HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Biyar

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Biyar

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 


           Page 15

Cikina ya murɗa naji tamkar zawo zai kubce min, bakina ya kasa ko buɗewa balle na samu damar amsa kiran da yake ƙwala min.

Har ya shigo ya iske ni zaune, na sadda kaina ƙasa ina jiran abin da zai faru, ba mamaki Yau sai Deeni ya wawwanka min mari. "Ke wai wani sabon rainin arziƙi aka koya maki ne ko me? Kina ji ina magana don iskanci za ki yi banza da Ni? Wallahi ki kiyaye ni ba ruwana da wani jego sai in maki rashin mutunci.  Dilla tashi ki ban nama na ɗan ci naga jiya ba sosai kika sako min ba don muguwar rowa irin taki da shegen son abin duniya. Safiya ma tace min baki saka mata abin kirki ba sai kace da kuɗinki aka siyo abubuwan, ni wallahi ban taɓa ganin mace mai shegen son kanta ba irinki ba, idan baki sauya hali ba wallahi za ki sha baƙar wahalar rayuwa yadda baki tunani." 
Ni dai ko da naji faɗan ya tsaya iyakar haka sai nayi wa Allah godiya na miƙe jiki sanyi ƙalau na shiga ɗaki na don na zuba ma shi abinci.
Bayan na kawo mai abincin ne ya dube ni a yamutse yace, "Naman fa da lemu mai sanyi? Ba ina zaune bakin titi naga an siyo maki katin na lemu da maltina ba? Ke dai Allah ya yi maki shegen kwaɗai kamar ƙuda."  Cike da kulawa nace ma shi, "Abban Haidar ba Ni na aika ba, Hajjo ce ta aika aka siyo mata da su ta tafi kuma wallahi ko guda bata aje ba."  Ya wani zaburo"Kina nufin duka ta tarkata lemun nan ta tafi? Har ina gayama Safiya za ki bata ko biyar-biyar ne tana ta murna? To wallahi ba za ki maida ni maƙaryaci ba, don haka fito da kuɗi na siya na kai mata ai ƙawarki ce tare na ganku." 
Kaina ya fara sarawa, na dafe ina jin bugun zuciyata na sauyawa , me Deeni ya ɗauke Ni? Komi yace min kan Safiya sai yace kuma wai ƙawata ce tare ya ganmu, shin ganinmu tare ya dace ace yana min abin da yake min? Gaskiya ba zan iya ba shi kuɗin lemun Safiya ba, sai dai dama nayi niyyar ba shi dubu goma cikin kuɗin da nasamu idan yaso ya saimata da su ban damu ba. Don haka na miƙe na nufi ɗaki ya ƙirgo mai Naira dubu goma cif na kawo na ba shi, nace, "Ga shi nan cikin kuɗin da na samu ne, sauran Hajjo tace na nemi sana'a na dinga yi kar in zauna haka nan." 
Ya amshi kuɗi ya tura aljihu yana kai lomar abinci a bakinsa yace, "Nawa ne kuɗin duka da kika samu ne? Ko mugun halinki bai bari ki gayamin ko nawa kika samu ma? Kin san dai daraja ta ce tasa kika samu kuɗin ai ba wata tsiya ba ko? Don da ban aure ki ba kika haihun ba wanda zai ba ki ko sisi."  Kaina ƙasa na gayamai duk abin da na samu tas.
Ya fito da kuɗin ya watsa min a jiki cikin ɗaga murya yace, "Amma dai kin jima da raina min hankali, watau Ƙato da shan duka Gardi da amshe kuɗaɗe ko? To da ban aure ki ba ina ke ina samun waɗannan kuɗin? Amma don baƙin hali shi ne kikai mirsisi kina cewa wai Hajjo tace ki yi sana'a da su. To ni da ke wa ya kamata ya kama sana'a ban da rashin kunya?  To idan mafarki kike ya kamata ki farka domin wannan tsohuwar na lura da nan garin take babu abin da zai hanata koya maki rashin daraja. Wai tsohuwa da ita har tasan ta leƙa ƙofar gidana tai min kashedi kamar ta cika min kuɗi lokacin da nake gina gidan nawa, wallahi bayan na fahimci ta fini tujara da babu abin da zai hana ni yi mata rashin kunyar gaske sai naga idanunta a buɗe don haka na rabu da ita amma kika ce za ki ɗauki nasiharta ruwa kike tsab zata halakar dake a banza tana Kano ta gama aurenta ita ke ce a ruwa ke za a saka wutar jahannama Deeni na aljannah na kallon tsala-tsalan ƴan matan aljanna dubunnai da aka ce za a ba kowane magidanci, don haka dama kin gyara halinki ko jikinki ya gaya maki a wuta, Ni dai nasiha nake maki mai kyau da inganci, idan kuma kin ɗauka to zan gane ta hanyar ban kuɗin duka na samu sana'ar kirki na dinga yi da su sai ki ga kin yi albarka."

Kaina na ƙasa na kasa cewa komai, domin dai ban fatar shiga wuta, saboda an yi mana wa'azi sosai islamiyya kan wutar jahannama don haka ba zan bari saboda kuɗin da ban san wace sana'ar zan kama ba su kai Ni. Domin Mamarmu na yawan yi mun nasiha kan nabi mijina, duniya duk shirmen banza ce, lahira ita ce madogara don haka in nemi lahirata ta hanyar kyautatawa mijina da bin umarninsa,da yafe masa kura-kuransa hakan shi ne hanyar tsira.
Don haka na ɗauko kuɗin duka na ba shi, ina addu'ar Allah Ya ɗaukaka duk sana'ar da zai da su.

Bayan kwana biyu, shiru ban ji Abban Haidar yace mun ga sana'ar da ya fara yi ba,amma dai ya yi sabbin ɗinki ya sai waya babbar gaske wadda ake kira shafa-shafa, hatta takalma ya sai taki biyu abinsa, sai baƙin gilashi daya siya yake rufe idanunsa. Ganin abin sai gaba yake yasa Yau nace idan ya dawo zan tambaye shi sana'ar da yake da kuɗin da ya amsa, ko da nace gida sai na gayama Mama yadda akai.

Sai sha biyu daidai ya dawo, har na jima da kwanciya, don ban jiransa, ina ƙoƙarin aje mai duk abin da yake buƙata sai in kwanta, saboda idan na hana kaina barci na jira shi nace sai ya zo ya ci abincin gabana, irin abin nan wai, sai ya dinga tsaki yana cewa Kin zo kin wani tsare ni da kallo, ko abincin bai shiga yadda ya kamata don masifar kallona da kike, mace kamar almajira kana cin abinci tana gwalalo maka idanu ina amfani, idan baki ƙoshi ba me yasa baki dafa mai yawa ba."  Hakan yasa sam ban zama duk da abin na birgeni na ganni gabansa yana cin abinci ina kallonsa yana kallona ko da bai min magana ba, ina son ni na dinga ma shi magana ina ba shi labarin ko da littafan Hausan da nake karantawa ne, ba mamaki idan ya ji yadda ma'aurata ke faruwa ya sausauta min abin da yake min nima.

Ina jin shi ya gama cin abincin har yana faɗan don tsabar ruganci na kwashe naman duk ƙashi na zuba mai, kuma wallahi babu ma naman, sai ƙashin kuma ban ci ko ɗaya ba duk shi na zubamawa, don dai a zauna lafiya, amma ban tsira ba.
Sai da ya gama komai ya kwanta yana jin waƙa kamar yadda ya saba ya shiga ɗakin, (kasancewar har zuwa yanzu a falo nake kwana Ni da Haidar) sallamar da nayi tayi uku ba wadda ya amsa kuma nasan ya jini sarai domin wayace a hannunsa yana latsawa. A hankali na zauna gefen gadon nace, "Abban Haidar sannu, dama magana na zo mu yi ne idan ban takura maka ba don Allah."
Ba tare da ya aje wayar ba yace, "Takurawa na nawa kuma? Wallahi duk sanda idanuna suka sauka kanki ji nake kin takura ma rayuwata kin mun karan tsaye a rayuwata, kin hanani rawar gaban hantsi."  Na haɗiye hawayen dake son zubamin na jin baƙar maganar daya lafta min nace, "Abban Haidar nace wace sana'a ka fara da kuɗin ne? Naga baka kawo komai ba kace na sana'ar ne har mun doshi sati uku da baka kuɗin."
Idan ya tanka bangon ɗakin ya tanka, don haka na fahimci ba zai min magana kome zan ce bai ban amsa. Hakan yasa bakina alaikum na miƙe na nufi gun kwanciyata, ina jin tsakinsa na rako ni.

Washegari da sassafe yabar gidan, tun kafin na haɗa kokon safe, sai dai bai jima ba ya dawo yace min, "Ke ba naji jiya kina cewa za ki kaima Mamarku yaron can ta gani ba ne?" Cikin ɗoki na amsa da "E." Ya juya ya fice alamar ya amince na tafi. Sauri-sauri na shirya daman tsohuwar nan da wuri take zuwa asubar fari ta dafa mana ruwan wanka ta tafi, don haka shirya ma Haidar kawai nayi na rufe gidan na bada ajiyar makullin inda yace na fice zuwa gun Mama, bata taɓa ganin Haidar ba.

Allah Sarki! Ina zuwa na iske Mama a gidansu ɗakin Inna, duk ta rame ta yi uwar rama, daka ganta kasan tana cike da damuwa. Jiki sanyaye na ida isa inda take zaune tana jan carbi, na sauko Haidar daga goye na zauna ina jiran ta gama na gaidata. Amma Allah kaɗai yasan yadda zuciyata ke harbawa ganin Mama a wannan mugun yanayin, ko da yake rabona da ita tun ranar da mijinta ya rasu, sai Yau.
Bayan ta gama na gaidata, ta amshi Haidar tana ta kallonshi tana mai murmushi kwance kan fuskarta, sai abin ya yi min daɗi ganin Mama na murmushi nima na dinga sakin murmushin.
Nan da nan ta tashi ta fara ƙoƙarin haɗa wuta,nasan girki take ƙoƙarin ɗorawa don haka na dakatar da ita.
Sai da yamma tayi na tashi na ɗora sanwar tuwo,na gama kenan na zubo zan ci Abban Haidar ya faɗo gidan ba ko sallama sai faɗa yake tamkar ya ci babu. "Ban da hauka ma irin naki miye abin ki kama hanya ki taho ki bar gida ba kowa? To ai ga shi nan an kwashe kaf kayan abincin dake gidan hankalinki sai ta kwanta ai yanzu kin ja min asara da rana tsaka."
Daga ni har Mama kallonsa kawai mu ke ba mai bakin magana, duk da na fahimci abin da yake nufi amma sai na gaza gasgata abin da yake cewa, wai an sace kaf kayan abincinmu! Abin da mamaki kam, ban taɓa jin an shiga gidan wani ba a unguwarmu ko Ni daga baya na gano Abban Haidar ne ya kwashe kayana ya saida na lefe kawai shiru nayi ban magana ba, don bata da amfani ko na yi.
Mama ce tai ƙarfin halin fara gaida shi, ya amsa ba ko kunya yana cigaba da gaya mata ban jin magana sam halayena ba masu kyau bane ba.

Nan dai Mama ta dinga min faɗa tana ba shi haƙuri tace na tashi na shirya na tafi gida.

Tare muka fito da shi sai faɗa yake yana cewa "Saura ki je ki kama bincike kamar ƴar sanda kan anyi min sata a gida." Kaina ƙasa ban ce komai ba Ni dai har muka isa gidan ya buɗe muka shiga.

Kai tsaye ɗakin na wuce babu komai an kwashe hatta magi da jarkunan mai babu ko ɗaya, na duba atamfofin ma babu kayan Haidar ne kawai ba a taɓa ba.

Kasa kuka nayi sai zaman ƴan bori da nayi kawai. Ya fice ya bar Ni yana buge min kashedin kada na je nayi mai talla cikin unguwa abinci dai shi ne mai siye ba wani ba.

Bai jima da fita ba, Binta ta shigo ta dube ni nasha kuka har fuskata na nuna tace, "Wallahi Jiddah tun da naga Deeni da kura yana ta loda kayan abincin nan nasan daman na lefenki zai maimaita, ban san wane irin miji bane ba Deeni, kuma Wallahi a banza zai je ya saida su ya barki da yunwa. Maganar gaskiya Jiddah ki tashi tsaye kan Deeni ki nuna mai ɓacin ranki kuma kice ya maido maki kayan abincinki tun da ba shi ne ya siye su ba kowa yasan daga gidanku suke.

Wani jiri-jiri ya sauko min duk da a zaune nake sai da naji kamar zan faɗi, don haka na zame na kwanta kawai ina maida numfashi.
Har Binta ta bar gidan ban san ta bar gidan ba.

To masu karatu, ko Jiddah zata ɗauki mataki kan Deeni wannan karon koko?
Ina kuɗin sunan da Deeni ya amsa ya fara sana'a?


Daga taku a kullum Haupha!!!!