WATA UNGUWA: Fita Ta 29
BABI NA ASHIRIN DA TARA
Bayan fitar Irfan a mota bai zame ko'ina ba sai kafar yaɗa labarai mafi kusa da shi, ya gabatar musu da shaƙuwarsa. A nan suka nemi ya ba su hotunan ita yarinyar da bayanai akanta domin su fara yaɗawa.
Irfan ya yi wiƙi-wiƙi da ido tamkar mara gaskiya, sannan ya ce "Am! Gaskiya ba ni da hotonta a yanzu, amma..."
"Ranka ya daɗe taya za'a rasa nono a ruga? Matarka ce fa, ya za'a yi ka ce baka da hotonta?" Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya faɗa fuskarsa na bayyanar da mamaki.
Ma'eesh ya yi saurin tarar numfashin mai maganar "Ba fa matarsa ba ce ja'irar, wacce ya ƙalafa a rai ce yake burin aura."
"Dakata Ma'eesh! Ban gayyato ka nan don ka ci zarafin masoyiyata ba, idan wannan ne ya kawo ka don Allah ka tafi tun muna shaida juna."
Ma'eesh Ya kalle shi da mamaki "Akan waccen ja'irar yarinyar zaka yarfa ni a gaban jama'a? Yarinyar da ma ko ƙaunarka bata yi?"
Irfan ya miƙe "Eh ɗin na ji, ta ƙaunace ni ko akasin haka duk wannan ni ta shafa, kuma ina ƙaunarta a haka. Ma'eesh kafi kowa sanin cewa ni mai sauƙin kai ne, amma akan al'amarin Matata Maheerah ni mai zafi ne tamkar Borkono. Ka tafi kawai."
Jin wannan zancen ya sa Ma'eesh ya fice a fusace. Irfan ya juya yana huci kaɗan.
Ya ba su bayanan da suke nema sannan ya masu alƙawarin nan da gobe zai kawo masu hotunanta.
*********
Babban Birnin Balgori
Superior Hotel
9:30pm
Tafe take tana tauna cingum ƙas-ƙas-ƙas, tana sanye da wasu ɗamammun English wears a dirararren jikinta. Ƙafafunta sanye da takalmi, Doguwa ce ba can ba, tana da manyan fararen idanu tamkar madara.
A gefenta Alhaji Rabi'u ne suke tattakin a tare da shi. Sun zo dai-dai corridorn da zai sadaka da harabar hotel ɗin wayarta ta hau burari.
Cike da iyayi irin na matan bariki ta ɗauka. "Hello dear Sis!"
A can bangaren aka yi dariya tare da faɗar "Ashe fa yanzu kan mage ya waye kin zama yar hannu."
Ta yi 'yar dariya "Abin da ya wajaba akaina kenan tun da har na fantsamo duniya. To fa ba gudu ba ja da baya, sai na ga abin da zai ture naɗin Buzu."
Daga can ɓangaren aka sake yin dariya "Ashe za'a jima ana iyo a tafkin zunubai don jiran zuwan wannan ranar da daidai yake da neman jaki mai ƙaho."
Suka saka dariya a tare "Baki da dama Sis."
Sorfina ta tsagaita dariyar tana faɗar "Wai ina kika shige ne yau? Duk na damu kin san baki taɓa kwana ba a nan gidan ba."
Mahee ta juya ta kalli Alhaji tare da kashe masa ido ɗaya, sannan ta mayar da hankalinta akan wayar.
"Ina tare da Alhaji Sunusi ne a Superior Hotel, amma yanzun nan zaki ganni don ina hanya ne ma."
Daga haka suka yi sallama, Alhaji Rabi'u ya kalle ta, "Amma baki da dama Lady Mahee, me ya saka baki faɗa mata gaskiyar cewa kina tare da ni ba ne?"
Dai dai lokacin ne suka zo inda ta yi fakin motarta, don haka ta danna malatsin motar.
Kafin ta shiga ta kalli cikin idonsa tana wani irin fari "Ai na ga take-takenta ne fa tun a ranar farko, ka san wai yan magana sun ce idan ka ga kare yana sansana takalmi to ɗauka zai yi. Ni kuma ba zan yi sake a yi mini sakiyar da ba ruwa ba."
Ta murmusa, ya mayar mata da martani murmurshi "Kina da gaskiya Lady Mahee, ai ko a rayuwar bariki wanda duk ya same ki ya gama kula wasu matan, domin ba za su burge shi ba."
Ta faɗaɗa murmurshinta sannan ta yi blowing kiss a hannunta ta hura masa iskar ta shige motarta tare da yi mata key tana faɗar "Sai gani na biyu Honey."
Ya tsaya a gun yana bin motar da ido 'Lallai kin shigo bariki da ƙafar dama, amma da sannu zan fanshe duka dukiyata da kike ci sannan daga ƙarshe na cimma manufata a kanki.' ya yi wani shu'umin murmurshin da shi kaɗai ya san ma'anarsa
**** Haka kwanaki suka ci gaba da turawa al'amarin Maheerah sai daɗa ta'azzara yake yi. Har ta kai matsayin da bata jin shakka ko tsoron wani ya san sana'arta. Bata shakkar taka masu mulki da dukiya, zuwa wannan lokacin har gidaje guda biyu take da, wanda alhazawan da take tarawa suka gina mata. Ita da gidan London girl sai idan ta kai mata ziyara.
Daga nan ƙyashi da hassada suka fara ziyartar zuciyar Sorfina don ta ga Maheerah na neman shiga gabanta a kowanne al'amari, ga shi tana neman wargaza mata plan dinta akan Alhaji Rabi'u, wanda ta ci alwashin sai ta janyo shi ƙasa.
Tun lokacin da ta fara harkar bariki kawo yanzu bata taɓa samun wanda ya fita da ita ƙasar waje ba.
Amma abin mamaki wai agwa-gwa da ƙin ruwa, sai ga shi Maheerar da ko shekara bata rufa ba a harkar, kusan ko da yaushe tana yawatawa a ƙasashen duniya.
Wannan ya saka duk yawan ƙaunar da Sorfina take yi wa Mahee bai hana mata jin ƙyashinta ba, duk da cewa bata yi wani yunƙuri na dakatar da Maheerar daga fantamawa a duniyar daular da take ciki ba.
******
GARIN MAMBIYA
Irfan ya faka motarsa cike da zafin rai ya shiga ma'aikatar ta su. Kai tsaye office ɗinsa ya shige sannan ya cire cort ɗin da yake sanye da ita ya saƙale a abin saƙale kaya da ke kafe a gefe cikin office ɗin.
Ya rage daga shi sai rigar ciki. Ya ƙure masuburbuɗar sanyin da take sanyaya ofishin.
Duk da haka zafi yake ji, kuma zufa bata daina tsattsafowa daga kafofin gashin jikinsa ba. Bako tantama zafin dake zuciyarsa ne yake taimakawa wurin rura wutar zafin da yake ji a gaɓɓan jikinsa.
"Meyasa Masoyiya? Why? Me yasa zaki horar da ni ta wannan ɓangaren, ba zan iya jurewa ba."
Ya sauke doguwar ajiyar zuciya sannan ya shige banɗakin ofishin ya watso ruwa ya fito.
Zamansa da knocking ɗin ƙofar duk ba yi minti biyu ba.
"Yes, shigo"
Sakatariyarsa ta shigo ta ɗan rusuna ta gaida shi cikin girmamawa.
Ya amsa yana kallonta ba walwala "Meya faru kika shigo mini a wannan lokacin da na fi sha'awar kaɗaici?"
"Sir wata matashiya ce ta zo nemanka."
"Me ya kawo ta?"
"Ba ni da masaniya Sir sai dai ta nuna mini tsananin buƙatarta da ganin naka, shi ya sa ma..."
"Je ki faɗa mata ba yanzu ba, ta dawo wani lokacin."
Zata sake yin magana ya zare mata ido.
"Ki je kawai ki cika aikinki."
Ya koma ya zauna tare da sunkuyar da kansa kan teburin ya fara karatun wasiƙar jaki.
Ta fice jiki a sanyaye, cikin abin da bai fi minti ɗaya ba ya ji an murɗa handle ɗin ƙofar alamar buɗewa.
Ya yi saurin ɗagowa a fusace a zatonsa ko sakatariyar ce ta dawo.
Ya zazzaro ido tare da miƙewa a hanzarce "Ke! Ke ce a nan? Me ya dawo dake a cikin rayuwata a dai-dai wannan gaɓar?"
Ummu Inteesar ce
managarciya