Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 22
Tafiya nake ba kowa kasancewar safiya ce sosai, sai da nayi nisa sosai sai kuma nayi tsaye hawaye suka zubomin wata zuciyata tace min, "Yanzu Jiddah kin amince kema yaranki su taso suna maki kallon da kika taso kina yi ma mahaifanki? Yanzu Jiddah ba za ki zauna ki raini yaranki ba, ko dan ki hana su kukan rashin Uwa? Haba Jiddah za ki yi babban rashin hankali idan kika tsallake yaranki kika bi duniya, ribar me za ki tsinta a yawon duniya? Jiddah wa ke gareki wanda zai tausaya maki idan kika bi duniya? Wannan shi ne sakayyar da za ki yi ma Mahaifiyarki? Ashe baki tausanta? Ashe za ki iya ɗora mata wahala ki bar mata yara ki bi uwa duniya? Lallai Jiddah akwai sauran rashin tausayi a cikin zuciyarki." Sai kawai na fashe da kuka na kamo hanya na dawo gida, tun daga ƙofar gida nake jin kukan Afnah da Afnan tamkar ana dukansu, da sauri na ida shigewa na ɗauki Afnah ina lallashi ina shafa kan Afnan, shi kau Haidar yana zaune da kofin ruwa ba shakka su ya ba don naga duk rigarsu ta jike da ruwan. Rungume su nayi duka na fashe da kukan tausayin kaina dana yarana.
"Ya Allah ga baiwarka tare da yaranta a halin da kafi kowa sani Ya Allah ka agaza mana ka bamu mafita kan wannan yanayin rayuwa da mu ke ciki mai wahala." Ita ce kawai addu'ar da nake ina kuka tamkar raina zai fita, sanin ina fama da ciwon hawan jini dana gushewar hankali yasa na samu da ƙyar na natsu na daina kuka na koma ajiyar zuciya kawai.
Har ƙarfe biyun rana ba abin da muka ci Ni da yarana saboda ban da komai haka ban da abin da zan ba su, sai na saka hijabina nabar su nan na je wani shagon Mustapha mai shago muka gaisa nayi shiru domin dai ban iya neman taimako kuma ina jin kunyar amsar bashi duk da nima ina bin bashin amma an hana ni dole na haƙura na barsu sai mun je can sai su biyani.
Ganin nayi ɗan jim yasa mai shagon cewa, "Jiddah lafiya lau kuwa?" Nayi Jim saboda ban san ya zan ce ba, amma sai na samu bakina da furta "Don Allah ka ban taliya da magi idan mu kai aikin polio zan kawo maka insha Allah."
Ya dube ni sai kuma ya ɗauko abin da nace ya ban. Na yi godiya na tafi ina jin daɗi sosai.
Ko da na je gidan na iske Haidar nata yi masu wasa suna dariya kamar ba yunwa suke ji ba, tausayin su ya kamani nan da nan na haɗa wuta na ɗora sanwar, sai ga Haidar ya zo yana ta hura wutar gwanin ban tausayi.
Su kuma su Afnah sai sukai barci nan da nan na gama dafawa na tada su na zubawa Haidar amma sai yaron nan ya ɗebo taliyar ya nufi bakina, alamar yana nufin na fara ci kafin ya ci shi. Na girgiza kaina ina jin daɗin yadda tun yanzu Allah Ya sakawa yarana tausayina komai su ke ci sai sun ban a baki, Haidar ko kukan yunwa bai yi yaron sai dai ya lafe ya yi shiru kawai, idan su Afnah ke kukan sai ya kama yi masu wasa da dariya har sai ya ɗauke masu hankali sun daina kukan.
Idan kuwa ban lafiya sai ya zauna kusa da Ni ya dinga taɓa jikina yana mun sannu ya ɗebo ruwa ya ban duk abin da ya samu ya kawo min, idan kuwa yaga na lulluɓe sai ya kama kuka ya dinga shiga makwabta yana cewa a zo Umminsu bata lafiya.
Polion da nake yake matuƙar taimaka min, duk wata ina amsar kayan abinci gun Mustapha mai shago da an bamu kuɗin polio sai na kai ma shi na amshi wasu kayan.
Abban Haidar bai dawo ba sai da ya yi wata guda har da kwana shida rannan kwatsam ina shara sai ga shi ya faɗo gidan ba ko sallama kamar wanda ya fito daga kewaye (toilet) na dube shi nayi ma shi sannu da zuwa na cigaba da sharar da nake ina jin yaran na kiran ga Abba ga Abba nasan ba lallai bane ba ya dube su balle ya tanka masu na aje tsintsiyar na bi shi ɗakin da ruwan sha.
Yana zaune kan gado yana duba rediyon shi na shiga da sallama ta. Ya ɗago kai ya dube ni ya ci gaba da abin da yake yi. Sai naji na kasa yi mai maganar kuɗina daya kwashe ranar da zai tafi, sai dai na yi zaune kawai bakina ya rufe sai a cikin zuciyata nake siffanta maganganun da zan yi mai. Ya dube ni a sheƙeƙe ya ce, "lafiya dai ko? Naga kin wani tasa ni gaba da wani ruwa kamar kin ban abinci na ci." Madadin na yi magana sai kawai na miƙe na fice don ban da ta cewa a fili sai a zuciya, to kuma bai faɗuwa na zuciyar.
Cikin yarana na koma na zauna nayi tagumi hawaye suka zubo min. Ji nai ana share min hawayen, ashe Haidar ne, shima kukan yake yana cewa, "Ummi Abba ne ko?" Girgiza kaina nayi nace, "Kaina ke ciwo Haidar." Tashi ya yi ya ɗebo ruwa ya ɗauko min maganin da nake ba Afnan da bata lafiya ya ban wai na sha na warke.
Muna haka Abban Haidar ya fito ya leƙa diram ɗin da ake zuba ruwa yaga babu ya ja tsaki ya yaye labulan ɗakin ya ce min, "Ke wai ba ruwa ne gidan?" Cikin sanyin jiki nace "Yanzu zan je na ɗebo dama shara zan gama na je na ɗebo kamar ko da yaushe."
Ya saki labulan ya fice ina jin ƙarar rufe gidan. Na sauke ajiyar zuciya na tashi na ɗauki bokiti na nufi mono ɗibar ruwa, Haidar ya ɗauko buta ya biyo ni da ita shima zai taya Ni ɗaukar ruwan.
Tun daga lokacin nice ke ɗebo ruwan gidan, Abban Haidar na kwance zan je na ɗebo ruwa a mono mutanen unguwa nata gulmata wasu ma da kansu suke tareni a hanya suna tambaya ta ina maigidana da nake zuwa ɗibar ruwa? Ni dai dariya kawai nake na wuce don ban da amsar ba su.
BAYANA SHEKARA BAKWAI
Ana cewa ba a sabo da wahala to Ni dai na saba da wahala sai dai ba yadda za ai ka ganni ka gane cewa ina cikin matsala, domin ko da yaushe cikin fara'a nake da murmushi, ban taɓa wanke ƙafa na je gun iyaye da maganar abin da Deeni ke mun ba, amma ina matuƙar jin tsana da ƙiyayyarsa a zuciyata duk tsawon lokacin nan ban da tsanar shi babu abin da ke yawo a jikina.
Kasancewar yanzu ban da polio ina yin duk wani aiki daya shafi ɓangaren sai na samu sauƙi sosai har na shiga makarantar koyar da sana'a ta shekara biyu, duk sanda zan tafi sai na kai kayan yarana gun Mama idan sun dawo daga makaranta su saka idan na dawo na biya na taho da su gida.
Itama Mama har zuwa yanzu ba sauƙi saima cigaba da zaman ƙuncin da take a gidan mijinta, abin da duk idan na tuna nake kuka ina ƙarawa ina jin a raina wai yaushe ne zan zama kamar kowa ne? Yaushe ne zan farin ciki Ni da yarana kamar kowa? Kowa ne yara zaka gansu da kazar-kazar amma ban da nawa, sun fahimci wace irin rayuwa mu ke da mahaifinsu sun gane cewar su kansu ba tasu yake ba, domin hatta makaranta nice na samu mai sauƙi ta gwamnati na saka su, haka ma islamiyya duk Ni na kai su.
Ƴanci guda na samu shi ne wanda na datse duk wata alaƙa ta aure tsakanina da Deeni, saboda na lura bai damu da ciwon da ya yi yawa a duniya ba, don haka na same shi na gaya mai na gaji da aurensa don haka ba zan sake amincewa da shi ba. Bai damu ba yace min idan kau haka ne hatta yaranki sai dai kisan yadda za ki yi da su domin ba zan iya riƙe su ba Ni. Har ga Allah naji daɗin hakan domin daman Ni ke riƙe da su ba shi ba, don haka na amince da sharaɗin babu ruwana da shi haka ba ruwana da hidimarsa kowa ya yi abin da zai fissheshi nace na yarda.
Sai dai ba a jima ba ina zaune aka zo a'a ce na gyara za a duba gidan nace kamar ya aka ce ai Deeni ya saida rabin gidan ne shekara biyu da suka wuce.
Naji mugun tashin hankali domin kuwa nasan idan har Deeni zai iya saida rabin gida ban sani ba to tabbas wata rana gidan zai saida ban da labari. Hakan yasa na nufi gidansu domin na gayama iyayensa sai dai Mamarsa nuna min tai shi ya sai gidansa don haka duk yadda ya yi da shi ba ruwan wani. Jin haka yasa na koma gida jikina sanyi ƙalau domin akwai yiyuwar watarana ace gamu can gidan haya..idan kau haka ne tabbas kuɗin hayar Ni ce zan dinga biya kenan.
Cikin lokacin komai ya yi min tsanani polion aka daina sai na koma ban da wani tsari illa abin da ya samu daga jama'ar gari mutanen arziƙi masu ƙaunata.
Ina a halin ne kwatsam Allah Ya jeho Uncle Salim kamar daga sama, ya jima yana kuka ganin halin da nake ciki, cikin ɓacin rai yace na shirya kayana da yarana mu tafi Kano, cikin sauri na haɗa komai sai dai muna zuwa Mama tace bata yarda ba kar da in sake na tsallake gidan mijina na tafi tunda ba sakina ya yi ba.
Babu yadda Uncle Salim bai ba dole ya haƙura amma sai da ya biya min kuɗi na sauya jarabawa ya biya min jamb sannan ya sai min waya yace mu dinga magana karatu zan koma ba zan zauna haka ba.
Cikin ikon Allah na samu jarabawata tai kyau yadda ya kamata don haka na je na rubuta jamb cikin kwanciyar hankali da fatan dacewa, komai nake Uncle Salim na taimaka min daga Kano yake turomin kuɗi domin yasa na buɗe account na banki, don haka sai na sake samun sauƙin rayuwa karo na barkatai.
Harma na dinga tunanin gani can a makaranta ina karatu yarana kuma suna gun Mamana cikin aminci da kulawa,
Bayan wani lokaci na gama komai duk Deeni na kallona bai ce komai ba sai ana saura sati guda na fara zuwa makaranta yace sai na biya mai kuɗin makarantar shi ma idan dai ina so nayi karatun nima.
Na gayama Uncle Salim sai yace ba komai don haka ya turomin kuɗin na ba shi, shi dai fatanshi na kama karatu kawai na barshi ya yi duk abin da zai.
Cikin ikon Allah na fara zuwa makaranta babu abin da Uncle Salim bai saimin ba, ranar da na fara zuwa makarantar ji nayi tamkar na fara sabuwar rayuwa, ji nayi na manta duk wata damuwata ji nayi kamar wata sabuwa a wata sabuwar duniyar.
Cikin kwana biyu nayi ƙawata guda ɗaya mai Rahma Kazaure, zaune mu ke cikin farin ciki ban manta yarana ba ina masu addu'a duk lokacin da nayi sallah haka ina neman Allah Ya shirya mahaifina Ya haɗa kanmu waje guda Yasa mana fahimtar juna haka ina yawan saka mahaifiyata sai dai har ga Allah mantawa nake da wani Deeni a rayuwata sam don haka ban wani saka shi a cikin lissafina sam.
Ina duk lokacin dana dawo daga makaranta sai na iske Deeni da wata, amma ko a jikina saboda na riga na cire shi a raina baki ɗaya kawai karatuna nake ina jiran na gama nasan Uncle Salim zai samar min aiki na kula da kaina da yarana tare da mahaifiyata.
Ranar da akai mana hutun semester na dawo gida ina jin duk ban jin daɗi, don haka na kasa ko zuwa gidanmu don in taho da yarana sai nayi kwance kawai ina jin duniyar tai min zafi baki ɗaya.
Barci ya kwashe Ni sai nayi mafarkin gani zaune da Uncle Salim yana kallona ya ce, "Jiddah ki yi haƙuri da rayuwa kowace iri ce, don Allah ki zama jaruma ki jajirce kan lamurranki da yaranki ki natsu ki kama kanki ki kama mutuncin kanki insha Allah watarana za ki yi dariya." Ya nuna min wani mutum daya juya baya ya ce, "Jiddah zan tafi Ni, tafiya mai nisan gaske amma kin ga wancan? Shi ne zai maye maki gurbina duk rintsi kar ki rabu da shi tabbas na yarda da shi nasan zai kula da ke Jiddah." Ya tashi ya juya ya tafi ina ta kiran sunansa bai ko waigo ba... Ƙarar wayata ce ta tada Ni daga barcin da nake ina mafarkin Uncle Salim.
Mamarmu ce ke kirana, "Ki maza ki shirya ki taho Kano za mu je an yi rasuwa." Iyakar abin da Mama tace kenan ta kashe wayarta.
Gabana ya faɗi daram! Kar dai ace Hajjo ce ta rasu! Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Tabbas idan Hajjo ta rasu na shiga uku ni Jiddah shike nan komai zai iya tsayawa sai Uncle Salim kawai ya rage min duk da cewar yafi Hajjo taimako na amma Hajjo macece dole wata damuwar sai mace.
Haka na shirya na nufi gida na iske Mama cikin shirinta tana ta jan carbi, kawai tasha muka nufa sai Kano, tun a ƙofar gidan naga tarin mutane sai na ida amincewa Hajjo ta rigamu gidan gaskiya.
Sai dai ina shiga Hajjo na fara cin karo da ita zaune tana sanye da hijabi tana jan casbaha.
To waye ya rasu ne?" Ita ce tambayar da nake ma kaina. Saƙo ya shigo wayata ina dubawa naga daga Deeni ne ga abin da ya ce. "Ni Ƙamaraddini na saki matata Jiddah saki biyu."
Idan kin gama idda ki aure kuma kayan ɗakinki na saida sai ki riƙe yaran duk na bar maki.
To masu karatu waye ya rasu?
Deeni ya saki Jiddah saki biyu ina zata je?
Mu haɗu a kashi na gaba.
Taku a kullum Haupha!!!!