosai, siririn kara tayi lokacin da ruwan zafin ya shiga jikinta, cikin tausayinta yace "sorry"
ta gama wankan cikin dauriya tayi alwala, saida ya kaita ɗaki ya shinfiɗa mata sallaya tareda bata dogon hijabi kafin shima ya shiga ya fara wanka, rufe ido yayi ya rasa kukan me yake yi, da haka ya gama wankan ya fito ɗaure da towel ta idar da sallan ta fara kallonshi, tana jinta tanada kyau amma yau da taga asalin halittan Abdool sai taji duk ta raina kanta, murmushi yayi mata lokacin da yasa jallabiya, itama ta mayar mishi shimfiɗa sallaya yayi, ya tada salla, tana kallonshi ko ɗauke ido batayi har ya idar da sallan kwanciya yayi a wajen ya ɗaura kanshi a cinyarta ya rufe ido kamar me bacci, ya jima a haka kafin tace "bacci nake ji"
tashi yayi ya ɗauketa cak ya kaita kan gado, shima hawa yayi ya rungumeta a haka suka fara bacci.

saida sukayi kwana biyu bai fita ko ina ba yana kula da ita, a kwana na uku tana zaune ta marairaice tace "Abdool kaje company yau nifa na warke ina lafiya ƙalau"
pillow ya janyo ya kwanta tareda juya mata baya yace "babu inda zanje ina tare dake"
juya baya tayi ta gaji da rokonshi, tayi shiru, jin shesheƙan kuka ya tashi da wuri yana kallon bayanta data juya mishi, jikinshi yana mutuwa idan tana kuka, yace "to shikenan zan je"
juyowa tayi tana dariya tace "da gaske?"
gyaɗa kai yayi yace "eh"
tashi yayi ya fara shiri, zuwa tayi gabanshi ta fara shiryashi, yayi kyau cikin coffee dress tasa mishi hula kafin ta rungumeshi tace "kayi kyau sosai"
yace "thank you boss"
turo baki tayi tace "yanzu ai kaine boss ba company a hanunka yake ba?"
yace "kece dai ni rikon kwarya nayi"
tana rike da hanunshi ta rakashi har kofa, umma tana tsaye a bakin kofan ɗakinta ta harɗe hanu a kirji tana kallonsu, murmushi tayi tace "yau Abdulrahman ne yayi kwana uku baizo ya ganni ba kuma bai damu ba?"
saida ta rakashi ta juyo zata koma ɗaki sukayi ido huɗu da umma, ɗauke kai tayi da sauri ta tafi ɗaki.

man yana fita a gidan ya wuce gidansu ameesha domin su tafi tare, hon yayi tayi kamar yadda ya saba, ganin bata fito ba ya fito daga motan ya shiga ciki, tun a bakin kofa yace "meesha fito mu tafi"
fahad wanda yake kwance a falon yana karatu da glass a idonshi fari bai kalleshi ba yace "ta tafi"
da mamaki yace "ta tafi kuma da kafa?"
yana cigaba da karatun a takaice yace "ka manta tanada mashin ne? ai dashi take zuwa aiki kullum"
ganin yadda yake bashi amsan yace "wai me yake faruwa?"
fahad yace "zuciyanta karye yake, duk abinda take yi kawai tana yi ne dabida tanada dauriya da kawaici kayi tafiyarka kada ka kara karya mata zuciya akan wanda take ciki"
yace "me kake faɗa ne fahad"

shiru yayi mishi yana karatunshi bai kara amsawa ba, Anty ce ta shigo tace "tashi kaje kayi wanka fahad"
ganin man tace "Abdool kaine da safen nan?"
yace "nine Anty ina kwana"
tace "lafiya ƙalau ya matar taka?"
a hankali yace "tana lafiya"
tace "madalla"
cikin sanyin jiki yace "na tafi"
basu kulashi sosai ba har ya fita, motarshi ya shiga yace "zuciyanta a karye?"
baije company farko ba wajen aikinta yaje, ya tsaya ya cewa megadi ayi mata magana, tace ace tana aiki boss nata ya hanata fita, shiru yayi jikinshi a mace yace "to"
har zai tafi sai kuma ya fito daga motan ya shiga ciki, tana zaune akan kujera tana aiki gefenta wata ce itama tana rubutu sai dariya ameesha take ya kalleta ta rame kaɗan amma tayi kyau sosai cikin dogon riga baƙi da mayafi baki, kamar kullum dariya baya yankewa a fuskanta, a hankali yayi murmushi ya karaso, tana ganinshi tace "man"
yace "meesha kin tafi kin barni"
tace "no ba haka bane sauri nake kuma banso na dameka"
gani yayi tana cigaba da rubutun bata bashi attention sosai ba, yace "to zan tafi anjima zaki jirani?"
girgiza kai tayi tace "Anty tace naje na karɓa mata ɗinkinta ina gama aikinnan zan tafi kuma ba zan dawo ba sai gobe"
yace "to zamu haɗu a gida"
tace "okay"
yace "na tafi"
gani yayi bata tashi kamar yadda ta saba ba tace "okay bye"
cigaba tayi da rubutu tana bawa yarinyar labari tana dariya, har yaje bakin kofa ya kara juyowa ya kalleta bata kallonshi idonta akan takaddan, yaji babu daɗi sosai, yaga canji a tareda ita, a hankali ya shiga mota yana driving cikin rashin kuzari, da haka ya isa company ya fito daga motan, yana shiga su faruk suka fara ce mishi "ango ango ango"
ɓata rai yayi yace "banson tsokana fa"
shiga ciki yayi ya zauna a office nashi ya fara aiki.

yamma likis ameesha ta karɓo ɗinkin Anty haɗe dana umma ta kai musu tare, zama tayi tana bawa anty nata sannan tace "idan na huta zan kaiwa umma nata"
Anty tace "yayi kyau Allah miki albarka"
tace "ameen"
Imran yana kwance a ɗakin umma yana bacci, tashinshi tayi tace "kai tashi babu kyau baccin yamma"
turo baki yayi yace "to umma"
zama yayi kawai yana ɓata rai ya tsani a tasheshi a bacci, wankinta ta ɗauko zata fita dashi tace "ina kayan da kasa jiya? kawo na wanke maka dan naga fari ne"
yace "to"
ɗauko mata yayi ta karɓa ta haɗa da wankinta ta fita, tana fita ya koma ya kwanta yaci gaba da baccin, a cikin gida ta aje wankin ta ɗibo ruwa da omo ta fara wanki, manal ta ɗaga labulen window tana karewa umma kallo, riga da wando ne a jikinta wando me faɗi da riga me shara-shara fari, ta kame tulin gashinta da ribbon tasa hulan net, sakin labulen tayi ta fara safa da marwa a ɗakin hanunta goye a bayanta, a hankali tace "babu wani mahaluki da zai shiga tsakanina da Abdool na bashi dama, ya zama dole na magance wannan matar da take shirin rabani dashi, ita kuma wancan ameeshan zanji da ita"
wayan man ta kira yana ɗagawa yace "Baby"
a hankali tace "ya aiki? ina zaune inata kewanka"
yace "nima haka"
tace "na gaji da zaman ɗaki naga umma a cikin gida tana wanki naje na taya ta?"
murmushi me sauti yayi ya kula tsoro take ji shiyasa har ta tambayeshi yace "kije mana nima na kusa dawowa idan kina ganin zaki taƙura kiyi zamanki a ɗaki zan dawo yanzu"
tace "to kafin ka dawo bari naje"
dariya yayi yace "tsoro fa kike ji"
a shagwaɓe tace "nidai bana jin tsoro"
yace "to shikenan kinsan su faruk suna kokari? yanzu na hau social media naga yadda ake yaba company ɗin m.u.m"
tace "nima na gani kuma naji daɗi sosai, amma koma ina company ɗinmu ya kai, ka bada babban gudunmawa"
yace "to baby kin fara koyan surutu"
dariya tayi tace "ina tare dake ba dole na koya ba?"
yace "idan na dawo zamuci gaba da hira amma yanzu ina aiki"
tace "bye I love you"
katse wayan yayi, aje wayan tayi tasa flat shoe me kyau ta fito daga ɗakin, cikin tafiyan kasaita da izza ta fito a asalinta na manal, fito takeyi kamar yadda ta saba, umma ta ɗago kai domin ganin waye yake fito haka? tasan dai Imran baya fiito (wanda basu san fito ba shine whistle mutum ya rinka hura iskan baki yana bada sauti yawanci ƴan iska ne suke yinshi macen arziki ko namijin arziki basa yi)

Ido huɗu sukayi da umma tayi mata murmushin da idan tayi tofa babu kyau, a hankali ta durkusa tace "ina kwana umma?"
ɗauke kai tayi taci gaba da wankinta, janye bahon wankin tayi tace "gaisheki fa nake BILKISU"
a firgice umma ta kalleta jin ta kira sunanta kai tsaye, janye bahon zatayi manal ta rike mata hanu, kara umma tayi jin zafi sosai a hanun kuma shine hanun data faɗi akai su ameesha suka gyara mata da Imran, da sauri ta saki hanun tace "ai sorry na manta akan hanun kika faɗi ko kuma na tureki?"
kallonta tayi, ta yiwa umma signal tareda murmushin gefen baki, tace "kinji haushi ne dana kira sunanki kai tsaye? to kiyi hakuri zan kara respect bilkisu me gadon zinari hakan yayi miki?"
umma sai yanzu tace "ba zanyi mamaki ba sabida dama bakiyi kama da me tarbiya ba"
dariya tayi sosai harda rike ciki sannan ta haɗe rai ta janye bahon tace "bari na tayaki"
a fusace umma tace "ki sakarmin baho kafin na ɓata miki rai"
tana girgiza kai tace "a,a nikam saina tayaki"
tureta umma tayi da karfi tace "ki bar nan banason ganinki na tsaneki"
a kasa ta faɗi kanta kasa bata ɗago ba, umma taci gaba da wankinta bata ko kara kallonta ba, a hankali ta tashi ta fara tafiya, bayan gidan taje ta ɗauko wani gatari da yake a ɓoye cikin kayan karafuna, rikewa tayi a hanu ta fara tafiya tana kallon umma, a tsorace umma ta cire hanunta daga wanki idonta a waje tana kallon manal, ganin tana nufota gadan gadan tace "Imran ka fito zata kasheni"
idonta a bushe zuciyanta yana tafasa take takowa da gatarin a hanunta, Imran garin sauka daga gado saida ya faɗi kasa, da gudu ya fita waje ya tsaya yana kallonta, ta karaso wajen umma ta riko hanunta, saura kaɗan umma tayi fistsari a tsaye tsaban firgita, idon manal ya canja kala ta damƙa mata gatarin a hannu, a lokacin Ameesha ta shigo a ɗan gajiye tace "umma ga ɗinkin..."
zaro ido tayi ganin manal ta damƙe hanun umma tasa mata gatari tana kallonta umma kuma jikinta yana rawa, da gudu ta karaso zatayi magana manal ta ɗaga mata hanu, tsayawa tayi, manal cikin wani irin murya tace "kin tsaneni ki kasheni"
girgiza kai umma tayi "ba zan kasheki ba amma na tsaneki"
cikin daka tsawa ta ɗaga gatarin zata sara akanta tace "ki kasheni, tunda bakyason na zauna da ɗanki ki kasheni, ina sanshi kamar zan mutu shima yana sona meyasa kikeson shiga tsakanina dashi? ke wa ya shiga tsakaninki da mijinki?"
umma tace "manal ki sakeni"
tace "bazan sakeki ba saikin kasheni"
a firgice ameesha taja da baya ganin manal ta haɗa hanunta dana umma ta sarawa gefen cikinta gatarin jini ya fara zuba, umma a firgice ta kalli Imran tace "na shiga uku da gaske da take kada ta kashe kanta ace nice ku taimakeni"
Imran da gudu yazo kafin ya karaso ta kara ɗaga gatarin ta sarawa kafanta, ameesha jikinta ya fara rawa, idanunta sun kara girma, ta kasa koda motsi tana kallon jinin da yake zuba daga jikin manal ga kuma idonta da yake a bushe yayi jajur tana kallon cikin idon umma take cike da tsoro da tsananin tashin hankali, ameesha batasan time ɗin da taje ta riƙe manal Imran yana kwace gatarin ba, ganin tanada karfi har yanzu bata saki hanun umma ba duk kwacewan da suke mata, suka kwantar da ita a kasa suna kwacewa, cikin sallama ya turo kofan hulan a hanunshi da alama a gajiye yake, tana ganinshi ta saki gatarin a hannu umma, da ihu tace "Abdool zasu kashe ni ka taimakeni"
wurgar da hulan yayi da gudu yaje wajen yana jayeta daga danneta da sukayi a kasa, cikin kiɗima yake kallonsu su duka, jinin dake zuba daga gefen cikinta dana kafarta yake kallo jikinshi yana rawa, kallon umma yayi wacce take rike da gatari da jini a jiki, so yake yayi magana ya kasa, manal cikin kuka tace "ka taimakeni zasu kashe ni"
umma data kasa cewa komai kuma ta kasa yarda gatarin tana kallonshi kawai tana girgiza kai, Imran ne yazo ya karɓi gatarin ya wurgar, jijjiga umma yayi firgigit ta dawo hayyacinta, cikin rawan murya tace "Abdool ka yadda dani bany....."
da wani irin tsawan da yasa ameesha toshe kunne tareda runtse ido yace "kimin shiru"
tsit tayi dan tuna take dashi yau shekara 30 kenan bai taɓa yimata koda kwatankwacin irin wannan tsawan ba, yace "bakya sonta shine zaki kashe ta? idan ƴarki ce aka yiwa haka zakiji daɗi?"
cikin tsawa ya matso dab ita yace "zakiji daɗi?"
a firgice ta koma bayan Imran, ranshi yayi mugun ɓaci ganin jikin ummanshi yana rawa sabida tsawan da man yake mata, yace "Abdool ka iya bakinka ka daina yiwa umma tsawa...."
maruka masu zafi ya wankeshi dasu yace "idan naci gaba fa me zakayi?"
yace "zan rama mata"
ɗaga hanu yayi zai kara mishi marin Ameesha ta damƙe hanunshi tana kallonshi itama da mugun ɓacin rai akan fuskanta, cikin zafin rai kamar ana zuba mata wuta a zuciya tace "akan wannan gold digger kake yiwa ummanka tsawa kake marin kaninka? yaushe ka zama butulu ne man?"
kwace hanunshi yayi yace "kece gold digger ameesha, ashe kina kishi da manal shiyasa kika danneta umma ta sareta tanaso ta kasheta"
murmushin da yafi kuka ciwo tayi kana tace "kishi? kishi fa kace, akan wannan zanyi kishin?"
manal gefe ganin tana mishi tsawa tace "ya isheki haka"
cikin fushi ta wani shaƙe wuyan manal ɗin tana huci, kakarin mutuwa manal ta fara, tace "dake nake magana? nace dake nake magana? da wanda ya ajeki nake magana"
fizgeta man yayi ya juyo da ita da karfi, yace "to saiki kasheni ni ba ita ba"
tace "man sakarmin hannu"
yace "bazan sakeki ba, toma ina magana da family ɗina me yasa bakinki ciki?"
tace "abinda yasa wannan matar taka ciki shi ya sani ciki butulu kawai..."
cikin ɓacin rai yace "karki kara kirana da butulu"
tace "na faɗa butulu butulu butul...."
marin daya ɗauketa dashi saida ta faɗi kasa kusa da Imran, dafa kunci tayi har gefen fuskanta yayi jaaa, Imran yace "kada ka kara sa hanunka koda wasa ka taɓa ta"
matsowa yayi kusa da ameesha yace "idan na kara fa?"
yace "zan rama mata"
mari ya kuma ɗauketa dashi, Imran ya wankeshi da maruka har uku a jere, duka ya fara kaiwa Imran shima cikin ɓacin rai ya fara ramawa, umma ihu tayi tace "ameesha zasu kashe kansu"
ameesha jan Imran ta fara ita kuma manal tana jan man, da kyar suka raba su, bakin Imran yana jini yace "mugu mara imani"
zai yi magana manal tace "dan Allah kayi shiru, na yadda zan bar gidan ka sakeni kawai zan tafi dan Allah kuyi hakuri ku daina hakan"
tana magana tana hawaye, kallon kyakkyawan fuskanta yayi sannan ya share mata hawayen yace "babu inda zakije ke kaɗai ina tare dake tare zamu tafi"
jan hanunta yayi zuwa ɗaki, duk suna tsaye a wajen har ya tattara kayansu duk ya zuba a akwati yasa mata hijabi ya ɗau duk wani abinshi me amfani yaja hanun manal suka fito tare yana jan akwatin, Anty sai a lokacin ta shigo duk abinda sukeyi taji kuma ta gani, fahad yana gefenta, manal tana kuka tana cewa "me kakeyi haka abdool family ɗinka nefa wannan bakada kamar su"
baiyi magana ba saida ya tsaya a gaban umma dasu yace "tunda bakwa sonta ni ina santa zan bar muku gidan kafin kun kasheta"
jan hanunta yayi umma tace "Abdulrahman karka tafi ka barni, dan Allah ka dawo"
kallon Anty da fahad yayi, fahad wani kallon tsana yake aika mishi, baiyi magana ba yaja manal dake kuka, jikinta duk jini, saida ya fita ta juya baya tana kallonsu, murmushi tayi musu sannan ta bishi, a mota yasa kayansu yace "shiga"
shiga tayi yaja da karfi ya bar kofan gidan, asibiti ya fara kaita akayi dressing ciwon jinin ya tsaya amma taji rauni sosai, riketa yayi tana takakawa da kyar ganin haka kawai ya ɗauketa ya kaita motan, tana iya hango wani yanayi da yake ciki na tashin hankali me wuyan fassara"
kakkarya sim ɗinshi yayi ya watsar a wajen kafin yaja motan suka tafi, tace "gidanmu zamuje?"
girgiza kai yayi, tace "to ina zamuje?"
yace "barin garin zamuyi"
da sauri yace "kenan zan tafi na bar ammi? ka manta komai namu yana wannan garin? ka manta company ɗinmu anan yake? ka manta anan ƴan uwanka da ammina suke? muje gidanmu tunda zamu iya zama acan"
girgiza kai yayi yaci gaba da driving yana hawaye, haɗa kai tayi da gwiwa a hankali ta fara raira kuka, gani tayi ya juya kan motar ya nufi hanyan gidansu, da sauri tace "zamu koma gidanmu?"
gyaɗa kai yayi, tace "na gode Abdool"
a compound yayi parking kana ya zagayo ya ɗauketa yace a shigo mishi da akwatin, tana rungume a kirjinshi ya shiga da ita ciki, knocking yayi sannan yayi sallama, ammi tana jin muryanshi tace "Abdool bismilla"
shiga yayi da murmushi akan fuskanta tace "Abdool kaine..."
turus ta tsaya ganin manal kwance a hanunshi jikinta duk ya ɓaci da jini, da sauri ta karaso tace "meya sameta?"
cikin ɗacin rai zaiyi magana manal tace "yanzu ba lokacin magana bane"
kasa daurewa yayi saida ya faɗawa ammi abinda ya faru, dafa kirji tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, yanzu ka dawomin da ita gida ba? na gode tunda ka dawomin da ita da rai"
kwantar da ita yayi akan sofa yace "mun dawo tare alkawari nayi zan kula da ita ba zan taɓa barinta ba"
ammi tace "na gode Abdool".

umma jikinta yana rawa ta fara jin kamar zata faɗi, da kyar ta iya magana a hankali ta yadda babu wanda ya iya jinta bakinta yayi nauyi idonta ya rufe tana ganin duhu tace "ameesha Imran ku rikeni zan faɗi..."
kafin ta karasa maganan ta zube a kasa, a firgice ameesha da Imran sukayo kanta suna kiran sunanta "umma? umma?"
Imran ya fara bubbugata da karfi yace "umma dan Allah ki tashi karki tafi ki barmu, kinga ya man ya tafi ya barmu yabi ta kema tafiya zakiyi ki barmu?" 
ganin bata tashi ba kawai ya kalli ameesha wacce ta kasa motsi sai rarraba ido take cike da tashin hankali, ji tayi Imran ya rungumeta ya kankameta sosai ya fashe da kuka, da kyar ta iya ɗaga hanu ta ɗaura akanshi ta shafa sumanshi daya hargitse tsaban tashin hankali, bata iya tayi magana ba kawai ta zameshi daga jikinta fita tayi daga gidan babu ko takalmi a kafarta, a haukace take gudu akan titin, Allah ne ya kaita wani chemist lafiya, ta shiga da gudu tana haƙi ta kasa magana sai nunawa me chemist ɗin hanyan gida take, me chemist yace "wai meya faru ameesha kiyi magana mana"
da kyar tace "ka...ka...taimakemu umma ta faɗi bata numfashi"
da sauri yace "subhanallah muje"
fita sukayi suka nufi gidan, Imran ne ya ɗagata ya kaita ɗaki yana tsaye a kusa da gadon yana kai kawo, umma kwance flat bata motsi, fahad da Anty sai kuka suke, shigowa sukayi ameesha tace "gata can"
dubata ya fara yana gwaje gwaje, kasa tsayuwa Imran yayi a hankali yaje gaban ameesha ya tsaya yana kallonta, taɓe baki yayi wani kukan yana kara zuwa mishi, a hankali ta janyoshi jikinta tana tapping bayanshi tace "shiiii ya isa ka daina kukan haka ya isa zata samu lafiya"
cikin sanyin jiki dr ya tashi ya kalli ameesha da sauri tace "menene?"
yace "akwai babban matsala"
Ameesha jikinta yana rawa tace "na me?"
yace "ɓarin jikinta ɗaya ba zai kara aiki ba, ba zata kara iya tafiya ba".


_Jiddah Ce..._
08144818849