Babban Buri:Fita Ta Huɗu
A hankali ya buɗe idanuwansa ya sauke su a kan fuskarta, sai kuma ya ƙara lumshe idanuwansa.
BABBAN BURI
بسم الله الرحمن الرحيم
FITOWA TA HUƊU.
~~~Tun kan na rufe bakina kiran sallah ya karaɗemin kunne da hanzari na miƙe naje jikin randar lakar da muke da'ita na ɗibo ruwa a cikin cup biyu na kawowa Mama ɗaya sannan na juya na bawa A'isha ɗayan.
Ƙurɓi biyu Mama ta saukar da kofin daga bakinta haɗi da zubamin godiya sai faman sanyamin albarka take yi.
Gasashiyar kazarnan na fiddo daga leda na miƙe da kaina na samo faranti da wuƙa a cikin kitchin sannan na dawo na zauna.
Yankawa Mama tsoka na yi na miƙa mata sannan na yanka wa A'isha na juya gunsu Ahmad na taradda su suna ta faman saka lomomi cikin bakin su.
Girgiza kai nayi haɗi da ajiye farantin a gefen Mama na miƙe na ce "Bara naje na yi sallah Mama".
A tare muka nufi gurin da muke ajiye butocin gidanmu ni da A'isha muka zubawa ko wacce ruwa, kana muka gabatar da alwalarmu muka shige ɗaki domin gabatar da salla.
Kallon su Umar Mama ta yi ta ce "Umar ku ajiye abincinnan haka nan kuje ku ɗaura alwala ku yi Sallah ku dawo."
Miƙewa suma suka yi a tare sannan suka ɗibi ruwa suka sha suka gabatar da alwala duk Mama na tsaye tana ganin yadda suke gudanar da alwalar.
Bayan mun kammala sallar ne muka fito daga ɗakinmu muka janyo ƙofar ɗakin kana muka doshi ɗakin Mama, da yake a kowanne dare a ɗakin muke taruwa yin fira.
Koda muka shiga a zaune muka ganta hannunta riƙe da carbi tana lazumi, tabarma na shinfiɗa mana sannan naje gunda muke rataye ƴar fitilarmu na kunnata.
Nan danan ɗakin ya dauki haske kuwa, ganin A'isha ta wuni bata ci komai ba yasan ni na fice daga ɗakin naje na ɗauko risho ina dubawa ko Allah zai sa naga ko a kwai kalanzir a cikin sa.
Ganin a kwaisa na mike cikin murna naje na ɗauko ashana na kunna wutar na samo silba na ɗaura a saman rishon na samo ruwa na zuba na koma gefe ina jiran su tafarfasa.
Suna tafasa na juye su a cup na fice daga kicin ɗin.
Ɗakin Mama na koma na ajiye ruwan na koma gurin da nake ajiye lipton na ɗauko nasa a ciki na koma a tsakar gida na kinkimo kular abincinnan na kai ɗakin sannan na zauna na kalli A'isha na ce "matso ki sha ruwan nan ko kayan cikinki sa warware".
Miƙa mata kofin nayi sai da ta shanye kusan rabi kan ta ajiye kofin, ai kuwa nan take sai ga zufa ya rufe ta.
Kallonta na sake yi na ce "yau kin duba littaffan ki kuwa?", Kyaɗa kanta tayi alamar eh, ban damu da shurun nata a gare ni ba domin kuwa daman nasan halinta ne hakan, wani lokacin tana jin mutum na magana sai dai kawai ta bishi da idanuwa.
Banji da jiba na ce "Dan Allah A'isha karki ba ni kunya ki dage gurin karatunnan kin ji, bana son a samu matsala, a rayuwata bani da burin daya wuce naje na nemo kuɗi na kular mana da ƴan ƙannenmu ke kuwa ki je ki nemo mana ilimin da zamu yi alfari da shi wanda zamu samu tudun dafawa".
Riƙe hannuna ta yi shine ya sanya ni kallonta, buɗe bakinta ta yi kan tace dani "Anty khadeejah karki damu insha Allahu ba zan baki kunya ba, addu'ar ku kawai nake buƙata."
"Shafa kanta na yi nace "Allah ya taimaka A'isha na".
Kallona nakai gunda Mama take wacce ta yi azamar dauke idanuwanta a kanmu tana dauke ƙwallar data ziraro mata daga cikin idanuwa.
Ɗauke kaina nayi a kanta inajin wani abu na tokaremin zuciya.....
★★★★★★
Bayan fitowa ta daga gidan, miƙewa Hajiya Inna ta yi ta leƙa ɗakin Haidar ganin baya ɗakin ya sanya ta shigewa uwar ɗakin nasa.
Kwance yake cikin lallausan katifarsa wacce ta wadatu da faffaɗan zanen gado ga sanyayyen sanyin dake faman ratsa dukkanin gaɓobin mutum , lulluɓe yake cikin bargo sai faman sauke numfashi yake yi a hankali a hankali.
Zama tayi gefen shimfaɗar tasa sannan tasa hannu ta fara shafa sumar kansa wacce take ta fulanin a sali.
A hankali ya buɗe idanuwansa ya sauke su a kan fuskarta , sai kuma ya ƙara lumshe idanuwansa.
Muryarta ce ta ratsa dodon kunnensa "Shalelena a tashi magarib tana tunkaro mu hwa."
Miƙewa zaune yayi yana ya mutsa fuska, sannan ya miƙe ya nufi hanyar banɗaki, da kallo ta bishi tana faman girgiza kai sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin.
Parlour ta koma ta zauna tana tunanin rayuwar data shuɗe.
*ASALIN LABARIN....*
Malam Sulaiman Wurno haifaffen ɗan garin Wurno ne dake cikin jahar Sokoto, shi kaɗai ne a gurin iyayensa hakan ne ya ba su damar ba shi dukkanin abinda yake so, ba ƙaramin so suke yi masa ba kasancewar shi kaɗaine da su.
Yayi karatun Islama dai dai gwargwado kana daga bisani suka turosa a cikin jahar Sokoto domin samun ilimin zamani.
A cikin jahar Sokoto ya yi karatunsa na pramary har secondry da yake kuma mahaifinsa nason karatun kuma yaron yana da kwakwalwar karatu sai suka nem masa jami'ar Usmanu ɗanfodiyo University dake cikin jahar Sokoto.
Bayan kammala karatunsa ya samu aiki anan cikin Sokoto a asibitin WC dake cikin ƙwaryar birni Sokoto, wannan abun ba ƙaramin faranta ran iyayensa ya yi ba.
Bada jimawa ba kuwa suka zaɓa masa matar aure daga cikin danginsa.
Da yake ba irin ƴaƴan yanzu bane sai kawai ya lamunce aka daura aurensa da amaryarsa MARYAMAH.
Bayan MARYAMAH sai da ya ƙara mata uku suka cike huɗu , nan kuwa Allah ya albarkaci zuri'arsa.
Amaryar gidan wato Hajiya Turai tana da ƴaƴa goma cifff , yayinda ta uku take da ƴaƴa takwas ta biyun ce keda sha uku sai Maryamah wacce suke cewa Hajiya Inna dake da ƴaƴa biyu wato Aminu da Aliyu.
A cikin ƴaƴannan gaba ɗaya ba mace cikinsu kaf ɗinsu maza ne, Jimilarsu 33 kenan.
Gida ne Wanda duk dame gidan yana tsaye a kan ƙafafuwan sa , amman neman yake ya zama abinda ya zama.
A ko wacce Safiya ta Allah sai anyi jidali a tsakanin yaran gidan ko wanne zuciyarsa a baki take kuma ko wanne baya ƙaunar ɗan ubansa sai dai ɗan ɗakinsu.
Mahaifinsu yasha zama yana lurar dasu muhimmanci zumunci amman ko ƙaɗan basa ɗauka.
Da yake Aminu ne Babba a cikinsu mahaifinsu yakan zaunar dashi ya dinga nuna masa muhimmanci zumunci, yakan yawaita faɗan "Aminullah, ko bayan raina ka kasance meson zumunci ka kula da ƴan uwanka kamar ina raye.
Dukkaninsu sunyi karatun Islama dana zamani dai dai gwargwado.
Aminu da Aliyu dukkaninsu sunyi karatu a sashen kasuwanci sauran kuwa gaba ɗaya su aikin office ne a gabansa.
A kwana a tashi hasarar me rai sai gashi rana ɗaya Allah ya azurta Aminu , dukiya ce ke shigo su tako wacce hanya .
Yayinda rai ya dinga ɗibar raywakkn matan gidan da ɗaya bayan ɗaya harya rage saura Maryam wacce suke cewa Hajiya Inna...
Za mu ci gaba a Gobe............
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU} MARUBUCIYAR MATAR ABDULLAH.
ƳAR MUTAN BUBARE CE.
Maryamah